Sashe 195
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tabarma don cikin akwai zafi ba wuta." Tana ƙoƙarin juyawa a tsawace mom ta ce, "Dakata malama...a tunanin ki kuna da wurin da zaku bani in zauna a cikin wannan akurkin gidan!" Innar su Salma ta bita da kallo da yanayin ruɗu, a ranta ta shiga tunanin to wai wannan wace irin baƙuwa ce suka yi haka, lokaci guda ta yanke anya baƙuwar su ce kuwa, ɗan murmushin yaƙe innar su Salma ta yi ta ce, "To Allah Ya baki hakuri hajiya, amman ina ganin kamar dai kin yi kuskuren kwatance ba nan kike nema ba." Kafin mom ta ce wani abu Salma ta ɗan matsa, ƙasa da murya ta furta, "Mom ɗin yaya Deen ce..." Ƙirjin innarsu ya buga da ƙarfi, mom ta yi wani guntun murmushi da baida alaƙa da farin ciki ta ce, "Good, gashi nan ɗiyar ki ta tabbatar mani ina a right place ban yi kuskure ba, kuma da a ce a cikin ku ba wanda ya san ni wacece hakan zai saka mani shakku a kan zargin mallake mani ɗa da kuka yi, yanzu kuwa na kara tabbatar da zargina...ban zo don in 6ata lokacina akan ku ba don baku cancanci hakan ba, idan mahaifinta na nan ki kira shi don yana buƙatar jin abun da ya kawo ni, idan kuma baya nan sai ki isar masa da saƙo idan ya dawo..na zo ne don in gargaɗe ku in kuma ja kunnan ku akan tun wuri ku raba ɗiyar ku da ɗana, ku janye batun wani aure a tsakanin su, kamar yadda bada sanina aka saka wai ranar aure tsakanin su ba, akan hakan zan ci gaba da kasancewa, wato ban san da zancen ba don ban haifar ma wata mai awara shi ba, bama ita kaɗai ba, a duk garin nan babu sa'ar auren shi..." Juyawa ta yi ta kalli Salma, da sauri Salma ta sauke idonta ƙasa bugun zuciyarta na ƙara tsananta sakamakon kalaman ta, tana sakin wani shu'umin murmushi ta ce, "Ƴan mata mai awara, a yi haƙuri a cire ran auran ɗana, domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, yana da matar aure da na za6a mashi, warce take ƴar dangi, ƴar arziki, sannan ƴar gata gaba da baya, wadda ko matsayin mai aikinta ba zaki samu ba balle wai ki zama kishiyarta, don haka tun wuri ki sama ma kan ki salama, ki yi gaggawar cire shi a ran ki idan baki son ciwon zuciya ya yi ajalin ki, don wllh matuƙar ni ce mahaifiyarsa ba zai ta6a auren ki ba!" Lokaci guda Salma ta fashe da kuka ta yi saurin kai hannu ta rufe bakinta, daidai nan Imrana ya shigo ɗaukan awara, yana ganin abun da ke faruwa ga yayarsa tana kuka, da gudu ya koma waje, majalissar da su Sageer ke zama ya nufa, cikin rawan murya ya ce, "Yaya Sageeru ga wata mata can a gidanmu tana ta faɗin maganganu, har yaya Salma nata kuka." Wata zabura Sageer ya yi ya miƙe yana tambayarsa wace mata ce, Imrana ya ce shima bai santa ba, wata fara ce mai kaman aljanu, tare da abokan sa su Ibrahim da Aliyu suka nufi gidan, Sageer kamar zai tashi sama don kusan da taƙi taƙi yake yin tafiyan tsabar saurin ya isa gidan...mom ta koma kan innarsu Salma tana faɗin, "Ina mai ƙara jaddada maku da ku cire ran auren ƴar ku da ɗana, ku raba su babu shi babu ita, haka idan ma wani ƙulli kuka yi ma ɗana to ku yi gaggawar warware shi don na fi ku iya tijara...a yanzu cikin lumana na zo maku, idan kuma kuka ƙi ji to ba kwa ƙi gani ba, don zan ɗauki mummunan matakin da baku taba zato ba....idan ma baya ga matsiyacin mutum da shegen ƙarfin hali, ina ɗana ina wannan ƴar taku da har zaku yi tunanin haɗa alaƙa da shi ban da shegen ƙwaɗayin tsiya..." Da sauri Sageer da ya iso gaban su ya katse ta da faɗin, "A'a hajiya....gaskiya mu ba matsiyata bane...ai babu matsiyaci sai wanda bai san ubangijinSa ba balle yadda zai bauta masa, mun dai yarda mu talakawa ne, kuma hakan ba yana nufin mun zama abun wulaƙantawa ba, saboda Allah ne ke son ganin mu a haka, idan da ya so muma zai iya bamu arziƙin tun da nashi ne ba na wani ba, kuma da mai arziƙi da talaka ba wanda ya fi wani a wurinsa face wanda ya fi bauta masa, kuma Alhamdulillah a haka ma muma masu arziƙi ne tun da ya bamu rai da lafiyan bauta masa, sannan bamu rasa ci ba bamu rasa sha ba balle sutura...tabbas mu talakawa ne amman masu wadatar zuci, ki bincika a duk faɗin garin nan ba ma unguwar nan kaɗai ba, ba wanda muke zuwa mu roƙi wani abu a wurin shi ko mu yi masa maula, muna da ƙarfin zuciyan neman na kan mu bamu dogara da kowa ba, kuma ko shi ɗan naki zaki iya tambayarsa idan mun ta6a roƙon wani abu a wurin sa, balle har ki yi tunanin ƙwaɗayin abun sa muke....sannan mu ba mushirikai bane, bamu ta6a zuwa wurin malami kan wata buƙata ba balle kuma boka, mun wadatu da tauhid ta yadda duk wata buƙatar mu kaitsaye wurin ubangiji muke kai ta sanin shi kaɗai ake bauta mawa kuma ake neman taimako, kuma a cikin mu ba wanda ya roƙi Allah ya haɗa ƙanwarmu da ɗan ki, addu'ar za6in alkhairi muke mata a koda yaushe wurin Allah, shi ne ya haɗa ta da ɗan ki, don haka idan baki son alaƙar su wannan tsakanin ki ne da ubangiji ba mu ba, kuma ɗan ki shi ya ce yana son ta ba ita ba, tun da kina da iko da shi ai shi zaki sa ya rabu da ita ba mu ki zo mana nan ba, tun da mu miye namu a ciki, ku sa waɗanda suka zo neman auren ta su dawo su janye, ba abun da hakan zai rage mu da shi, kuma ai gari da yawa Allah zai kawo mata wani, ba wai don ɗan ki bai aure ta ba hakan na nufin zata rasa mijin aure...." Tun da ya fara maganganun innarsu ke ta ƙoƙarin dakatar da shi ta hanyar kiran sunan shi amman ya ƙi ya yi shiru sai da ya kai aya, fuskar shi a murtuke yana ta ɗan hucin 6acin rai, Salma sai kuka take yi itama tana ce mashi ya yi shiru don Allah, mom dai still ta yi ta zuba mashi kaifafan idanunta har ya gama, tana jin tun da take ba wani mai tsaurin idon da ya ta6a tsayawa gabanta ya gaya mata maganganun irin haka, gashi a wasu maganganun nashi ya yi sara a kan ga6a ba tare da ya sani ba, sai mom Jameela take ganin kamar ya san wani abu game da ita, shine ya yi amfani da hakan ya gaggaya mata magana, juyawa ta yi kan innar su dake ta bata haƙuri kan maganganun Sageer tana cewa yaro ne, wani shu'umin murmushi mom ta saki ta kai hannunta da ya sha gold ta ɗan kama kunnanta ta ce mata tana fatan ta ji gargaɗin da ta zo masu da shi, da sauri innar su Salma ta ɗaga mata kai, mom ta saki kunnanta tare da faɗin, "...Kowa ya zauna lafiya..shi ya so!" Daga haka ta juya kan Sageer da ke tsaye yana ta hura hanci, ta ɗan yi murmushi irin na yaro bai san wuta ba ɗin nan, ta ce, "Na ji duk maganganun ka, sai dai ka sani kaf dangin ku babu sa'ar yi na...amman ka jira, daidai da yin ka za su zo su same ka." Har zata juya sai kuma ta dakata tana kallon Salma da fuskarta ta yi sharkaf da hawaye, tana ɗan murmushi ta ce, "Ƴan mata mai wara, kin ji gargadin da na yi maki akan ɗana ko?" Salma ta ɗan yi shiru sai kuma ta ɗan jinjina kai, mom ta furta, "Gud...idan kunne ya ji, to gangar jiki ta tsira!" Daga haka ta juya ta nufi ƙofa, su Aliyu da ke tsaye suka yi saurin bata hanya, da sauri innar su Salma ta ce ma Sageer mi ya sa ya saka mata baki ya yi maganganun da ya yi, a zuciye cikin karyewar murya Sageer ya ce, "To wai innarmu shike nan shi talaka bai da galihu, da kowa ya sai ya nemi taka shi a lokacin da ya so, kamar shi ne ya zabi kasancewa talakan, ko kuwa su da Allah Ya ba arzikin dama ya basu ne don su wulaƙanta wanda bai ba ba, ina ya basu ne don su taimaki wanda bai da shi don samun rabauta, kuma shima wanda Allah bai ba ban aka san mi ya tanadar masa gobe, kuma ai mune masu babban arziƙi tun da bamu wulaƙanta kowa, mun san darajar ɗan adam....ta hana ɗan nata auren ta ta ga idan hakan zai rage mu da wani abu...wllh ba wanda zan zuba ido ya zo har gida ya nemi wulaƙanta mu akan abun da ba laifin mu ba don kawai muna talakawa, kuma daɗin abun ma ai bamu ta6a zuwa neman taimako ko maula a wurin mutum ba..." Duk maganganun nan da ya ƙara yi akan kunnan mom Jameela da ta dakata a bakin zaure, wata uwar ƙwafa ta yi daga haka ta fita daga gidan, Salma ta zame ƙasa akan gwiwuwinta ta shiga yin kuka sosai, a zuciye Sageer ke ce mata dalla kada ta damu kan ta, idan ta sa ɗan nata ya fasa auren ta Allah zai iya kawo mata wani wanda ma ya fi shi...mom Jameela na fita su Ibrahim suka rufa mata baya, tsaye suka yi a ƙofar gidan suna kallonta ya yin da take tafiya, gaba ɗaya wani irin haushinta ne ya turnuƙe masu zuciya, tana cikin tafiya ta buɗe ƴar jakar hannunta ta fiddo waya, kira ta yi tare da yin magana a taƙaice, daidai tana zuwa bakin hanya baƙar jeep ɗin da suka zo da ita ta faka gabanta, aka buɗe mata ƙofa ta shiga daga haka suka tafi, Ibrahim na ganin ta tafi ya shiga latsa wayarsa zai aiwatar da abun da ya shirya....bayan wasu mintuna Auwalu ya