Sashe 124
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau tun bayan da Salma ta dawo daga school tana kwance a ɗaki don da ciwon ciki ta dawo, dama ta saba duk zata yi period sai ta yi ciwon cikin, imnarsu na zaune daga gefenta bayan ta sa ta ɗan ci abinci ta bata magani, akai akai take yi ma Salma sannu, tana kwance jikinta sanye da doguwar rigar material kanta ba kallabi, gaba ɗaya mazan gidan lokacin sun tafi masallaci kasantuwar ranar juma'a ne. Innarsu na a ɗakin Salma har lokacin da yaran gidan suka dawo daga masallaci, kowa sai da ya shigo ya ƙara yi ma Salma sannu da jiki har da mahaifinsu, Sageer ne na ƙarshe da ya dawo, ɗakin ya shigo yana sanye da riga da wando na shadda, daga bakin gado ya tsaya yana kallon Salma dake kwance ya ce, "Sannu patient, ya jikin?" Kai ta ɗan ɗaga masa kawai kana ganin fuskarta ka san bata lafiya, ledar da ya shigo da ita ya miƙa ma innarsu ya ce, "Ga abun ciwo nan na kawo mata." Amsa ta yi tare da dubawa, kallon Sagir ta yi tana ɗan murmushi ta ce, "Yanzu ka rasa mi zaka kawo mata abun ciwon sai gyaɗa?" Yana ƴar dariya ya ce, "To innarmu ina laifi, ni da ma na damu da ita har na kawo mata gyaɗan." Still da murmushi akan fuskarta ta ce, "To ita dake fama da kanta ta ya zata iya wani zaman cin gyaɗa." Sageer ya ce sai ta rinƙa 6ara mata tana bata tun da dama jinyar ta take, innarsu ta ce, "In dai ka damu da ciwon nata kamata ya yi ai ka kawo mata ko kaza." Ya ɗan buɗe ido yana dariya ya ce, "Kaza innarmu, ni da nike fama da kaina, kuma ita yanzu ai ita ce hajiyar gidan nan, wake samun irin kuɗin da take samu." Innarsu ta ce amman dai kuɗin ai ba ita kaɗai ke cin su ba, kowa na amfana tun da duk cikin hidiman gida ake haɗawa, yana dariya ya kalli Salma ya ce, "Zaki ci kaza?" Bin shi ta yi da kallo da ɗan murmushi, Sageer ya ce tun da ta ƙi magana bata son ci, cikin muryarta da ta ɗan disashe ta ce mashi ƴan shilan da yake siyowa take so, ya ɗan harare ta ya ce, "Kina ciwon ma sai kin yi kwaɗayi, to ai yanzu ba su fara gasa su ba, sai ki bari sai bayan magrib." Kai ta ɗaga masa daidai lokacin ciwon cikin nata ya motsa ya cize baki tare da kai hannu ta dafe mara, da sauri innarsu ta shiga yi mata sannu tare da dafa ta, Sageer da fuskarsa ta ɗan canza alamar tausayi ya ce, "To wai innarmu shi wannan ciwon bashi da magani ne? A ce duk wata mutum sai ya yi ta wahala." Shiru innarsu ta ɗan yi kafin ta ce ana samun maganin da ke yi musamman na hausa anata jarabawa har Allah Ya sa a dace, Sageer ya gyaɗa kai ya ce Allah Ya sa a dace, bayan ɗan lokaci ciwon ya lafa ta lumshe ido. Bayan Sageer ya baro ɗakin Salma, kicin ya wuce ya ɗauko abincinsa kafin ya wuce ɗakinsu, cire rigar shaddar jikinsa ya yi ya zauna da vest ya fara cin abincin, bayan ya gama ya ƙarasa hayewa saman katifarsu yana yin chatting, can ya ɗan waro ido ganin Deen ya turo masa saƙo, hannunsa har rawa yake yi wurin saurin buɗewa, sakon juma'a da Sageer ɗin ya saba tura masa ne ya yi masa reply, daɗi ne ya kama Sageer don yawanci idan ya tura masa bai wuce ya yi masa react ba, wani lokacin ma sai an daɗe sannan zai buɗe saƙon kuma ba zai yi ko react ɗin ba, amman yau ya amsa saƙon, ganin yana online a lokacin ya sa Sageer saurin tura masa, "Yaya Deen ina wuni." almost a minute sai gashi ya buɗe saƙon, ya yi masa reply da, "Lpy Alhamdulillah." Ƙara waro ido Sageer ya yi tare da washe baki, saurin gyara zama ya yi irin abun na yi ne ɗin nan, saƙo Sageer ya tura masa na yabo kan kokarin da suke a gasan premier league da suke cikin yi, shima bayan ɗan lokaci ya yi masa reply din godiya, daga haka bai ƙara tura masa komai ba shima Deen ɗin bai ce masa komai ba, har Sageer ya fita daga chat ɗin nasu sai kuma ya ga ya sake tura masa saƙo, da sauri ya buɗe, "Where is Salmerh?" shine abun da ya turo, da sauri Sageer ya tura masa da, "Tana nan, bata ma lafiya tana can kwance ɗakinta." Ya buɗe saƙon amman bai ce masa komai ba, sai ga vedio call ɗinsa ya shigo, har saida Sageer ya ɗan zabura ganin abun da bai zata ba, da sauri ya shiga daidaita zaman sa, har da kai hannu ya ɗan goge fuskarsa kafin ya ɗauka, faffaɗan murmushi Sageer ya shiga saki bayan ya yi tozali da Deen dake a ɗan kishingiɗe saman kaman gado kaman kuma kujera yana sanye da baƙar t-shirt, sumarsa a sake a wuyansa, gaida shi Sageer ya sake yi, a nutse ya amsa mashi kafin ya tambaye shi mi yake damun Salmerh? Sageer ya faɗa mashi ciwon ciki take yi, tambayar ta je asibiti Deen ya yi, bakin Sageer da ba control ya ce mashi ai dama ta saba yin ciwon duk wata, bata zuwa asibiti sai dai ta sha magani, shiru Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba, take kuma ya fahimci wane irin ciwo ne take yi, tambayarsa ya yi zai iya kai mata wayan don ya kira ta yanzu bata yi picking ba, da sauri Sageer ya ce, "Ƙilan wayan bata kusa da ita ne, don da ciwon ta dawo daga makaranta, dama bata zuwa da wayan school." Kai kawai Deen ya jinjina, da sauri Sageer ya shigo cikin gidan ya nufi ɗakinta, tuni ta samu bacci har innarsu ta bar ɗakin, nufar ta ya yi ya ɗan rankwafa yana tashin ta ta hanyar kiran sunanta, a hankali ta buɗe idanunta da suka ɗan sauya ta kalle shi, ɗan ɗaure fuska ta yi har zata fara yi masa ƙorafin tashinta da ya yi don baccin sauƙi ne a gare ta, kawai sai ya kanga mata wayar shi yana faɗin, "Ga yaya Deen yana son magana da ke." Wani faɗuwa gabanta ya yi lokacin da ta kalli screen ɗin suka haɗa ido da shi, satar kallon Sageer ta yi ganin haukan da ya yi mata, yana kallon a yadda take daga ita sai riga kanta a buɗe amman ya wani kanga mata waya, tashi ta yi ta zauna ta riƙe wayar Sageer ya juya ya tafi, ɗan murmushi ta shiga yi tana ƴan kame-kame, kanta an yi mata kitson gaba dama tun tana yarinya tana son shi, jelar kitson sun zubo mata a gefen fuska, "Yaya Deen ina wuni." Ta faɗa da disasshiyar muryarta, kai ya jinjina mata, suka yi shiru ta kasa tsayar da idanunta akansa, "Ya jikinki?" Ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Na samu sauƙi." suka ɗan ƙara yin shiru, "Mi yake damun ki ne?" Ta ji ya tambaya, ta bashi amsa da kanta ne yake ciwo tun a school, bin ta ya yi da kallo jin ta faɗi akasin abun da Sageer ya sanar da shi, daga yanayin da fuskarta ta nuna bayan ta faɗa mashi abun da yake damunta ya fahimci kunyar sanar da shi ainihin mi yake damun nata take yi, a karo na ukku da ya ji wani abu dangane da ita ya burge shi, na farko jijircewarta wurin sana'a, na biyu tausayinta kan abun da ya faru na Habu, yanzu kuma kunyar ta, wadda sam Basma bata da ita, ita duk idan period ɗin ta ya zo sai ya sani, haka zata yi ta mashi complaining ɗin ciwo duk da ba wani ma ciwon cikin take ba saboda mom ɗinta na kula da hakan matsayinta na likita, "Kin je hospital?" Ya tambaya, ta girgiza masa kai ta ce, "A'a, na sha magani na ji na samu sauƙi." Shiru ya ɗan yi kafin ya ce ok, sai kuma ya sake ce mata amman idan ta ji bai daina ciwon ba yakamata ta je asibiti ta ce masa to, "Where is ur phone?" Ta bashi amsa da tana cikin drawer ba da ita take zuwa school ba, kuma ta dawo da ciwo bata ɗauko ba, shiru suka ƙara yi, yana lura da yadda duk ta kasa sakewa, sai faman kai hannunta da ya sha zanen lalle take tana ɗan rufe gefen kitson gabanta alamun kunya, haka nan yau Deen yake jin komai na fuskarta na burge shi wanda a da da yake ganinta a zahiri bai jin hakan, hatta yadda kitson gabanta ya zuba ya ɗan rufe mata gefen fuska ya burge shi, duk ta ɗaga ido ta kalle shi sai ta ga ita yake ta kallo, can ta ce, "Na ga kuna yin gasan ko premier....Allah Ya bada sa'a." Ya yi ɗan murmushi tare da amsa mata da Amin, tambayarta ya yi tana kallon ƙwallo ke nan, da ɗan murmushi ta ce, "A'a da ban kallo, saboda kai ne na fara kalla, farko banma gane abubuwanta sai na tambayi yaya Sageer sai ya yi mani bayani." Yana ta kallonta tana yin maganar har ta gama, ya ɗan jinjina kai alamar ya fahimta, ta ji ya ce, "Thank you..." Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, bayan ɗan shiru ta ji ya ce, "Ina faraa." Ƴar dariya ta yi saboda yadda ya faɗi sunan, ta ce, "Nama kwana biyu ban yi ba." Ya yi shiru bai ce komai ba idonsa akanta, ta ce, "Kana son ci ne?" Slowly ta ga ya ɗaga mata kai alamar eh, ta ce, "To ai ka yi nisa da na yi maka, in da kana Abuja ne sai in yi in bada saƙon mota a kawo maka." Dan murmushi ta ga ya yi sai kuma ta ji ya ce nan ma zata iya aiko mashi, Salma ta ɗan waro ido alamar mamaki ta ce, "Ana bada saƙo ta jirgi ne?" Ya ɗan ɗaga mata kai, shiru ta yi mamaki shimfiɗe akan fuskarta