Sashe 82
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari Friday Deen ya zama busy sosai saboda gobe asabar ne bikin buɗe sabon club ɗinsa, da yamma wasu daga cikin baƙin da za su halarci bikin suka fara zuwa, yawanci ƴan kwallo ne na clubs daban daban daga wasu jahohi, tuni an kama masu masaukin da za su zauna dama, da daddare bayan sallar isha'i Salma ta zo gidan hajiya, tana shigowa harabar ta hango Deen daga can gefe wurin parking space zaune da wasu mutane, nufar hanyar shiga cikin gidan ta yi, "Salmerh.." Kafin ta ƙarasa ta ji an kira sunanta ta juya, Deen ta gani ya nufo ta ta tsaya idonta akan sa, a cikin ranta raya bata ta6a jin wanda sunanta yake daɗi a bakinsa ba irin shi, daga gabanta ya tsaya tana ɗan murmushi ta gaishe da shi, bayan ya amsa ya ce mata hajiya sun fita ba kowa a ciki, ledar hannunta ta ɗago ta ce, "Gashi aka ce in kawo maka." Kallon ledan ya yi ya maido idon shi kanta ya ce, "Awaraa?" Murmushin kan fuskarta ya ɗan fadada saboda yadda ya faɗi sunan ta ce mashi eh, kai ya jinjina ya ce mata thank you kafin ya ce ta kai mashi ciki idan ya gama da mutanen da yake tare zai je ya ci, ta amsa da to har za ta juya ta dakata ta ce, "Maganar aikin an samu mutum ukku da za su yi, amman innarmu ta ce a tambaye ka yanayin yawan abincin da za a rinƙa yi don a san mutane nawa za a ɗauka." Shiru ya ɗan yi kafin ya ce su yi magana da hajiya ita zata faɗi yanayin yadda za a rinƙa yi har da salary da za a rinƙa ba su, Salma ta ce to ta na murmushi ta ce bari ta kai mashi abun ciki, ya amsa da ok tare da ce mata, "Gud nyt." Daga haka ya juya ya koma wurin mutanen, bayan ta kai mashi kamar yadda ya ce ta fito ta wuce gida. Washe gari asabar misalin karfe sha ɗaya na safe aka fara bikin buɗe sabon club ɗin a stadium ɗin garin, wanda ya samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na wasu states da ma waɗanda ba ƴan kwallon ba masoyan Deen, cikin manyan mutane masu muƙami da suka halarta har da commisioner matasa da wasanni na jahar Katsina, da Executive Director Katsina State Sport Council da wasu stakeholders, hikimin garin, ɗan majalissar jaha da sauran manya masu muƙamai a garin duk sun halarta, dad ɗin shi ya so zuwa amman wani uzuri ya taso mashi a can Abuja da ya sa bai samu halarta ba amman daddyn su Fahad ya halarta kuma shine matsayin wanda ya wakilci mahaifinsa, hajiya da momyn su Fahad da sauran ƴan gidan duk sun zo, tare da sauran ƴan'uwa da abokan arziƙi, wuri ya cika da al'umma wasu ma don kawai su ga Deen suka zo, su Sagir ƴan wasan sabon club duk sun yi shiga cikin sabon jerseys da takalma, bayan buɗe taron da addu'oi an gabatar da jawabai daban daban wanda suka ƙunshi yabo, ƙarfafa gwiwa da fatan alkhairi, an yi abubuwan nishaɗi da suka haɗa da kaɗe-kaɗe sannan an gabatar da wasannin gasa tsakanin wasu ƙungiyoyi da sabon team ɗin inda a ƙarshe suka samu nasarar zuwa na biyu, an bayar da kyaututtuka sannan an rarraba abubuwan ci da sha, daga ƙarshe Deen ya yi bayani game da dalili da kuma abubuwan da yake burin cimmawa a sabon club din, ya bayyana burin sa na faɗaɗa tare da inganta club ɗin ta yadda ba a iya ƙasar kawai za su rinƙa buga wasa ba, ya kuma bayyana niyyar sa ta gina ma club ɗin stadium mai zaman kansa a garin ba da jimawa ba. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya, bayan kammala taron ne manyan baƙi da kuma shuwagabannin sabon club ɗin da ƴan wasa suka yi walimar cin abincin rana, an ci an sha an gode ma Allah. Sagir zaune a tsakar gida sam ya kasa rufe bakin sa, kasancewar sa a sabon club ɗin Deen a ganinsa mafarkinsa na zamowa shahararren ɗan ƙwallon ƙafa ya fara tabbata, gaba ɗaya ƴan gidan da wasu sun halarci bikin suna a kewaye da shi dukkan su suna cikin farin ciki sosai, Salma nata murmushin farin ciki tana kallon kyaututtukan da aka bashi kasancewarsa ɗaya daga cikin ƴan wasa da suka nuna hazaƙa wanda suka haɗa da kayan ƙwallo da takalma har da lambar yabo, "To, Allah Ubangiji Ya sa albarka, Ya sa an hau matakin nasara. Allah Ya albarkace ku Ya inganta rayuwar ku baki ɗaya." Babansu ya faɗa da faffaɗan murmushi, kusan a tare suka haɗa baki wurin amsa addu'ar mahaifin nasu, itama innarsu ta yi masu addu'a baki ɗaya, saboda farin cikin da suke ciki abinci na musamman aka yi a gidan har da kaji da lemuna, su Imrana ba baka sai kunne, bawan Allah saboda sadudar da ya yi da suna cin abincin har cewa ya yi da a ce Habu na nan sai ya di6ar masa cikin abincin shi ya kai mashi har gida, maganar shi ta ta6a zuciyoyinsu musamman Salma sai da ta ji ƙwalla sun tarun mata a ido, Sagir ne ya ce, "Da yana nan ɗin ba za kai hakan ba, sai dai da ana dawowa." Wani kallo Imrana ya yi masa bai ce komai ba. Washe gari lahadi wuraren ƙarfe sha biyun rana Sagir na cikin yin bacci a ɗakinsu ringing ɗin wayarsa ya tashe shi, ɗan tsoki ya yi don ya ji haushin katse masa baccin da kiran ya yi, ganin bai san lambar da ake kiran da ita ba ya sa shi saka wayar a vibrate, komawa ya yi ya kwanta bayan kiran ya yanke sai ga wani ya sake shigowa, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗago tare da ɗaukar wayan ya yi picking, yana niyyar yin magana ya ji an yi sallama da wata nutsattsiyar murya, daidaita zaman wayar Sagir ya yi kafin ya amsa shima a nutse sa6anin farko da ya yi niyyar yin magana a fusace, "Sageer, how are you doing?" Ɗan waro ido Sagir ya yi sai kuma ya yunƙura ya tashi zaune sosai yana amsawa, "Pls idan ba damuwa ina son yin magana da Salmerh if she is around." Kan Sagir ne ya ƙulle jin ana neman Salma ta wayarsa abun da ba a ta6a yi ba, yana son tambayar wanene amman kuma ya kasa don muryar ta yi masa ƙwarjini sosai, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarsa yana jin kamar ya san muryar kuma bai sha wahalar gane muryar da ta wa ta yi mashi kama ba, sai dai bai tunanin abu mai yuwuwa ne a ce Deen Jr ya kira wayarsa yana neman kuma Salma, dama su basu da lambarsa iya manyan ƙungiyarsu ne ke tuntu6arsa game da komai, miƙewa ya yi ya nufi cikin gidan bayan ya ce ma mai kiran bari ya kai mata, yana akan kiran bai yanke ba har Sagir ya shiga cikin gidan ya fara ƙwala ma Salma kira, innarsu dake a tsakar gidan ta ce mashi tana ɗakinta, a daidai bakin ƙofa suka haɗu ya miƙa mata wayar ya ce ana son magana da ita, ɗan jim ta yi tana kallon screen ɗin wayar, ta kalli Sagir ɗin a hankali ta ce masa waye, ya ɗan ta6e baki haɗi da ɗage kafaɗa ya ce mata oho, a ɗarare ta kai wayar kunne tare da yin sallama, tana jin muryarsa ta gane nan take ta saki ɗan murmushi, da hannu Sagir ya yi mata alamar waye ta ƙi ta ce komai ta shige cikin ɗakinta, after few seconds sai gata ta fito daga cikin ɗakin ta nufi Sagir da ke a kusa da innarsu bayan ta kira shi tana tambayar wa yake kiran Salma ya ce mata bai sani ba, miƙa masa wayar ta yi kafin ya ce wani abu innarsu ta riga shi cewa, "Waye ya kira ki?" Tana murmushi ta ce, "Yaya Deen ne wai cewa ya yi idan bani komai yana son gani na." Waro ido Sagir ya yi with surprise all over his face ya ce, "Deen!" Kai Salma ta ɗaga masa still tana murmushi, da alama mamaki ya kashe Sagir, ya sake cewa, "Ke, miye haɗin ki da shi da har yake neman ki ta waya?" Ganin yadda mamakinsa ya bayyana ya sa Salma yin dariya ta ce, "So na yake..." Wani kallan kallon kina hauka zaki fadi haka ya jefa mata, innarsu da ke kallon su dariya ce akan fuskarta, Salma ta ce, "Da gaske nike..." Wata dariyar kin raina mini wayo ya yi ya ce, "Baki da hankali yarinya, Deen ɗin ne zai so ki?" Sai lokacin innarsu ta saka baki ta ce, "Ka raina ta ne kake ganin ba zai iya son ta ba? Mace ce fa." Yana dariya ya ce, "Yo innarmu in dai mata ne wannan ya saba ganin su kala-kala, ƙarshe ma shi da yake rayuwa a cikin turawa, mata masu aji da kyau rububin shi suke sai ya tsaya cewa yana son wannan." Innarsu ta ce, "Ai abun baya a nan Sagir, sai ka ga duk su bai ga kyaun so ba sai ita, kuma dai kaima kasan Salma ba daga baya ba indai kyau ne, sannan shi so wani lokacin ba ruwansa da kyau, sai ka ga wani abun daban ne game da ita ya burge shi." Wata dariya Sagir ya yi ya ce, "Innarmu ko mi zaki ce ba zan ta6a yarda wai Deen Jr zai iya son wannan yarinyar ba." Ƴar hararar shi Salma ta yi tana murmushi ta ce, "Ka raina ni, kana ganin ba zan iya sa shi ya kamu da so na ba?" Yana dariya sosai ya ce, "Har abada kuwa ba zaki iya sa Deen wai ya so ki ba, idan kuma har kika iya yin nasarar hakan ni kuma na rantse da Allah daga lokacin zan koma ce maki yaya Salma." Dariya ce akan fuskar Salma irin ta ka san ba zaka iya abu ba ka dai faɗa ne kawai, innarsu ta ce, "Ki je wataƙil jiran ki yake kada ki biye ma Sagir." Juyawa ta yi ta koma ɗakinta don ta shiryo, matsa ma