← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 197

Sashe 112

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

✨A CIKIN RAYUWA

ZAINAB BATURE

37

Bayan Fahad ya baro makarantar su Leemarh ya hau hanyar tafiya Zaria, yana driving yayin da a zuciyarsa yake tunanin abubuwan da suka wakana tsakanin shi da Leemarh, yanzu ya tabbatar da yarinyar son shi take yi, dama kuma ya riga da ya fahimci hakan, wata zuciyar ta raya mashi yanzu ya ke nan zai yi? lokaci guda ya yanke a ransa cewa ba zai karya mata zuciya ba, matuƙar ta fito fili ta bayyana tana son shi kuma da aure zai amince da hakan, a da yana tunanin hakan ba mai yuwuwa bane saboda mom ɗinta, amman yanzu yana jin ya shirya ma duk wani ƙalubale da zai fuskanta daga gare ta matuƙar ba Leemarh ɗin ce ta janye ra'ayinta akansa ba, sai dai a yanzu ya yanke shawarar ba zai nuna mata ya gane komai ba zai fi su ci gaba da tafiya a yadda suke saboda now isn't the right time a ce soyayya ta shiga tsakaninsu musamman da bata kammala karatunta na secondary ba, sai dai idan ita ce ta fito ta bayyana masa tana son sa to bai da za6in da ya wuce ya yi accepting soyayyarta. A gajiye Salma ta shigo cikin gida bayan ta yi sallama, daga cikin ɗaki ta jiyo muryar innarsu can ƙasa tana amsa mata, ɗakin ta nufa ta ɗaga labule ta shiga, murmushi ta sakar ma innarsu da ta yunƙura ta tashi daga kwancen da take, a saman kujera Salma ta zauna ta ajiye ƙatuwar jakarta a saman hannun kujera, "Sannu da dawowa." Innarsu ta faɗa tana ɗan yin murmushi, Salma ta amsa da yauwa, tambayar su Imrana ta yi innarsu ta bata amsa da sun fita bayan sun ci abinci, "Ki je kema ki ci abinci sai ki huta ko." Salma ta amsa da to kafin ta ce, "Amman innarmu kaman wani abu na damun ki?" Ta tambaya cike da kulawa, ɗan murmushi ta yi ta ce mata a'a ba abun da ke damunta, Salma ta ce, "Ko dai baki son faɗa mani innarmu, gashi nan na ga alamun damuwa a tattare da ke. Ko baki jin daɗi?" Ɗan murmushi kawai innar ta yi, ta riga ta san matuƙar akwai abun da yake damunta to Salmar tana ganewa kamar yadda itama duk yadda Salma ta so 6oye mata abu a ranta sai ta gane saboda yadda suke bawa juna kulawa, "Don Allah innarmu ki faɗa mani mike damun ki, ko nima so kike in shiga damuwa ne." Salma ta faɗa har yanayin fuskarta ya sauya, sanin idan ba ta faɗa mata ba hankalinta ba zai kwanta ba ya sa ta ce, "Ba wani abu bane, amman dai ta wani 6angaren abu ne mara daɗi, dama bada jimawa ba muka gama yin waya da auntynki Kubrah shine take sanar mani cewa aurenta ya mutu." A ɗan zabure Salma ta kai hannu ta dafe ƙirji tare da ɗan waro idanunta, da ɗan ruɗani ta furta, "Wannan ne na ukku fa innarmu?" Cike da jimami innarsu ta ɗan girgiza kai, cikin raunin murya Salma ta ce, "Wai mi yasa ake mata haka don Allah, don kawai bata haihuwa? Ai ba ita ce zata ba kanta ba ko." Har idanunta sun kawo ruwa, innarsu ta gyaɗa kai ta ce, "Ku san dai wannan matsalar ita ce ke haddasa mata mutuwar aure, tun da ni dai a iya sanina Kubra bata da wani mummunan hali da zai sa a rinƙa rabuwa da ita, mutum ce mai tsananin kirki ga iya zama da mutane, tana da aikinta mai kyau da take biya ma kanta buƙatu bata damu da ta tsaya sai miji ya yi mata abu ba balle ya ga ta zamar masa jidali. Kawai dai kin san mutane kowa da irin kalar tunanin sa, kuma kowane bawa akwai ta inda Allah Ke jarabtar shi, ita kuma ta nan jarabawar tata take, sai dai mu taya ta da addu'a Allah Ya bata ikon cinye dukkan jarabawar da yake mata." Salma tana share hawaye ta amsa da Amin, rarrashinta innarsu ta yi kan ta daina kuka ta yi mata addu'a, bayan wani lokaci ta miƙe tare da ɗaukar jakarta zata fita innarsu na ƙara bata baki, dama ta san sai abun ya saka ta damuwa musamman yadda ta damu da auntyn tata. Dakinta ta nufa ta zauna a bakin gado tare da ajiye jakarta a ƙasa tana ci gaba da goge ƙwallan dake zubo mata, sosai take jin tausayin aunty Kubra kan rashin haihuwan da Allah bai bata ba wadda kusan ita ce ke haifar mata da matsala a gidajen aurenta, wayarta ta ji tana yin ringing ta miƙe ta nufi inda ta ajiye ta a cikin drawer ɗin mirror dama bada ita take zuwa makaranta ba, tana ɗauko ta ta ga aunty Kubran ce ke kira da alama ƙilan sun yi magana ne da innarsu yanzu, komawa ta yi ta zauna tare da ɗaukar kiran ta kara a kunne a hankali ta yi sallama, amsa mata aunty Kubra ta yi ta ce, "Baby an dawo school ɗin?" Ƙasa-ƙasa ta amsa mata da eh, "Ya na ji voice ɗin ki kamar kina a cikin damuwa, kamar ma kuka kike yi ko?" Ai kaman Salma tana jira ta yi mata tambayan ta saka mata kuka, da ɗan alamun tashin hankali ta shiga rarrashinta tana tambayarta mike damunta ta faɗa mata, cikin kuka ta ce yanzu bayan ta dawo innarsu ta sanar mata abun da ya faru da ita wllh bata ji daɗi ba, murmushi mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "To kuma baby shine abun kuka sai ka ce yau aka fara ehem? Ki kwantar da hankalinki pls, ba wani abu, bawa baya wuce ƙaddararsa, ni wllh kin ganni sam ban damu ba, tabbas mutuwar aure bata da daɗi to amman idan Allah Ya ƙaddaro ma bawa ya zai yi? Sai haƙuri, ki taya ni da addu'a Allah Ya bani ikon cinye jarawabar hakan na fi buƙata kin ji baby?" Kai ta ɗaga cikin muryar kuka ta ce, "Koda yaushe ina maki addu'a auntynah, in sha Allahu in dai saboda haihuwa ne suke maki haka Allah zai baki, ƴan biyu biyu ma zaki rinƙa haihuwa." Dariya mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "Na gode baby, amman ni wllh idan ma Allah bai ƙaddaro zan haihu ba na kar6i ƙaddarata hannu biyu, kuma sunan ban haihu bane amman tuni Allah Ya yi mani kyautar ƴa'ƴa a ciki kuma ya bani ɗiya ɗaya tamkar da dubu wato babynah farin cikin zuciyana." Murmushin jin daɗin kalamanta ne ya bayyana akan fuskar Salma, ta ce, "In sha Allahu ma zaki ƙara haiho wasu, ke ce ma zaki mani yar ƙanwa mace." Tana dariya ta ce, "To Amin, amman ni gaba ɗaya ma aure ya fita daga raina baby, ba za a ce dai ai ban yi ba ko, gaskiya na haƙura da sake yin aure, zan ci gaba da yin wasu ibadun, wadda muka yi ta aure kuma Allah Ya kar6a ya yafe mana kurakuranmu." Jikin Salma ne ya yi sanyi da jin kalamanta, tambayarta ta yi ko tana da wata buƙata, Salma ta ce, "A'a aunty Kubra, bani da wata buƙata, kuma kin manta yaya Deen har ya fara turo mani kuɗin albashin da ya ce zai riƙa bani." Aunty Kubra ta ce, "Wannan naki ne baby, kuma hakan ba zai hana mu sauke responsibilities din mu ba ai." Salma na ƴar dariya ta ce to ita ya zata rinƙa yi da waɗannan kuɗin masu yawa, aunty Kubra ta ce ita ta san mi zata yi da abun ta, cike da zolaya Salma ta ce to bari ta rinƙa tarawa sai a siya mata kayan ɗaki idan zata yi aure, dariya mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "Baby ko dai aure kike so ne?" Da sauri ta ce, "A'a wllh auty Kubra ni wasa fa nike." Aunty Kubra ta ce, "In sha Allahu kayan ɗakin ma da kuɗin mu zamu yi maki su na gani na faɗa, fatan mu a koda yaushe Allah Ya baki miji na gari mai zuciya da zai kula da rayuwarki. Ko har an samu?" Da sauri ta sake ce mata a'a tana dariya, "Ina shi ɗan ball ɗin, kin fara karkato hankalinsa kan ki?" Ɗan waro ido Salma ta yi don ta gane Deen take magana, ta ce, "A'a, ni tun da ya tafi ma bai fi sau biyu muka yi magana ba shima ta chat, kuma tambayata kawai yake idan da wani abu kan aikin da ya saka ni." Aunty Kubra na ƴar dariya ta ce wasa take yi mata dama, hira suka ci gaba da yi kafin daga baya suka yi sallama aunty Kubra na jaddada mata kan kada ta sake ta saka damuwa a ranta. Maganar da suka yi da aunty Kubra kan Deen ta sa ta hawa facebook ta shiga page ɗinsa tana dubawa, ta ga bada daɗewa ba an yi posting hotunan match ɗin da suka yi a pre season shi da teammates ɗin shi, duk da kasancewar sauran da yawa duk fararen fata ne amman Deen ya fita daban a cikinsu, gaba ɗaya ya kere su kyau da ƙirar jiki, idan ka gan shi bazaka ta ba kawo wa wani abu ya haɗa shi da Najeriya ba balle ya kasance ɗan nan, yadda ya ƙulle gashin sa a tsakiyar kai wasu suka ɗan zubo daga gaban kansa ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, a ranta take raya yanzu wannan ne zata iya jan hankalinsa wai ya so ta? To ta ina ma, mutumin da ta ga yadda mata ke rububinsa amman baya kula su har ana alaƙanta shi da sunan ɗan ƙwallo mai izza da jan aji, musamman yadda ta ji cewa shahararrun mata da duniya ta sani kama daga mawaƙa, yan film, models da sauran su ke yi masa tayin soyayyarsu amman sam baya da wata budurwa da yake tare da, kamar yadda yawanci shahararrun ƴan ƙwallo suke tarayya da fitattun mata, amma shi an ce sana'arsa kawai ya saka a gaba, sai dai kuma halin sa na ƙin kula matan na burge mutane da yawa musamman musulmai, ana masa kallon ɗan ƙwallo musulmi nagari mai kiyaye dokokin Allah. Ko zancen yana da matar da zai aura duniya bata sani ba sai ahalinsa kawai, ba irin ƙorafin da Basma bata yi masa kan yadda bai bayyanata ta hanyar ko da ɗaura hotunanta ne, idan har ka ga ya ɗaura hoton ta a social media to sai dai idan na family ne amman bai ta6a ɗaura ta ita kaɗai ba ko shi da ita balle har ya bayyana wacece ita ko mutane su zargi akwai wani abu a tsakaninsu.
Chapter 112 · 0% Book details