Sashe 150
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ya yi, tsaye ta yi ta fasa yin abun da ta yi niyya, Fahad ya gaishe da ita ta amsa masa a daƙile, ƙarasowa dad ya yi wurin su da murmushi akan fuskarsa yana kallon Leemarh ya ce mata bata yi bacci, cikin jin daɗin zuwan nashi tana murmushi ta ce, "Eh, yaya Fahad nike tayawa hira." dad ya jinjina kai ya ce ya yi kyau, kallon mom data yi tsaye kamar an dasa ta fuska a haɗe ya yi, ya tambaye ta ya aka yi ne, ta ɗauke kai tare da ce masa ba komai ta zo ta ce ma Leemarh ta je ta kwanta don gobe za su je school, dad ya ce, "Ki rabu da ita tun da bata jn baccin, ta ce tana taya yayanta hira ne." Ya yi maganar yana murmushi ya ce mata su je ciki, fuska a daure ta kalle shi kaman bazata tafin ba, harara ta wurga ma Leemarh kafin ta juya suka tafi, murmushi ne akan fuskar Leemarh don ta ji daɗin taka mata burkin da dad ya yi, shi dai Fahad shiru ya yi don ya fahimci abun da mom ɗin ta yi niyyar yi, sai dai a ransa yana jin ya shirya ma kowane irin abu da zai fuskanta a wurinta don yanzu sosai yake jin son Leemarh a cikin zuciyarsa. Washe gari da safe a tare gaba ɗaya suka yi breakfast kasantuwar ranar monday ne amman ban da mom, bayan sun gama Fahad ya yi sallama da dad a tare gaba ɗaya suka fito, dad zai wuce wurin aiki shi kuma Fahad ya ce zai yi dropping su Leemarh a school kafin ya wuce, bayan sun iso school ɗinsu Leemarh, har da kukanta da za su rabu, ya ji duk wani iri kamar ya koma da ita sai dai ya san hakan ba mai yuwuwa bane, rarrashinta ya yi ya ce mata idan suka samu wani hutun da kan shi zai zo ya ɗauke ta, hakan ya sa ta ɗan ji sanyi a ranta suka yi sallama cike da nuna za su yi kewar juna ya tafi. A ranar da daddare bayan sun gama cin abinci , Leemarh ta sa Batool da Sultan suka taya ta fiddo da kayayyakin da aka bata a Funtua, gidan su Fahad akwati guda aka yi mata na sababbin ɗinkakkun kaya har da su Batool, da su gyale da takalma har da su sarƙa da yan kunne, ledar da Sadeeya ta bata kuma nan underwear ne sabbabi da su perfume da roll on, shima Fahad tsadaddun sets ɗin mayukan shafawa da na gashi ya siya mata har da abayas masu kyau, sai kuɗi dubu ɗari da daddy ya ba Fahad ya bata, dama wasu daga cikin kayan da aka ɗinka masu daddy ne ya bada kuɗin, 6angaren hajiya itama akwatin kaya ta yi masu da Sultan da Batool har da su takalma da inner wears, dad ya bi kayan da kallo fuskarsa ta nuna jin dadi sosai, kallon mom ya yi ya ce, "Kin ga kaya kaman wani lefe." Babu yabo babu fallasa ta ce unhm, da yake mutum idan yana hali sai ya ɗauka ma kowa irin sa ne, mom gani take da gayya suka haɗo masu wannan uban kayan, sosai yaran suke ta farin cikin kayan, duk da hajiya ta saba aiko masu da kaya amman Leemarh ta ji daɗin wadannan sosai don bata ta6a zuwa hutu aka haɗo ta da kaya haka ba, dama Kano ne take yawan zuwa, can kuwa wani lokacin ita ake buƙatar wani abun ma a wurinta, wasu abubuwan ma nata ƙiri ƙiri idan ta je ake nuna ana so a raba ta da su, dad ya kalli mom a karo na biyu ya ce, "Yakamata ki kira su sai ki yi masu godiya." Wani kallo ta jefa masa, fuska a haɗe ta furta, "Ba don Allah aka yi masu ba da sai an yi godiya." Dad ya ce, "Wace irin magana ce haka, ko don Allah aka yi wanda ya yi ma naka wannan hidimar ai ya cancanci ka kira sa ka yi masa godiya." Ɗan tabe baki ta yi ta kauda fuskarta gefe, can ta miƙe tana faɗin ai ko shi zai iya kira ya yi masu godiyan, daga haka ta nufi hanyar part ɗinta, dad ya bita da kallo rai a matuƙar 6ace har ta shige, haka Leemarh da duk ta ji abun da ta faɗa ta bita da kallo fuskarta a haɗe, janye idonsa dad ya yi bayan ta shige, har cikin ransa yanzu ya gaji da halin Jameela, ya rasa gane ita ɗin wani irin hali ne da ita, wani mutum zaka ga idan aka ɗauki shekaru yana canza hali, amman ita kusan halin nata ƙaruwa yake koda yaushe, a da yana haƙuri da kauda kai a dukkanin abubuwan da take masa saboda son ta da yake sosai, to amman yanzu ta fara kai sa wuya kuma yana jin yana son ɗaukar mataki akanta, to amman ta yaya? Duk lokacin da ya yunƙuro zai ɗauki mataki kanta ƙarshe kasa ta6uka komai yake, ƴar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tunanin da yake, wayarsa ya ɗauka ya kira hajiyarsa, bayan ta ɗaga kiran cikin girmamawa ya gaishe da ita daga baya ya yi mata godiyar hidimar da aka yi ma su Leemarh tare da addu'oi, bayan ya gama yin godiyar tashi ya ba su Batool da Sultan suma duk suka yi mata godiya har suna ce mata idan aka yi masu hutu suma za su zo, hajiya ta ce to Allah Ya kaimu Ya kawo su lafiya tana jira, Leemarh ma ta amsa wayar ta ƙara yi mata godiya ta ce mata wllh duk tana missing nasu, bayan sun gama yin waya da hajiya, dad ya kira daddy Sa'ad shima suka yi masa godiya, bayan sun gama ya kira mommyn su Fahad itama duk suka yi mata godiya, Leemarh ta amsa itama ta ƙara yi mata godiya, ta sigar shagwa6a ta ce, "Wllh mommy duk na yi missing ɗin ku, ina jin kaman na dawo." Tana jiyo sautin ƴar dariya da mommy ta yi ta ce, "Muma daughter muna missing naki, musamman yadda kike cika mu da abubuwan daɗi, yanzun nan su Binafa ma suka gama magana wai da kina nan da kin haɗa masu abun dadi." Leemarh ta yamutsa fuska tana jin kaman ta ganta a Funtua, dad nata kallon ta suna wayar cike da jin daɗi, bayan sun gama dad ya kira Fahad ya ƙara yi masa godiya da ban gajiya, duk da ɗazun ma ya kira sa ya yi masa ya hanya lokacin ya sanar mashi har ya isa Zaria, suma yaran duk sai da dad ya basu suka yi masa ya ya isa, Leemarh ma ta ƙara yi mashi ban gajiya da godiya duk da sun yi waya da shi har sau biyu bayan tafiyarsa.