Sashe 106
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna komawa cikin falo wayar Zarah dake riƙe a hannunta ta fara yin ringing, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin Deen ne ke kira, bayan ta ɗauka ta kai kunne tare da yin sallama, ɗan saurarawa ta yi can ta ce, "Kai yaya Deen kuma, ai da ka bar shi pls." Tana murmushi ta ce mashi sun gode Allah Ya ƙara ɗaukaka, cire wayar ta yi ta kalli mummy ɗin su da duk idanunsu na akan ta jin ta ambaci sunan Deen, murmushi ta shiga yi ba tare da ta ce komai ba, aunty Murja ta tambaye ta ya aka yi, ta ce wai kuɗi ne ya turo ta account ɗinta ya ce su raba da su Nabeela da Nabeel, mamaki ne ya bayyana kan fuskar aunty Murja ta ce kuma bayan saƙon da ya ce za a kawo gobe na su, zama ta yi kan kujera kusa da Dr tana yaba hali irin na Deen, ta ce, "Wallahi ina son yaron, akwai hankali da natsuwa, wasu idan suka samu ɗaukaka sai su guji nasu amman shi sam ba haka yake ba, burin shi a koda yaushe ya yi ma nashi har ma da wanda ba nashin ba. Allah ya ba yaya Ibrahim ɗa ɗaya tamkar da dubu." Dr Mustapha ya ce, "Ni abun da ya fi burge ni da shi natsuwar shi, sam ɗaukakarsa bata sa ya gur6ata rayuwar sa ba, duk da ba tare da shi muke ba amman da gani bana tunanin yana aikata wani abu ba daidai ba, kuma ina ganin yadda mutane ke yabon halinsa a social media." Aunty Murja ta ce ai gaskiya zata iya shaidar sa kan hakan, basu jima ba suka bar falon kowa ya nufi 6angarensa, saman gado Nabeela ta faɗa tana ta faman washe baki ta ce, "Nima dai zan yi iphone in huta da wulaƙancin da kike mani idan na ce ki bani aron naki in yi pics, ko idan zan je wani wuri na ce ki ara mani in je da shi don in yi pictures." Ƴar dariya Zarah ta yi ta ce itama ta huta da takura matan da take yi, "Gaskiya ya Deen yana da kirki, wallahi ba ƙaramin burge ni yake yi ba, ga kyau, ga kuɗi, ga ɗaukaka, ga kuma kirki duk shi kaɗai." Zarah ta faɗa tana murmushi bayan ta zauna a bakin gado, "Ni kin san mi ya fi burge ni a tattare da shi?" Nabeela ta faɗa, Zarah ta girgiza mata kai, "Wannan gashin na shi, da ni zai aura wllh har kitso zan rinƙa yi masa." Dariya Zarah ta yi ta ce, "Yanzu idan ya ce yana son ki zai aure ki zaki amince." Nabeela ta ce, "Da gudun tsiya ma, ke idan ya ce yana son ki ba zaki amince ba." Zarah ta ɗan rausayar da kai ta ce, "Zan amince mana, ai bana tunanin akwai wata mace da zai ce yana so ta ƙi amincewa wllh, dole a tattare da shi akwai abun da zai saka mace ta so shi." Tashi zaune Nabeela ta yi tana kallon Zarah ta ce, "Amman an ce ai yana da wadda zai aura ko?" Kai Zarah ta ɗaga, "Yea, cousin ɗin sa ce wadda yake zaune wurin su a London, kuma wllh baki ganta ba, ba zan ce bata da kyau ba amman don a can take ne, da ace anan ƙasar take to sam basu dace da juna ba nesa ba kusa ba." Shiru Nabeela ta dan yi don ita wallahi bata ƙi ya ce yana son ta ba to da sai ta aure shi, "Kina da pic ɗin ta?" Ta tambaya, Zarah ta ce mata da dai tana da amman yanzu babu, Nabeela ta ce, "Zan so in ganta, gaskiya ta dace." Zarah ta ce ta bari zata yi ma Leemarh magana ta tura masu, cike da zaƙuwa ta amsa da ok. Bayan Deen ya koma hotel shirin kwanciya ya yi don ba ƙaramar gajiya yake tattare da ita ba, bayan ya kwanta ya ɗauki wayarsa yana ɗan duba saƙonnin dake gare sa, bai yi mamakin ganin saƙon yabon tallafin da ya yi ba daga wurin mom ɗin sa, ya san saboda garinta ne, har da saƙon gaisuwa da Salma ta turo masa ta whatsApp ya yi mata reply ɗin godiya, bai jima ba ya ajiye wayan saboda baccin da yake ji. Washe gari kafin Deen ya bar Kano sai da ya siya ma su Zarah dukkanin abubuwan da suka ce suna so tare da shi aka kai gidansu lokacin ma duk basu nan, dama maganar kawo saƙon ce ya yi ma maigadi a jiya da zai bar gidan, shima maigadin sai da ya yi mashi kyautar kuɗi masu yawa da har sai da ya zubar da ƙwalla, kamar ba zai koma gidansu mom ba daga baya dai ya je ya yi masu sallama. Wuraren ƙarfe biyar ɗin yamma ya baro kano, lokacin da ya iso Abuja gaba ɗaya ƴan gidansu ne suka zo tarbarsa har da mom ɗin shi. A cikin kwanakin da suka rage Deen ya koma London sosai ya ba su Leemarh lokaci, a nan Abuja ma sai da aka ƙara yin wata gasar ƙwallon da shi. Ranar asabar da yamma sai ga Fahad ya yi masu zuwan bazata don yin bankwana da Deen da zai tafi washe gari lahadi, farin ciki sosai Leemarh ta yi har ta kasa 6oyewa, a 6angaren mom ɗinsu kuwa kamar dai ko yaushe babu yabo babu fallasa ta tarbe shi, koda ta ji cewa don ya yi bankwana da Deen ya zo har da cewa ai da ba sai ya zo ba in don wannan ne a waya ma za su iya yin bankwanar, shi dai bai biye ta ba dama har da gudun matsala ya sa shi bai zo da motar da Deen ya bashi ba, don ya san muddin ta ganta sai ta ɗarsa zargi a zuciyarta kuma sai ta bi diddiginta. A daren ranar Fahad da Deen da su Leemarh suka fita outing, zagaya gari suka yi suka je wurare daban daban cike da nishadi, har da haɗaɗɗu kuma tsadaddun wuraren sayar da kayan ƙwalam da maƙwalashe suka je suka siya abubuwa, daga baya suka wuce babban mall Deen ya ƙara yi masu shopping, har Fahad ma sai da ya siya masu abubuwa, sai wuraren goma na dare suka koma gida, bayan sun koma kowa part ɗinsa ya wuce ba wanda ya nemi abinci don duk a ƙoshe suke, Fahad tare da Deen suka wuce part ɗin sa kowa ya yi wanka, Leemah na zuwa part ɗinta itama wanka ta shiga, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar bacci, da ta gama shiryawa ta fito ta wuce kitchen, Fahad da Deen na zauna a cikin falonsa a saman kujera mai mazaunin mutum ukku, dukkan su kayan bacci ne a jikinsu Fahad riga da wando Deen kuma robe da ta bayyanar da faffaɗan chest ɗinsa, gaba ɗayansu sun ɗan kishingiɗa a saman kujeran idanuwansu akan tv suna kallon ƙwallo, jin an turo ƙofa ya sa a kusan tare suka kai idanuwansu direction ɗinta, Leemarh ce ta shigo ciki hannuwanta riƙe da ɗan tray a sama mugs ne tiriri na ɗan fitowa, nufo ciki ta yi idanunta akansu ta fara yin ɗan murmushi, tana zuwa kusa da su gyalen da ta ɗauro a saman kanta ya zame ta fara ƙoƙarin ganin bai faɗi ba, sai dai ta kasa tsayar da shi saboda abun da take riƙe da a hannunta, miƙewa Fahad ya yi ya tarbe mata gyalen kafin ya ƙarasa faɗuwa ƙasa, ɗagowa ya yi suka haɗa ido tana murmushi ta ce, "Thank you ya Fahad." Ya ɗaga mata kai, miƙa ma Deen da ke kallon su mug ɗaya ta yi ta ce, "Ya Deen ga coffee na haɗa maku." Amsa ya yi da murmushi akan face ɗinsa ya yi mata godiya, juyawa ta yi ta kalli Fahad da ke tsaye gabanta riƙe da gyalenta shima ta miƙa masa ɗayan mug ɗin ya ɗauka ya miƙa mata gyalen, tana ta murmushi ta ƙara yi masa godiya, komawa ya yi ya zauna tare da nuna mata gefensa alamar ta zauna, Deen da ya fara kur6ar coffee ɗin ya ɗan dakata yana murmushi ya ce, "Albarkacin Ya Fahad nima na samu coffee ɗin ke nan." Da sauri ta saka hannunta ɗaya ta ɗan rufe bakinta tana dariya, bayan ta cire ta ce, "No yaya Deen kawai na haɗo maku ne, kuma na san ai kana sha duk dare." Ya ɗage gira ya ce, "Amman ai baki haɗa mani." Cikin kame kai tana ɗan murmushi ta ce to ai bai saka ta ta haɗo mashi shi yake haɗawa ko ya saka chef Alima ta haɗa masa, Fahad da ke kallonta murmushi ne akan fuskarsa yana shan coffee ɗin, kallon shi ta yi suka haɗa ido duk kunya ta kama ta kan maganar da Deen ya yi, bayan ɗan lokaci aka kira Deen a waya ya ɗauka yana amsawa tare da miƙewa hannunsa riƙe da mug ɗin ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, shiru na ɗan ƙalilan din lokaci bayan tafiyar Deen, Leemarh ta juya ta kalli Fahad da har lokacin bai ƙarasa shanye coffeen ba, janye idonsa ya yi daga kan tv ya maido su kanta suka haɗa ido, tana murmushi ta ce, "Ya Fahad dama ina son maka godiya.." Ɗan ɗage gira ya yi tare da janye mug ɗin daga bakinsa calmly ya ce, "Na mi?" Ta ce, "Na kayan da ka siya mana." Shiru ya ɗan yi yana kallonta kawai, can ya ce, "Kin yi ma Deen godiyan shima?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a, "Then why ni zaki yi mani." Shiru ta yi kawai tana ɗan murmushi don ya ɗaure ta, "Ko muna da bambanci ne ni da shi?" Da sauri ta girgiza masa kai, ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Mom ta tura kofar ɗakin Leemarh ta shiga tana sanye da kayan bacci, daga bakin ƙofar ta tsaya tana bin cikin ɗakin da kallo, ganin wayam bata ganta a ciki ba ta kai idanunta wurin da toilet yake, ciki ta ƙarasa shiga ta nufi kofar toilet ɗin ta ɗan dakata kafin ta kai hannu ta yi knocking, bayan ta ƙwanƙwasa