← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 197

Sashe 168

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sati biyu Deen ya dawo Nigeria tare da daddy Maleek da iyalan shi, a gidan Maleek da ke nan Abuja su Sapna suka sauka. Bayan kwana biyu da dawowar Deen aka yi bikin naɗin shi a garin Daura, dama saboda naɗin ya dawo, sosai al'umma suka halarci bikin naɗin har da dad dinsa da daddy Maleek, ƙaninsa Omar ma da yana a ƙasar ya je, daga can Funtua ma daddy Sa'ad da su Khaleel da sauran ƴan'uwa da abokan arziƙi duk sun halarta, sosai hotuna da videon naɗin suka karaɗe kafofin sada zumunta, Deen ya yi wani irin kyau na musamman a cikin shigar sarauta mutane ana ta santin kyaun da ya yi, yayin da mata ke ta bayyana burin son mallakar sa matsayin miji. Bayan kwana biyu da yin naɗin aka shirya gagarumar dinner a Abuja, duk ƴan familyn su na Kano da Funtua sun zo, har Fahad ma ya zo saboda dinner ɗin, Leemarh ta yi farin cikin zuwan shi sosai, katafaren ballroom ne za a yi dinner ɗin a ciki, an yi ma wurin tsadaddan decoration mai aji, da tsarin zama na table a tsakiya da kujeru zagaye, tsarin da aka yi a wurin na da matuƙar ɗaukar hankali...ko ta ina a wurin ƴan madara zaka gani, da manyan mutane da naira ta zauna masu, dad ɗin Deen da daddy Sa'ad da Maleek tare da abokan su manyan mutane da masu muƙaman gwamnati 6angaren su daban, haka mom da nata jama'ar suma wurin su daban, har Ammin su mom da su Bash duk suna a wurin, haka hajiyar ambasada da wasu dangi ƴan Funtua suma suna a wuri guda, wasu cikin abokan Deen yan team ɗin shi turawa sun zo da kuma yan team din Nigeria da suka buga world cup duk suna a wurin, Leemarh da Omar ma duk sun yi inviting abokansu, wuri dai ya cika da mutane ƴan gayu da jikin su ya jiƙu da naira, matan wurin ankon tsadaddan lace suka yi, kalan na iyaye daban haka ƴan mata ma nasu kalan daban, suma mazan sun yi ankon tsadaddan yadi, Naila tare da ƙanwarta Aseey wasu irin matsiyatan fitted gown aka yi masu, gaba ɗaya an ci mutuncin tsadaddan leshin, duk in da suka yi sai sun ja hankalin mutane saboda surar su da shigan da suka yi, Basma da Leemarh ɗinki iri ɗaya aka yi masu straight skirt da riga da suka fitar masu da shape ɗin su, Sadeeya da su Zarah da Nabeela yaran aunty Murja ƙanwar dad su ɗinkin su da mutunci don dogayen riguna aka yi masu. Lokacin da Zakin Wasannin Ƙasar Hausa ya bayyana a wurin gaba ɗaya idanu suka koma kan shi aka shiga bin shi da kallo cike da burgewa, gaba ɗaya shigar fararen kaya da farin rawani ya yi, a sama ya ɗaura wata rantsattsiyar golden akyabba da ta gama haduwa tana ta ƙyalli, a hannun shi ya riƙe sanda irin na sarauta wadda daga samanta aka yi design ɗin kan zaki, idan ka ga sandar zaka yi tunanin ta gold ce saboda yadda take ɗaukar ido, watakila ma ta gold din ce dai, gaba ɗaya yan matan wurin sun kasa janye idanunsu daga kan Deen saboda yadda ya tafi da imaninsu, Basma jikinta har wani tsuma yake tsabar yadda ya tafi da ita, ta rinƙa jin ina ma a lokacin su ma'aurata ne...a wurin da aka tanadar ma Deen ya zauna gefe da gefen shi bodyguad ɗin sa biyu suka tsaya, wasu irin narka narkan mutane da su masu suffar ban tsoro, daga sama har ƙasa duk sun yi shigar baƙaƙe ko fuskar su ba a gani...gaba ɗaya cikin wurin ya karaɗe da sautin daddaɗar waƙar da aka yi ma Deen mai amshin sarautar shi ta Zakin Wasannin Ƙasar Hausa, sosai waƙar ta yi ma mutane daɗi ba kamar amshinta wasu har ɗan bi suke, a wuri ɗaya Nailah ta zauna tare da Basma, haka duk inda zata yi a cikin wurin tana tare da ita riƙe da hannunta, Leemarh ta so su zauna tare da Fahad sai dai yana tare da wasu abokansu ƴan Funtua sun zauna a wuri ɗaya, Nabeela ɗiyar aunty Murja hankalinta na akan Khaleel ƙanin Fahad da ke zaune tare da su Omar, lokaci lokaci suke kallon juna suna sakar ma juna murmushi don soyayya suke ba tare da an sani ba, shima Omar ƙanin Deen hankalinsa na kan Zarah, jefi jefi suke haɗa ido su yi ma juna murmushi, su ma ku san soyayya suke yi duk da bata yi nisa ba, ba a daɗe ba da ya fara nuna mata so, sai dai ita Zarah gani take kamar ya yi mata ƙarami saboda su ɗin ku san age mate ne, duk da dai tana jin son shi...a kowane table an ajiye menu wato katin da ke ɗauke da jerin sunayen abinciccikan da ke akwai a wurin, sai abun da mutum ke so za a kawo masa, shi kan sa katin na naɗin sarautar ne har da hoton Deen a jiki, ma'aikatan abinci nata kai kawon kai ma mutane, manyan mawaƙan arewa har da na kudu ne ke perfoming a wurin, komai na dinner ɗin cikin aji ake gudanar da shi...bayan gama yin bayanan taya murna da Allah sanya alkhairi daga bakunan wasu makusantan Deen aka shiga yin hotuna. A kafafen sada zumunta dinner ɗin ce ke ta trending mutane nata tofa albarkacin bakin su wanda duk yabo ne...jikin Salma duk ya yi sanyi laƙwas yayin da take zaune a saman gado tana kallon hotuna da videos na dinner ɗin, ita kanta yanzu shakku take kan anya aure zai yuwu tsakaninta da Deen ganin irin mutanen da ke kewaye da shi, duk da ta san dama su ɗin masu arziƙi ne, amman a yanzu sai take ganin shi ɗin ya fi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amman kuma da ta tuna shi da bakinsa ne ya furta yana son ta sai ta ɗan ji ƙwarin gwiwa....a cikin hotunan dinner ɗin kawai sai ga hoton Deen da Basma an saki tare da bayyana dangantakar su da kuma kasancewar ta fiencee din shi, ai fa nan social media ta ɗauka mutane suka shiga cece ku ce, wasu suna faɗin sam basu dace ba don ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, yayin da wasu ke cewa ai itama ba mummuna bace tana da kyaunta ga kalar fatarta mai tsada kuma daga ganinta arziƙi ya zauna mata, wasu suna faɗin ƙaton baki gare ta da ƙananun idanu, yayin da wasu ke nuna su shape ɗin bakin ma nata ya burge su, haka dai mutane ke ta faman musayar ra'ayi akan Deen da Basma....sosai gaban Salma ya shiga faɗuwa data ga hotunan Deen da Basma da kuma bayyana ta matsayin wadda zai aura da aka yi, gashi kana ganin hotunan ba zaka ƙarya ta hakan ba don hada waɗanda ta kama shi, sosai hankalin Salma ya tashi taita kallon hotunan hannunta har ɗan rawa yake, a zuciyarta take raya ke nan ita ba son ta ya ke ba da gaske, ƙilan haka nan ya faɗa mata hakan don ta ce ba wanda ya yi mata da zata aura a cikin masu son ta, to amman mi yasa zai ce mata hakan bayan yana da wadda zai aura, idanunta suka cicciko da ƙwalla yin wannan tunanin, ta raya ita ya zata yi yanzu don wani irin son shi ke addabar zuciyarta, ƙwallan ne suka fara zubo mata sharr, a hankali ta kai kwance ƙwallan na ci gaba da gangaro mata a fuska tana ɗan kai hannu tana sharewa, bayan wani lokaci ta miƙe tana ƙara goge idanunta, wayarta ta ɗauka ta sauka daga saman gadon tana tafiya jikinta kamar babu laka, aunty Kubra na zaune a saman gado ta jingina da kan gadon, jikinta sanye da kayan bacci hannunta tana riƙe da wayarta, ta ɗaga kai jin an buɗe kofar ɗakin, Salma ce ta shigo suka haɗa ido a hankali ta sauke kanta ta nufo cikin ɗakin, daga bakin gadon ta tsaya aunty nata kallonta ganin damuwa bayyane a kan fuskarta, a hankali ta ce, "Baby ya aka yi?" A sanyaye ba tare data kalle ta ba ta ce, "Dama zuwa na yi in nuna maki..." Ta faɗa tana miƙa ma aunty wayarta hannunta har ɗan rawa take, bayan aunty ta amsa wayar ta bi hoton Deen da Basma da kallo, ita kanta yanzu nan take ganin hoton, itama hankalinta ya tashi da ganin haka abun kuma ya ɗaure mata kai, ɗago idonta ta yi tana kallon Salma da har lokacin kanta na a ƙasa, hannunta aunty ta kama ta zaunar da ita a bakin gadon, cikin kwantar da murya ta ce, "Nima yanzun nan nike ganin hotunan nasu, na yi mamakin hakan....amman ke bai yi maki maganar wannan ɗin ba?" Salma ta girgiza mata kai ta ce yadda ta faɗa mata haka suka yi da shi, aunty ta yi shiru tana kallon wuri guda, bayan ɗan lokaci ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina ganin kada mu yi saurin yanke masa hukunci, da ba son kin yake da gaske ba haka nan ba zai furta maki hakan ba. Abu biyu nike tunani a raina, ko dai dama akwai maganar wannan ɗin, ko kuma daga baya maganar shi da ita ta taso tun da naga familyn su ɗaya, yanzu abun da ya fi mu jira mu ji daga gare shi, na san uzururruka ne suka sa bai neme ki ba." Ta ƙarasa tana kallon Salma da ta yi shiru idanunta ƙasa, aunty Kubra ta bi ta da ido ganin yadda duk ta shiga damuwa, hannu ta kai ta dafa shoulder ɗinta cikin kwantar da murya ta ce, "Don't worry my baby, ba abun da zai faru sai alkhairi, kaman yadda na faɗa maki a baya cewa idan shi rabon ki ne kina zaune zai furta maki so sai gashi kuma hakan ya faru, to haka ma idan Allah Ya ƙaddaro shi ne mijin ki, babu wani abu da zai zama shamaki ga faruwan hakan, mu ci gaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Salma ta ɗaga mata kai a hankali, shiru suka ɗan yi, aunty duk bata jin daɗin hakan dake faruwa a cikin ranta musamman ganin damuwar da
Chapter 168 · 0% Book details