Sashe 164
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"Yanzu sai aure zaki yi ke nan?" Ta ji ya jefo mata tambayar, da sauri ta girgiza masa kai ta ce, "A'a.." ta ji ya ce miyasa, "Karatu nike son yi, yanzu haka ma na dawo Kaduna wurin aunty na a nan zan ci gaba da karatun." ya ce mata mi yasa bata son yin aure, Salma ta ji tambayar ta yi mata nauyi, gashi ta ɗan ji mamakin ma yadda ya yi mata irin tambayar, kiran sunanta ta ji ya yi ta ɗaga ido ta kalle shi, ya ce miyasa ta yi shiru, da ƙyar tana sauke idanunta ta ce, "Haka nan, na fi son yin karatu." ya ce, "But, ko an yi aure ana karatu." Kanta a ƙasa Salma ta ɗan cije baki jin abun da ya ce, ta ɗaga mashi kai alamar eh, "Ke miyasa baza ki haka ba?" Ɗago idonta ta yi suka shiga cikin nashi, a hankali ta ce, "Kawai...ban sama rai na aure zan yi ba." Ya ɗan yi shiru still kallonta yake, ita kuma duk nauyin maganar auren take ji hakan yasa ta kasa tsayar da idanunta kan shi, softly ya ce "Ko baki da suitors ne?" Da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi, sai kuma ta yi ƴar dariya ta ce, "Ina da su...kawai dai..." Ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa ba don bata ma san mi zata ce masa ba, "Ko duk ba wanda ya yi maki da zaki aura a cikin su?" ya tambaya, Salma ta ɗan runtse ido kanta a ƙasa, tunanin wace amsa ma zata bashi ta shiga yi, ita da ba wani samari sosai gare ta ba saboda ba saurarar su take yi ba, tsayayye wanda zata iya aura bai wuce Dr Hisham ba, shi kuma har yanzu bata wani jin shi a ranta kawai dai tana tare da shi ne, kuma ta ga kaman aunty Kubra tana son ta da shi, kiran sunanta ta ji Deen ya yi, a hankali ta amsa ya ce ta bashi amsa, ta ɗaga mashi kai ta ce eh ba wanda ya yi mata da aure, shiru ya yi yana ta kallon ta ita kuma ta ƙi ɗago fuskarta, a cikin rai Deen yake jin kaman this is the right time da ya kamata ya sanar da ita abun da yake ji game da ita tun can baya, dama ya bari ne sai ta kammala secondary school ɗinta ko zai bayyana mata sanin tana da son karatu, kada hakan ya raba mata hankali, "Salmerh.." Har sai da ta ji gabanta ya faɗi don bada irin sautin da ya saba kiranta ya kira ta yanzu ba, murya ƙasa ta ce, "Na'aam..." ba tare da ta ɗago ba, shiru ya ɗan yi kafin ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ni na yi maki?" Ƙirjinta ne ya wani irin buga, ba shiri Salma ta zaro ido tare da ɗago kai tana kallon Deen da idanunsa ke a lumshe tamkar ba shine ya furta maganar ba.....
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
53
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
53