← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 197

Sashe 92

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kallon dad da idanuwanta masu kaifi ta furta, "Sai ya je ya yi abun da ransa ke so..." Daga haka ta juya ta nufi hanyar part ɗin ta tana tafiya mai cike da isa, duk suka bi ta da kallo har ta shige part ɗin ta, miƙewa Batool ta yi ta bi bayan mom ɗin, Sultan ma ya bita daga baya Omar shima ya tashi, kallon Leemarh da ta yi zaune fuskarta duk ta nuna rashin jin daɗi dad ya yi ya ce ta je ta kwanta, a hankali ta ce, "Pls dad ka yi haƙuri.." Dan murmushi ya yi mata tare da jinjina mata kai ya ce ba komai ya wuce, bayan tafiyar ta Deen ya ɗago tare da kallon dad ɗin su da ke kallon 6angare guda, slowly ya ce, "I'm sorry dad..." Juyo fuskarsa ya yi ya kalli Deen ya ce, "Ba komai ka da ka damu, kai ma ka ci gaba da haƙuri da abubuwan da take yi, kasan akwai mutane da suke yin abu ba daidai ba amman su koda yaushe gani suke akan daidai suke, to itama haka ne akan ta, zan yi ƙoƙarin shawo kanta, sannan ka da ka sare ka ci gaba da yin ayyukan alherin ka a duk in da ka yi niyya matuƙar kana da hali. Ɗazun babanku na can Funtua ya kira ni har yake mani godiyar mota da ka ba Fahad, bai san ni bani da masaniya ba akan hakan, amman dai kawai na nuna masa hakan ai ba wani abu bane kyautatawa ce tsakanin ka da ɗan'uwanka." Sauke kai ƙasa Deen ya yi don shi bai yi niyyar sanar da su ba gudun abun da zai iya biyo baya, tsinkayar muryar dad ya yi yana cewa, "Ba wanda zai hana ka kyautata ma ƴan'uwanka, saidai ina son ka bar abun tsakanin ku kawai, kada ka bari ita mom ɗin naku ta sani gudun matsala ganin kuɗin motan na da yawa, na san dai su ba wanda zai yi magana game da hakan da ita." Jinjina kai Deen ya yi alamar zai yi yadda ya ce, addu'oin ƙarin buɗi na alkhairi ya yi masa kafin ya ce mashi ya je ya kwanta ya san yana tattare da gajiya, shiru Deen ya ɗan yi kafin a hankali ya miƙe ya ce ma dad ɗin sai da safe, ya amsa mashi da Allah Ya tashe su lafiya daga haka ya nufi matattakalar bene ya haye zuwa part dinsa....
Chapter 92 · 0% Book details