Sashe 25
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A nutse take taka matattakalar benen yayin da take saukowa daga sama ƙafafunta na sanye da slippers masu taushi irin wanda ake yawo a cikin gida, cikin babban falon ta shigo tana sanye da nightgown iya gwuiwa da ta bayyana ɗan dirinta na matashiyar budurwa, kanta ta saka hula yalwatacciyar sumarta ta fito gefe da gefen kanta ta ƙulle ta da ribbom ta baya, kunnawanta na sanye da ƴar barimar diamond. A yanayin halitta ba za a kira ta fara ba, kana kallon ta ka san baƙa ce, sai dai daga yanayin fatarta yadda take sakin sheƙi ta fallasa ba ƙaramin hutu da jin daɗi take a ciki ba, sam ba wata kyakkyawar a zo a gani bace amman kuma ba za a kira ta da mummuna ba, tana da ƴar doguwar fuska mai ɗauke da ƙananun idanu da madaidaicin hanci da bashi da tsawo sosai, tana da ɗan babban baki mai ɗauke da manyan labba, yadda yanayin shape ɗin labbanta suka fita sun yi kalan ƴan gayu. Bin cikin falon ta yi da kallo sai kuma ta ci gaba da yin tafiya, bangaren mom ɗinta ta nufa, ɗan madaidaicin falo ta shigo da shima ya tsaru da kayan zamani, ganin bata a ciki ta wuce bedroom ta buɗe kofar ta shiga, nan ma wata aljannar duniyar ce guda, duk da ɗakin baya da hayaniya amman an zuba tsaddaddun kayan alatu a ciki, ganin nan ma mom ɗin bata nan ta nufi bakin kofar toilet ta ƙwanƙwasa tare da furta, "Mum, are you in there?" Jin Shiru ta ƙara kiran sunan mum ɗin, nan ma shiru hakan ya sa ta gane bata ciki ta juya ta nufi hanyar fita, babban falon ta dawo ta wuce kaitsaye zuwa study corner don ta san bata wuce tana can, tana shiga ta hango su zaune ta tsaya daga bakin ƙofa, cikin sigar shagwa6a ta furta, "Mum, dad..." A tare suka juya suka kalli direction ɗin da take, lokaci guda murmushi ya bayyana akan fuskokinsu ganin ɗiyarsu ɗaya tal da Allah Ya basu wadda ta kasance mafi soyuwa kuma sanyin idaniyarsu, hannu Maleek ya miƙa mata ta nufo su, a gefen shi ta zauna bayan ta kama hannun nashi, yana kallon ta ya ce, "Baby, haven't u slept yet?" Ta ɗan yamutsa fuska ta furta baccin ya ƙi zuwa, cike da kulawa idanunsa akan fuskarta ya ce ko wani abu na damunta? A hankali ta ɗan girgiza masa kai tare da kwantar da kanta a gefen kafaɗarsa, Sapna da ta maido duk attention ɗinta kan ɗiyar tata, tana ɗan murmushi ta ce, "Ko dai duk missing ɗin Deen ne?" Ɗan murmushi ne ya bayyana kan fuskar Basma ta maida idanunta ƙasa ba tare da ta ce komai ba, "Haka ne baby?" Maleek ya tambaya yana ɗan leƙen fuskarta, ɗago idonta ta yi da ɗan alamun damuwa ta ce har yanzu basu yi magana ba tana ta kira da daren nan but no response, kallon juna suka yi shi da Sapna, ba sai an faɗa masu ba sun san yadda take tsananin son Deen, hannu ya kai ya dafa kanta yana murmushi ya ce kada ta damu ya san ya yi busy ne sosai shi yasa bai samu damar su yi magana ba, musamman da ya ɗan daɗe bai je Nijeriya ba gashi a daren nan aka yi masa welcome dinner,
"Yakamata ma ki saba da hakan, tun da ko yana a nan ba wani cika samun lokacin kan sa yake ba." Nodding kai Basma ta yi jin maganar mum ɗinta, har da hakan nema ya sa take yawan yi masa uzuri tana ɗaukar rashin bata kulawan da yake har da lokaci da bai da shi sosai. "Na tura maki saƙo kin gani." Maleek ya tambayi Basma, ta ɗago tare da ɗaga mashi kai ta ce masa thank you, Sapnah ta tambaye shi saƙon miye, ya ce ba wani abu bane ta ce tana buƙatan kuɗi ne shine ya tura mata, wani kallo ta yi ma Basma da itama take kallon nata cike da kama kai, mamakin mi zata yi da kuɗi ne Sapna ta shiga yi don ba a fi kwana biyar ba da ta buƙaci kuɗi a wurinta kuma ta bata masu yawa, bayan haka duk ƙarshen wata kowa a cikin su ke tura mata kuɗi don yin buƙatun kanta. Tabbas ta san kashe kuɗin Basma yana yin yawa, amma sanin ɗiyar tata na da son yin gayu da tsadaddun kaya ga kuma kyauta da take da ita musamman ga ƙawayenta yasa bata damuwa ta san duk anan kuɗin ke tafiya, wannan tunanin ya sa ta share bata ce komai ba, itama ta yi ma Maleek godiya da fatan ninkuwar arziƙinsa, yana murmushi ya ce ai su nauyinsa ne komai ya yi masu hakkinsa ne don haka no need sai sun rinƙa masa godiya, Sapna ta ce duk da hakan ai an ce yaba kyauta tukuici to godiyan ne yake serving as tukuicin, murmushinsa na dattako ya yi kafin ya ce su je su sha coffee, Sapna ta ce "Amman ba ka ce aikin da kake mai muhimmanci bane kuma na gaggawa, ka ci gaba da aikin ka, bari in raka baby part ɗinta." ƙoƙarin miƙewa ya fara yi yana riƙe da hannun Basma ya bata amsa da, "All work and no play...." Basma ta ƙarasa masa karin maganar da faɗin, "....makes Jack a dull boy." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, itama ta kama ɗayan hannun Basma ta yadda sun saka ta a tsakiyar su suka nufi ƙofar fita gwanin burgewa....
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 9
....Bayan sun fito cikin babban falon, kaitsaye tea corner dake a wani bangaren falon suka nufa, nan ma wurin kan shi wata duniyar ƙawa ce, akwai babban teburin gilashi mai salo na zamani, saidai ba irin tebur bane da aka saba gani, wannan interactive glass coffee table ne, teburin yana da touchscreen surface gaba ɗaya. Idan aka taba saman gilashin sai haske ya kunnu ta ƙarƙashin glass ɗin, ya bayyana ƙananun menu icons tamkar wayar hannu, ana iya amfani da shi wajen buɗe Internet wato mutum zai iya browsing, duba email ko labarai kai tsaye a saman teburin. Sannan ana iya kallon hotuna ko bidiyo daga wata na'ura kaman waya, ta hanyar yin connecting ɗin bluetooth ko Wi-fi su bayyana a saman teburin, sannan za a iya matsar da hotunan ko vedio da yatsa, a zagaya ko a faɗaɗa su. Banda waɗannan kuma za a iya kunna waƙa da bidiyo, sannan teburin yana haɗe da tsarin sautin gidan (surround system), ta yadda idan aka kunna waƙa daga teburin sauran kayan sautin gidan suma za su kama ko ina za a ji. Ana iya yin wasanni wato games ta teburin sannan akwai app dake bada damar kashe fitilu,daidaita labule ko kunna AC duk daga saman gilashin. Ta ko ina dai a gidan fasaha ce ke aiki. Bayan sun iso cikin tea corner ɗin, Maleek ya ce su zauna shi zai haɗo masu coffee, a saman kujerun dake zagaye da coffee table ɗin suka zauna, Basma ta ce mashi ita hot chocolate take so ya ɗaga mata hannu ya ce, "Alright baby...." Hannu ta kai saman glass ɗin teburin da idan ba a cikin yin amfani dashi a ke ba yana nuna wasu artistic wallpaper, wato wani zane mai motsi tamkar ruwa da kuma mai kaman walƙiya, wanda hakan yana sa shi ya zama abin kallo ko da ba a kunna shi ba, game ta buɗe ta ce ma mom su yi kafin a kawo masu, gefe a cikin wurin Maleek ya nufa wanda a wurin akwai na'urar haɗa coffee da sauran abubuwan sha, da kuma china cabinet dake ɗauke da kufuna iri-iri da kayan haɗa abubuwan sha daban-daban, komai na wurin dai ya gama tsaruwa, within few minutes ya gama haɗa masu, Basma ya fara kai ma hot chocolate ɗin ta, bayan ta amsa ta furta, "Thank you, one and only dad." Ya wani kashe mata ido, a waje wanda bai san shi ba zai ce bai da irin barkwanci haka saboda yadda fuskarsa ke cike da ƙwarjini da haiba, bayan ya ɗauko masu coffee ɗinsu shi da Sapnah, a nutse duk suka fara sha, bayan wani lokaci ya kai hannu saman teburin, menu icons suka bayyana ya buɗe in da jerin karatuttukan alqurani suke, karatun alaramma Ahmad Sulaiman Kano ya kunna don tana daga cikin ƙira'oin da yake su gashi kuma ɗan garinsu, kan ka ce me gaba ɗaya kayan sautin falon suka kama karatun cikin madaidaicin sauti mai kwantar da zuciya da saka natsuwa....