Sashe 41
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baƙo ne muka yi ya yi mana zuwan bazata, akawo masu abun da za su sha sai ki shirya masu abinci a table." Amsa mata ta yi da to ta juya, Deen na murmushi ya ce mata shine baƙon, hajiyar na dariya ta ce mashi eh mana mutumin da za a yi shekaru ba a gani ba ai ya zama baƙo, yar hayaniya suka fara jiyowa daga waje hajiya ta kai idonta kan ƙofar shigowa tana faɗin kamar hayaniyar mutane take ji, miƙewa Fahad ya yi ya nufi kofar ya leƙa, juyowa ya yi yana faɗin a gate ne ya san su officer ne suka sanar da zuwan Deen, hajiya ta ce ai Deen ɗin ne yana da masoya har zuwa ake ana tambayar ta yaushe zai zo, zama Fahad ya yi tare da ciro wayar shi ya yi sending kira, magana ya yi da officer ya bashi umarnin kar a bar kowa ya shigo sai Deen ya huta ko zai ga mutane, cire wayar ya yi daga kunne yana faɗin dole sai an ƙara security a gate, hajiya ta ce gaskiya don ta san yanzu mutane za su cika gidan. Bayan Balaraba ta gama shirya masu abincin ta zo ta sanar da su, Deen ya ce ma hajiya ta taso su je su ci abincin ta ce ai ita tuni ta ci abinci shiyasa ma ta zauna tana shan kankana, ya ce to ta taso su je ta bashi a baki ya yi missing hakan, tana murmushi ta miƙe, Fahad ma ya tashi, Deen ya kama hannunta suka nufi wurin table tana faɗin ita yaushe rabon ma da ta zauna cin abinci a can ta fi jin daɗin ta zauna kan kujera ta ci, balaraba ce ta yi serving na su abincin hajiya ta ce dole a ƙara sama masu wani abun su ƙara ta amsa mata da to, bayan ta gama ta bar wurin, a nutse suka fara cin abincin hajiya ta fara ba Deen a baki kamar yadda ya buƙata suna ta murmushi, lumshe ido ya yi yana tauna abincin ya furta ya yi missing ɗin wasu abinci na nan,
"Ko dai santi kake yi?" Hajiya ta faÉ—a tana faffaÉ—an murmushi, amsa ya bata da in ma ya yi santin ba laifi bane don cook É—inta ta iya abinci sosai,
"Ko kana son in baka ita idan ka yi aure sai ta rinƙa dafa maku abincin, ko kuwa ka fi son na matar ka?" Hajiya ta tambaya bayan ta bashi abincin yana taunawa, Fahad ya ɗaga ido ya kalle shi da ɗan murmushi, shima murmushin kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, a ranshi ya ayyana baya ma tunanin Basma ta iya ko ruƙe tukunya balle akai ga maganar iya yin girki. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya ce ma hajiya ta sa mai aikinta ta ɗauko masu jakunkuna a cikin mota kafin suka wuce bangaren da ɗakin da Fahad ke zama a gidan don su huta, hajiya kuma ta koma cikin falo bayan ta kirawo Balaraba ta bata umarnin ɗauko jakunkunan.
Da sallama ta shigo cikin gidan, saida ta ƙara yin wata da ɗan ɗaga murya sannan ta jiyo muryar innarsu tana amsa mata daga can cikin ɗaki, nufar ɗakin innar tasu ta yi tana haye tudun baranda lokacin innar ta fito jikinta sanye da doguwar rigar atamfa, tana ganin Salma ta saki faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Alhamdulillahi, hasken gidanmu ya dawo." Washe bakin jin daɗi Salma ta yi ta nufe ta da sauri tana ƙarasawa innar ta buɗe mata hannu ta faɗa jikinta, ɗagowa ta yi tana kallon innar ta ce, "Innarmu ina wuni, ya gida?"
"Lafiya lau tauraruwata, ya makarantar, kin dai ci abinci ko?" Tana Æ´ar dariya ta É—aga mata kai, dama kullum ne idan ta dawo daga makaranta sai ta tambaye ta ta ci abinci,
"Je ki rage kayan jikin ki, bari na kawo maki abinci." Kai ta ɗaga mata ta wuce inda ɗakinta yake innarsu kuma ta nufi kicin, ba a jima ba Salma ta fito ta cire hijab ɗinta sai riga da wandon uniform kanta ba kallabi sai tufkar kitsonta dake naɗe, wata irin suma gare ta mai kyaun gaske daga gaban kanta ta kwanta mata luf luf, cikin barandar ta dawo lokacin innar ta iso gabanta riƙe da plate ɗin abinci ta saka mata cokali ta bata,
"Thank you best mom."
Murmushin daɗi innar ta saki Allah Ya sani tana tsananin jin son ƴar tata, ita ɗin kyautar Allah ce a gareta don gani take kamar bata isa ta haifi kamar ta ba, ganin tana ƙoƙarin zama akan tudun baranda ta nuna mata tabarmar dake a shimfiɗe ta ce ga wuri nan ta zauna, Salma ta ce lafiya lau bari ta zauna anan ɗin, ita kuma innar ta zauna a saman tabarmar.
"Ban ga su Imrana ba, ba dai basu dawo ba har yanzu?" Salma ta tambaya tana kai abinci baki,
"A'a sun dawo, na aiki Imrana kantin Mubarak ya siyo mani ɗan tsami shine Hamza ya bishi." Kai ta gyaɗa ta sake cewa, "Halan bacci Usman ke yi?" Innar ta bata amsa da kamar ta sani, ƴar dariya Salma ta yi ta ce ai kusan kullum ne idan ta dawo daga makaranta yana bacci, tana cikin cin abincin ta ƙware ta dafe ƙirji tana tari, a ruɗe innarsu ta miƙe ta nufi hanyar kicin da sauri, dawowa ta yi hannunta riƙe da ɗan babban kofi ta kawo mata, da kanta ta bata ruwan a baki, bayan ta gama sha ta ce mata ta yi haƙuri ta manta bata haɗo mata da ruwa ba, Salma tana murmushi ta furta, "Innarmu kina ji da ni sosai, shiyasa Sagir yake kishi da ni." Dariya innar ta saki tana komawa wurin zamanta ta ce to ba dole ta ji da ita ba ƴar macen tata guda ɗaya tal,
"Ai zaki ƙara haifo mana wata in sha Allahu." Waro ido innar ta yi, "Haihuwar lafiya kuma Salma, ai na gama ina laifin ku da na haifa, mun bar ma yara dai."
"Ai innarmu kema ba wani girma kika yi sosai ba, kamar ma baki haife mu ba Allah." Tana dariya ta ce ta girma mana tun da ta kai shekara arba'in.
"Amman dai Allah innarmu baki girmi haihuwa ba, kina da kyawun jiki ba wanda zai ce kin kai shekara arba'in." Shiru innar ta yi bata ce komai ba tana yar dariya.
"Ina mutumina man Sagir ko an shige gari." Salma ta tambaya, innar ta bata amsa da bada jimawa ba ya shigo ya ɗauki abinci ta tambayeta ta duba ɗakin su ne baya nan, Salma ta ce da ta shigo ta ga an ɗan turo ƙofar ɗakin shiyasa bata leƙa ba, innar ta ce to ba mamaki yana ciki yana bacci, wayar innarsu dake a cikin ɗaki ce ta fara yin ƙara, Salma har ta yunƙura zata je ta ɗauƙo mata innar ta dakatar da ita ta ce ta ci gaba da cin abincinta bari ta je ta ɗauka, lokacin da ta shiga ɗakin har kiran ya yanke, ɗauko wayar ta yi tana kokarin duba wanda ya kira ta, daidai tana fitowa wani kiran ya sake shigowa, zama ta yi akan tabarmar tare da ɗauka ta kai kunne, sallama ta yi kafin cike da girmamawa ta gaishe da wanda ya kira ta da fara'a har da ɗan rankwafawa, ɗan saurarawa ta yi kafin ta amsa da yaran duk suna lafiya gasu nan duk sun dawo daga makaranta.
"Eh hajiya....to lafiya lau ba matsala za a samu dama cikin yin ta nike yanzu haka." Ɗan saurarawa ta yi kafin ta sake cewa, "Lafiya lau hajiya bakomai a basshi." Da sauri kuma ta ƙara cewa, "A'a ba a yi haka ba hajiya." Shiru ta yi tana sauraren hajiyar da ta kira ta, daga baya ta furta to zata faɗi sai an gama, daga haka suka kammala yin wayar ta cire daga kunnanta tana murmushi tare da faɗin, "Ina ruwan hajiya.." Salma dake kallon ta ta tambayi wace hajiya ce?
"Hajiyar Ambasada ce, awara take so ta rabin tiya, wai baƙi ne suka yi mata zuwan bazata ba a shirya masu wani abincin kirki ba shine take son a haɗa masu awarar da sauce ta san za su ji daɗinta, to wai da ta tambayi kuɗin na ce ta basshi shine ta ce man to nima na bar awarar tawa." Ƴar dariya Salma ta yi,
"Mutumin da haka nan ma kullum cikin yi maka alkhairi yake, duk aka yi mata awara haka zata bada kuÉ—i fin abun da aka faÉ—a ai ba wani abu bane don an ce ta barshi." Innar ta faÉ—a tana ta murmushi,
"Yanzu wata za a yi mata daban?" girgiza kai innar ta yi ta ce, "Kawai bari sai a bata cikin wadda aka yi tun da sauri ake kada a 6ata mata lokaci, ke sai ki soya ragowan kawai." Kai Salma ta ɗaga, su Imrana ne suka dawo daga aiken, suna ganin yayarsu ta dawo suka nufo ta suna murmushi, ware ma hamza hannu ta yi ya faɗa jikinta yana dariya ta ce masu ya makaranta duk suka amsa, kallon Imrana dake tsaye gefe ta yi da murmushi ta ce, "Malam Imrana ya, yau akwai assignment ne?" Kai ya ɗaga mata kafin ya ce mata amman bashi da wahala zai iya ta jinjina kai. Bayan innar ta amshi saƙon aiken ta koma kan aikin awaran Salma ma ta bita don ta taya ta, innarsu na ta basshi ita da ta kwaso gajiyar makaranta kuma anjima zata fita suyan awara, Salma ta bata amsa da ai yau awaran bashi da yawa bazata gaji ba.