Sashe 121
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu ƴan matan da kake tare da su ba." Fahad ya amsa mashi da bai samu wadda yake son aura ba, alhaji Sa'ad ya ce, "Ke nan duk cikin ƴan matan naka babu wadda ta yi maka?" Shiru Fahad ya yi bai ce komai ba, daddy ya ce, "To ko mu mu nema maka matar auren ne, ko a cikin family ma za a iya samu." Fahad ya ɗan ɗago ya kalle sa ba tare da ya ce komai ba, daddy ya ci gaba da cewa, "Ga ƴar'uwarka Zarah ma, ko itama ina ganin lafiya lau kaman bata da matsala in zaku daidaita, dama gashi irin abun da ka karanta itama take karanta ka ga zaku taimaka ma juna sosai." Shiru Fahad ya yi har saida daddyn ya ce bai ce komai ba, dagowa ya yi ya ce, "Daddy ina bukatan a dan kara mani lokaci." daddy ya ce, "Itama Zarah bata yi maka ba ke nan?" Fahad ya ce, "No, akwai wadda nike shirin fitarwa, tana cikin karatu ne yanzu, amman nan da zuwa next year zata gama." Daddy ya ɗan jinjina kai kafin ya tambaye shi wacece ita? Fahad ya ce, "Itama a cikin family take, idan muka gama daidaitawa I will let you know." Daddy ya ɗan yi shiru kafin ya ce mashi yana ganin za su daidaita da itan, "In sha Allah, already mun fara fahimtar juna da ita." Da ɗan murmushi daddy ya ce, "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi, nan da shekara mai zuwa ai kaman gobe ne idan muna da rabon gani. But, bana son jin wani uzuri kuma, idan ba haka ba zan yanke decision din dana ga ya yi akan ka." Fahad ya ɗan ɗago da ɗan murmushi ya ce in sha Allah za su ji abun da suke son ji, daga haka daddy ya sallame shi ya tafi. Mom Jameela zaune a dining area ita da su Leemarh da dad ɗinsu suna yin breakfast kasantuwar weekend ne, kowannen su ya yi shiga mai kyau don duk sai da suka yi wanka kafin suka zauna cin abinci, abinci kala kala gasu nan sai abun da mutum ke so zai ci, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da aroma ɗin abinciccikan ga kuma ƙamshin da jikinsu ke saki, Leemarh ta kai chips baki, bayan ta gama ci ta ɗan dakata tare da ajiye fork ɗin tana kallon dad ɗinsu ta ce, "Dad next week zamu fara exam, muna gamawa zan tafi Funtua a can zan yi hutu." Kafin dad ɗin da ya kai tea cup baki ya ce wani abu mom Jameela ta yi saurin cinye abun da ke bakinta ta ce, "Na faɗa maki baza ki je ba!" Leemarh ta ɗan 6ata rai tare da tura baki, "But saboda me?" Dad ɗin su ya tambaya bayan ya ajiye tea cup ɗin hannunsa, "Kano zata tafi, su Ammi har sun yi magana." Dad ya bita da ido kawai, Leemarh tana tura baki ta ce, "Ni ba zan je can ba, kuma yawanci duk hutu ba Kanon nike zuwa ba." Dad ya ce, "Ki barta ta je Funtua ɗin tun da can take son zuwa, kuma suma za su ji daɗi tun da an daɗe ba wanda ya je a cikin su." Wani kallo ta yi masa ta ce, "Ita Ammin da har ta yi magana sai a ce mata ya ya ke nan? Ko sai a ce mata bazata je wurin su ba Funtua za ta tafi, kana tunanin hakan daidai ne?" Shiru dad ya yi tare da kallon Leemarh, ganin ya yi shiru ta san ƙarshenta goyon bayan mom ɗin zai yi ya sa ta fara yamutsa fuska tana faɗin ita wllh Funtua zata je ba Kano ba, mom ta yi mata wani kallo ta ce, "Sai ki je ɗin." Leemarh ta dangwarar da cokalin da take riƙe da, ta mike tana ƙunƙunin ita bazata je Kano ba ta nufi hanyar ɗakinta. Bayan barin Leemarh wurin, dad ɗinsu bai ce komai ba, amman a ransa ya bari zai lalla6a mom ɗin daga baya kan ta barta ta je Funtua. Leemarh na shiga ɗakinta ta nufi gado ta faɗa, ƙwalla ne suka ciko idanunta, a hankali suka fara gangaro mata, a fili ta shiga faɗin, "Ni wllh ba wani Kano ɗin da zan je, ko dama can da nike zuwa wani lokacin ba da son raina bane mom take matsa mani..." A cikin ranta ta shiga tuna maganar da ta yi ma Fahad na cewa zata je hutu can, yanzu kuma sai ta dawo ta ce mashi mi? Kuma ita dai har cikin ranta tana son zuwa can ɗin ko ba don kowa ba don shi, tunanin mafita ta shiga yi sanin halin mom ɗinsu idan bata son abu to kuwa ba a isa a yi ba, da sauri ta yunƙura ta tashi zaune bayan zuciyarta ta bata shawarar abun da ya kamata ta yi, ta ɗauki wayarta ta fara dannawa... Hajiyar ambasada na zaune a saman kujera, bata daɗe da fitowa ba bayan Balaraba ta gama gyara falon ko ina fes sai ƙamshi ke tashi, idanunta akan Tv tana kallon labaru, wayarta dake ajiye a gefenta ta fara ringing, kai idonta ta yi kan screen ɗin wayan, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin mai kiran nata, bayan ta ɗauka ta kara a kunne ta furta, "Assalamu alaikum, Haleematu." Daga ɗayan 6angaren Leemarh ta ce, "Na'am, hajiya ina kwana." Hajiya ta amsa mata da lafiya lau tare da tambayarta duk ya suke, Leemarh ta amsa mata da lafiya lau daga haka ta yi shiru, hajiya da ta fahimci kaman da wani abu ga shi ta ji muryarta can ciki ta ce, "Haleematu ya aka yi, lafiya dai ko?" Kaman tana jira cikin muryar kuka ta ce, "Ba mom ba ce..." Hajiya ta gyara zama don wannan ne karo na farko da ta kira ta da sunan kawo ƙorafin mom din nasu, "Ina ji, mi ya faru ne?" hajiya ta tambaya, bayan ta sanar mata ɗan murmushin dattako ne ya bayyana akan fuskar hajiya, cikin alamun rarrashi ta ce, "To ki yi haƙuri Haleematu tun da ta riga ta yanke can Kano zaki je, tun da ba gama karatun kika yi ba idan Allah Ya kaimu wani hutun sai ki taho nan, idan ma ni kike so sai in zo in taho da ke." Cikin ƙuna ƙuni Leemarh ta ce, "Ni dai bana son zuwa Kanon, kuma duk yawanci duk hutu ba can nike zuwa ba, yaushe rabon da mu zo nan, ni dai nan zan zo in ma ta ƙi bari na zan je car park in hawo mota ba tare da ta sani ba." Hajiya ta ɗan buɗa ido jin maganar Leemarh, sai kuma ta yi dariya ta ce, "Shike nan ki bari zan yi magana da iyayen naki, amman kada ki sake ki ce zaki baro gida ba tare da sanin su ba." Bayan sun ɗan ƙara yin magana suka yi sallama, hajiya ta ɗan kwa6e fuska tana kallon gabanta, dama ta riga ta san rashin zuwan su nan har da mom ɗinsu, shi kuma mahaifin nasu dama ta san ba wani tsawatar mata yake ba, ya riga ya sake mata tana yin duk abun da ta ga dama, duk da bata son shiga harkar iyalin yaran nata, ta ji dole ta yi magana tun da har ga furucin da Leemarh ta yi na tahowa ba tare da sanin su ba. Dad ɗinsu Deen na cikin cin abinci wayarsa dake ajiye gefe ta fara ringing, kai idanunsa ya yi kan screen ɗin, ganin hajiyarsa ce ke kira ya sa shi yin saurin ajiye fork ɗin hannunsa ya kai hannu ya ɗauki wayar, a nutse bayan ya ɗauka ya gaishe da ita kafin ya ce mata bari ya kira, mom da ta bisa da ido tun bayan da kiran ya shigo wayarsa ta janye idanun nata don ta gane wadda ke kiran nasa daga yanayin yadda ya amsa, bayan ya kira cikin girmamawa ya shiga gaishe da ita, shiru ya yi yana sauraranta kafin ya ce, "Nima na ce a barta ta zo tun da nan take son zuwa, to ita mom ɗin tasu ta ce sun riga sun yi magana da su can suna son ta je." Mom ta juya ta yi masa wani kallo don ta fahimci zancen Leemarh suke, ɗan ta6e baki ta yi ta ci gaba da cin abun gabanta, can dad ya ce, "Eh, gata nan." Cire wayar ya yi ya miƙa ma mom Jameela, ta wani kalle sa fuska a ɗan yamutse ta tambayi waye kamar irin bata san wanda ya kira ba, ya bata amsa da hajiya ce ke son magana da ita sannan ta amsa, da ɗan girmamawa ta gaishe da ita ta yi shiru tana sauraranta, yanayin fuskarta ne ya sauya ta ce, "Ba haka bane, Ammi ta riga ta buƙaci ta je masu hutu ne, yanzu idan kuma aka ce bazata je can ba ga inda zata je tana iya ganin ba a yi mata daidai ba kan abun da ta isa da shi." Daga ɗayan 6angaren hajiya ta ce, "Ni kuma Jameela ba zan ga an yi mani ba daidai ɗin ba? Yaushe rabon da yaran nan su zo nan? Yanzu kuma wata a cikin su ta nuna tana son zuwa nan sai a hana ta? Mi hakan ke nufi?" Da ɗan sauri mom ta ce, "No hajiya, ni fa ba ina nufin komai ba, kawai don ita Ammin da kanta ta riga ta buƙaci ta je can ne, idan aka yi wani hutun sai ta zo nan ai." Hajiya ta ce, "Tun da ta nuna nan take son ta zo kuma sun ɗauki lokaci basu zo ba, bari zan yi magana da Ammin na san zata fahimta." mom ta ɗan yi shiru jin abun da hajiya ta ce na zata yi magana da Amminsu, dama duk shirinta ne hakan ba wata Ammin da ta buƙaci Leemarh ta je hutu, hakan ya sa ta ɗan yi saurin cema hajiya shike nan Leemarh ɗin zata zo ita zata yi magana da Ammin, cikin haɗe rai ta ajiye wayar bayan sun gama, ta watsa ma dad wani kallo kafin ta miƙe ta bar wurin. Dakin Leemarh ta nufa, sai dai koda