Sashe 180
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ta fiddo abun da ke ciki ta ga latest iphone, da sauri ta juya ta kalli aunty da itama idanunta ke akan wayar ta hau jinjina kai mamaki ya cika ta, can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce, "Wannan hidima ai har ta yi yawa ma." Salma da duk jikinta ya gama yin sanyi ta kasa cewa komai, aunty ta ɗauko ɗayan jakar da ta gani ta buɗe ta ga akwatin zoben ne a ciki ta fiddo, bin red velvet box ɗin ta yi da kallo tana ɗan jinjina kai, kallon Salma ta yi ta ce, "Wannan ma ba ƙaramin diamond ring bane baby, daga akwatin shi da kuma yankan da aka mashi." Ita dai Salma ta bita da ido don ba sanin yadda ake gane mai tsada take yi ba, aunty ta kalle ta ta tambayi Deen ɗin ya tafi ne, Salma ta ce mata eh ya ce ma Funtua zai wuce daga nan kuma saboda ita zai je, aunty ta zaro ido kafin da sauri ta kai hannu ta ɗauki wayarta tana faɗin bari ta kira yaya Fiddausy a shaida masu kada su ji abun kwatsam, sai dai koda ta kira layin aka sanar da ita a kashe yake, Sageer ta kira shima tana ta ringing baya ɗauka ta ce yanzu haka yana wurin ƙwallo, ta ce bari ɗan anjima zata sake kiran innar ta su. Bayan sallan magrib Sageer na zaune tare da abokan shi su Aliyu a gaban gidan dake kallon nasu in da suka saba zama, hira suke suna cin awara da suka siya a wurin Imrana da shine yanzu ke yin awaran, "Kai...wannan ba kamar Salma ba?" Wani abokin su Ibrahim da ke latsa waya ya faɗa, Sageer ya ce wace Salma, nuna masa hoton Ibrahim ya yi, Sageer ya bi hoton Salma da kallo wanda sam ita bata ma san da Deen ya yi mata shi ba ɗazun a restaurant, sai dai iya gefen fuskarta ne a hoton ta ɗan sadda kanta ƙasa tana yin murmushi dogon hancinta ya fito sosai, shima Sageer ya ga kaman ita sai dai yana shakkun hakan ba kamar ganin wanda ya ɗaura hoton, ɗagowa ya yi yana miƙa ma Ibrahim wayar ya ce kawai dai kama ce amman ba ita bace, Aliyu ya miƙo hannu ya amshi wayan yana faɗin ya ga hoton, yana ganin hoton da tsananin mamaki ya ce, "Wannan tabbas Salma ce, ka duba da kyau." Amsar wayar Sageer ya sake yi yana kallo still ya kasa gasgata ita ɗin ce duk da ya ga kammani sosai, ya ce, "Ta ya za a ce Salma ce, Deen ne fa ya ɗaura hoton, shi miye tsakanin shi da ita da har zai ɗaura hoton ta." Ibrahim ya ce, "Ba tana magana da shi saboda aikin da take mashi ba, ka sani ko sun fara soyayya ne. Kuma ka duba caption ɗin hoton da kyau." Sageer ya ƙura ma rubutun jikin hoton ido wanda capital S tare da heart emoji aka saka, ƙara bin hoton ya yi da kallo lokaci guda kuma ya zaro ido da al'ajabi ya ce, "Kai wllh kuma kamar fa ita." Cike da tabbatarwa Ibrahim ya ce ai itama ce S ɗin da aka rubuta farkon sunanta ne, shi dai Aliyu yana ta bin su da ido mamaki ya sa ya kasa yin magana don ya gane ita ce, da sauri Sageer ya miƙe yana faɗin bari ya ɗauko wayarsa da ya saka caji tun da zai je ƙwallo ya kira ta....Mom Jameela na zaune saman kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya a falonta dake a 6angarenta, basu daɗe da dawowa daga airport ba rakiyar su Sapna da za su koma London bayan sun je Kano sun kwana biyu, dama saboda naɗin sarautar Deen suka zo ba daɗewa za su yi ba, waya ce a hannun mom Jameela tana latsawa yayin da daga gabanta saman c-table yankakkun fruit ne a hankali take ɗauka tana sha, lokaci guda ta tsaya cak da tauna apple ɗin da ta kai baki, yanayin fuskarta ne ya sauya zuwa alamun al'ajabin abun da take kallo, hoton Salma ne da ke ta yawo ana bayyana ta matsayin sabuwar budurwar Deen Jr. Lokaci guda ta wani kalan haɗe rai tare da sauke ƙafarta, hannunta har ɗan rawa yake don ta je ta duba idan da gaske Deen ɗin ne ya ɗaura hoton a instagram kamar yadda take ganin anata faɗa....a wani kalan zabure mom ta miƙe bayan ta tabbatar da shi ɗinne da gaske ya ɗaura hoton, fuska a yamutsa ta ƙanƙance idanu ta shiga kiran Deen, ta kai wayan kunne yayin da ta fara yin ringing tana wani cije baki tare da ɗage kai sama, ta riƙe ƙugunta da ɗayan hannun....