← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 197

Sashe 188

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

auren Salma da za a zo a ranar juma'a mai zuwa, gaba ɗaya ganin abun suke kamar mafarki ba gaske ba, Sageer ya fi kowa yin farin ciki tamkar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha, ji yake kamar ya juya ya ciji kunnansa don daɗi, a yadda aunty ta shirya za su taho Funtua kafin ranar Friday don a yi shirin tarbar baki da ita, to sai baban su Salma ya ce ba a nan gidan za a tarbe su ba, a gidan yayan shi Alhaji Sani nan za a sauke su, kuma Alhaji Sanin ya ce a bar mashi duk wani shirin tarbar su can za su yi, hakan ya sa aunty ta bari sai ranar juma'a ɗin za su taho. Duk abun nan mom bata san da maganar za a je neman auren Salma ba, don ba yadda dad bai yi ba ya rarrashe ta ta amince ma auren amma ta rantse ta maya ba zai auri yarinyar ba. A can London kuwa bayan Deen ya koma ya samu daddy Maleek da maganar haɗa auren Basma da Salma, amman daddy ya ce mashi ya ci gaba da shirin auren Salma yanzu ita Basma ya bari za su yi magana daga baya, sosai Basma ta nuna masa tashin hankali bayan ya koma, tai ta yi mashi kuka akan Salma, ya samu ya rarrashe ta tare da sanar da ita cewa tare zai aure su, hakan ya ɗan sa hankalinta ya kwanta, dama ita ba wani zafin kishi ta sani ba saboda a irin rayuwar da ta taso, ita dai dama burinta kawai Deen ya aure ta. Rana bata ƙarya...ranar juma'a bayan an taso daga sallar juma'a daddy Sa'ad da kawu Hamida suka isa gidan yayan baban su Salma wato alhaji Sani, gidan ba laifi yana da ɗan kyau don Alhaji sanin ya fi baban su Salma wadata, a sitting room ɗin gidan aka tarbe su da abubuwan ci da sha, kuma daidai gwargwado an yi ƙoƙari, Alhaji Sani da wani ɗan'uwan su malam Lawan suka tarbe su, cikin mutuntawa da girmama juna aka gaggaisa daga baya suka shiga gabatar da abun da ya kawo su kamar yadda ake yi a al'ada, su daddy Sa'ad suka ce bayan neman aure har da saka rana suke so a yi idan zai yuwu, alhaji Sani ya bayyana farin ciki ya ce idan ma har da auren suke son a ɗaura a nan take su ba matsala a wurin su, cike da nuna jin daɗi su kawu Hamida suka yi godiya, nan suka bayyana nan da wata biyu suke son a saka auren amma ba sai an tsaida rana ba saboda yanayin aikin Deen, yadda suka tsara idan Allah Ya kaimu nan da wata biyun sai a kira rana kawai, su Alhaji Sani suka nuna amincewa da hakan, daga baya su daddy Sa'ad suka bada goro mai yawa da suka zo da su, sai kuma kuɗi miliyan ɗaya matsayin kuɗin neman aure da sauran abubuwan da ake kawowa na saka biki, wanda kuɗin daddy Sa'ad ne ya bada su don basu buƙaci komai ba daga wurin Deen ko mahaifinsa, bayan gama saka ranan daddy Sa'ad ya isar da saƙon da hajiya ta bashi na cewa ba a buƙatar komai da ya danganci kayan ɗaki, wannan magana ba ƙaramin daɗi ta yi ma su alhaji Sani ba, nan sukai ta yi masu godiya da addu'oin ƙarin girma da arziki, har da mahaifin su daddy Sa'ad da ke kwance ƙasa wato anbassador sai da ya sha addu'oi, bayan kammala saka ranan suka matsa masu sai da suka ɗan ci abubuwan da aka tanadar masu don da sun ce a ƙoshe suke ruwa da lemu kawai za su sha. Bayan tafiyar su daddy Sa'ad, alhaji Sani da malam Lawan suka kwashi goron da kuɗin da aka kawo a motar alhaji Sani suka nufi gidan su Salma, a nan cikin baranda aka yi shimfiɗa duk mutanan gidan suka zo suka gaishe da su, daga baya malam Lawan ya shiga yi masu bayanin yadda suka yi da su daddy Sa'ad, suka nuna masu goron da su Sageer suka shigo da su tare da basu kuɗin da aka bada, kowa ka gani a wurin bakinsa ya ƙi rufuwa tsabar farin ciki, sai ma da alhaji Sani ya sanar da su zancen ba a buƙatar komai na kayan ɗaki, wayyo daɗi! Farin ciki ne ya ƙara cika su, innarsu Salma har da ƙwallan daɗi, shima baban su sai faman murmushi yake yi yana ƙara godiya ga Allah, ana cikin haka sai ga su Aunty Kubra sun shigo, su Imrana suka saki ƙarar murnar ganin yayar su, da gudu suka nufo ta, Salma ta wara masu hannu tana ta dariya, jikinta ta sha gayu da ɗaya daga cikin abayas ɗin da Deen ya kai mata, jaka da takalman ƙafarta ma duk na cikin kayan ne da suka hau da rigan, sai ta yi kamar wata tauraruwa tsabar yadda ta yi kyau, Sageer ya nufo ta yana washe baki, yana zuwa gabanta ya kama hanci yana yin guɗar shaƙiyanci, duk ya saka mutane dariya, ya rungume Salma yana faɗin, "Welcome amaryarmu." Aunty Kubra na tsaye bakin baranda riƙe da hannun Imrana da Hamza, jikinta ta sha doguwar rigar leshi mai ɗan banzan kyau, ta yi wayayen ɗaurin kallabi yayin da idanuwanta ke sanye da bakin glasses da ya matukar ƙawata fuskarta ya ƙara fito da haskenta, ta kai hannu tana cire glasses ɗin tana amsa sannu da zuwan da innarsu Salma ke yi mata da fara'a, ƙarasawa suka yi cikin barandar tuni har baban su Salma ya yi mata shimfiɗa, ta zauna da faffaɗan murmushi suka shiga gaisawa da baban su Salma da su alhaji Sani suna yi mata an zo lafiya, Sageer ya ƙaraso cikin barandar yana riƙe da hannun Salma da ke ta bin kowa da kallo tana sakin murmushi, cire hannunta ta yi a na Sageer ta nufi innarsu, innar nata sakin faffaɗan murmushi tana kallon ta ta ce, "Salma.." Ta ce, "Na'am innarmu.." Ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana murmushin daɗi don duk ta yi missing ɗin su, innarsu ta ɗago ta suka zauna, ta kalli baban su da ke ta kallon ɗiyar tashi fuskarsa cike da farin cikin ganin yadda ta canza, Salma ta gaishe da babanta tare da su alhaji Sani, duk suka amsa mata da fara'a suna kiran ta da amarya, ta yi saurin sauke kanta ƙasa tana ɗan murmushi, bayan gama gaishe gaishe innarsu Salma ta ce ma aunty ai sun yi zaton ganin su tun ɗazu, aunty ta ce mata wllh sun ɗan samu delay ne a motor pack basu taso da wuri ba, "Aunty ai da kawai kin tuƙo ku a motar ki." Sageer ya faɗa, tana murmushi ta ce har yanzu tsoron yin dogon driving take duk da daga Kadunan zuwa nan ba wani nisa sosai amman tana tsoron hawa babbar hanya, Auwalu da ke zaune a tudunkar baranda ya ɗan rankwafa kai yana gaishe da ita, ta amsa tare da ambaton sunan sa, alhaji Sani ya ce masu to su dai suna ganin za su tafi yanzu, aunty ta kalli kayan dake gefe ta ce, "Ko har baƙin ma sun zo?" Alhaji Sani ya ce mata eh har lokaci an saka, nan ya yi mata bayanin komai har da kayan ɗaki da aka ce ba a buƙata, tsabar daɗi aunty bata san lokacin da ta rangaɗa guɗa ba a wurin, duk aka saka dariya, cike da zolaya baban su Salma ya ce ashe wannan gajeran hancin nata zai iya guɗa haka, aunty ta juya tana kallon Salma da ta raku6e gefen innarsu, tana murmushi ta ce, "Babyna an zama amarya..." Da sauri suka ga ta miƙe ta shige cikin ɗakin innarsu duk suka yi dariya, "Ma sha Allah, Allah shine abun godiya, wllh tsabar farin ciki ji nake kamar na zuba ruwa ƙasa in sha...Allah Ya tabbatar mana da alkhairi ya nuna mana lokacin...Alhamdulillah, baby kam sai son barka don ta cika mai sa'a wllh." Aunty ta faɗa tana ta faman washe baki, Alhaji Sani ya ce, "Tabbas, don haɗa zuria da iyalan marigayi Ambasada ba ƙaramar sa'a ba ce, to bare kuma auran shi yaron, ban da ɗaukakar da Allah ya yi masa, ko'ina ana shedarsa da halin kirki, ai ba abun da zamu yi ma Allah sai godiya, Allah Ya kai mu lokacin da rai da lafiya." Duk aka amsa da Amin, malam Lawan ya ɗan gyara zama ya ce, "Ina son zan ɗan bada wata shawara....ina ganin zai fi a rufe al'amarin nan a bar shi iya dangi kawai, a bari koda za a bayyana sai lokacin ya zo, don yanzu rayuwar ta zama abun tsoro, kai kana zaune da kowa lafiya baka riƙi kowa da wata mummunar manufa ba, amman wani yana nan ba wanda yake jin haushi irin ka, kasancewar ka lafiya da ɗan rufin asirin da Allah Ya yi maka su suke ci masa tuwo a kwarya, wani kuma lafiya lau kuke da juna, amman wani abun arziƙin na samun ka sai wutar hassada ta ruru a zuciyarsa, har ta kai ya kasa jurewa ya fara neman yadda zai raba ka da abun ta ko wane hali, shiyasa yake da kyau a koda yaushe mu kasance muna masu yin addu'ar neman tsari da hassada..." Kowa ya amince da shawaran kawu Lawan, alhaji Sani ya bada misali da yadda akai ta yayata zancen soyayyar Salma da Deen a kafafen sada zumunta da maganganun da mutane sukai ta yi na nuna mamakin yadda ya iya yin soyayya da ita ana faɗin sana'ar da take yi, aunty Kubra ta juya ta kalli Auwalu da Sageer ta ce, "Kun ji ko, maganar saka ranar auren ta tsaya iya nan, kada wanda ya yaɗa a social media har sai Allah Ya kaimu lokacin." Duk suka ce ba zasu yaɗa ba, ta kalli Imrana da Hamza ta ɗan kama kunnanta alamar gargarɗi ta ce, "Ku ma kada wanda ya sake ya faɗa ma wani cewa an saka ma yayar ku Salma ranar aure!" Duk suka ɗaga kai suka ce ba zasu faɗa ba, daga haka su yaya Sani suka yi sallama, baban su Salma ya yi saurin cewa to ai ko abinci ba su ci ba, alhaji Sani ya
Chapter 188 · 0% Book details