Sashe 6
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Bro Deen, pls gobe ka kaimu school friends dina na ta son su gan ka da na faɗa masu zaka zo, wasu ma sun ce sai sun zo nan gidan sun gan ka ku gaisa." Shiru ya yi idonsa akan Leemah da ta yi maganar yana ɗan murmushi, magiya ta shiga yi masa akan ya kai su, Sultan ma ya ce shima abokansa na son shi sosai kuma suna ta son ganin shi, haɗuwa suka yi suna roƙon shi akan ya kai su makarantar, Leemah har da duƙawa ƙasa a gaban sa, su Dad sai dariya suke masu, amsa masu ya yi da zai duba ko da ba goben ba zai kai su, sallamar da suka ji an yi ce ta saka su kai idanunsu gaba ɗaya kan ƙofar shigowa, wani matashin mutum ne ya shigo, a yanayin halitta dogo ne kusan zasu iya yin kai ɗaya da Deen, baida jiki yanayin shi irin na ƴan gayun fulani da hutu ya zauna masu, amman kuma duk da rashin jikin shi sam baida sirantaka, jikinsa na da ɗan cika ta yadda riga da wandon jeans din da yake sanye da su sun kar6e shi sosai, yanayin hasken fatarsa da kuma sumar kansa sun fallasa kasancewar shi bafullatani, duk da bai kai hasken su Deen ba amman kuma shima ba baƙi bane, saidai ya fi wasu daga cikin ƴan gidan su Deen ɗin haske kamar Omar da Sultan hasken mutumin ya fi nasu, ba kamar Deen da Leemah ba da suka fi kowa fari a gidan don sak kalar fatar mahaifiyarsu suka ɗauko, itama Batool tana da haske tafi su Omar da Sultan amman kuma ba ta kai hasken Deen da Leemah ba,
Leemah da bata kai ga miƙewa daga durƙuson da ta yi a gaban Deen, tana ganin mutumin da ya shigo ta yi saurin miƙewa, nufar shi ta yi muryarta da alamun mamaki ta furta, "Ya Fahad!" Bin ta da wani mugun kallo mom ɗin su ta yi ganin yadda take rawar jikin ganinsa, ba tun yanzu ba tana jin haushin yadda Leemah ke rawar ƙafa duk in ta ga Fahad, kwanaki can baya har tsare ta ta ta6a yi kan ta faɗi mata ko akwai wani abu a tsakaninsu, Leemah ɗin ta ce mata ita ba wani abu kuma miye don tana nuna murna in ta ganshi ba ɗan'uwanta bane, kuma matsayin yayanta tun da ɗan yayan mahaifinta ne, a lokacin kashe ma mom ɗin nasu baki ta yi da amsar da ta bata dama kuma Leemah tsagera ce.
Deen na ganin wanda ya shigo shima ya yi saurin miƙewa yana sakar masa murmushi ya nufe shi, dad dake zaune sai murmushi yake ganin Fahad ɗin, tsaye Leemah ta yi a gaban shi tana sakar mashi murmushi ta ce, "Sannu da zuwa yaya Fahad, ashe zaka zo?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, Deen na ƙarasowa ya nufe shi tare da ɗan rungumo shi yana yi mashi sannu da zuwa, bayan ya ɗago Fahad ɗin ya amsa mashi tare da yi masa an zo lafiya, kamo hannunsa ya yi yana faɗin su shiga ciki, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin turaren jikinsa mai daɗin ƙamshi da sanyaya zuciya yayin da suke ƙarasa shigowa ciki, a saman kujera ɗaya suka zauna, dad dake kallon shi fuskar shi ɗauke da murmushin ganin ɗan yayansa, da ido kawai mom din su ta bi su saidai a cikin ranta sam bata jin daɗin yadda su Deen ke rawar jiki akan Fahad din,
"Daddy ina wuni." Fahad din ya gaishe da shi a nutse, da faffaÉ—an murmushi ya amsa. "Lafiya lau son, ya hanya? Ya ka baro duk mutanen Funtua?" Amsa masa ya yi da Alhamdulillah duk suna lafiya suna gaishe da su, maida idon shi ya yi kan mom din su Deen itama ya gaishe da ita.
"Yauwa, an zo lafiya." Ta amsa babu yabo babu fallasa, ba tare da ya maida idonsa a kanta ba a taƙaice ya amsa mata da lafiya lau, kallon Deen ya yi suka sakar ma juna murmushi,
"Our football star, sai ga ka a ƙasarmu." Fahad din ya faɗa, ƴar dariya Deen ya yi ya ce, "I thought zan ganka cikin wanda suka zo welcoming ɗina a airport." Hannu ya kai ya ɗan shafi gashin fuskarsa da ke a kwance ya sha gyara tare da ɗan gyara zamansa ya ce mashi aiki ne ya ruƙe shi ya yi ƙoƙarin ya taho da wuri,
"Daga wurin aikin ma ka taho ke nan?" Dad ya tambaya, Fahad ya É—aga kai ya bashi amsa da eh,
"To ya aikin? Ana dai ƙoƙari yadda ya kamata ko?" Kai ya jinjina ma Dad alamar eh, addu'ar Allah ya taimaka ya yi masa suka amsa da Amin har da Deen, Leemah ce ta shigo hannunta ruƙe da madaidaicin tray a saman shi glass jug ne ɗauke da ruwan lemu da cup, kallon mamaki mom ta bita da shi don ba wanda ya lura da lokacin da ta fice daga falon, ɗan tebur ɗin dake a gefen kujera ta dauko ta ɗaura tray ɗin, da kanta ta tsiyaya masa lemun ta miƙa mashi tana murmushi ta ce gashi ta san yana buƙatar shi tun da ya yo tafiya mai nisa, jin abun da ta ce ya sa shi kallonta suka haɗa ido ya sakar mata murmushi kumatunsa duk suka ɗan lotsa alamar yana da dimples, amsar cup ɗin lemun ya yi tare da yi mata godiya.
"DaÉ—i na da Leemah wani lokacin akwai hankali." Da sauri ta kalli daddynsu da ya yi maganar, É—an tura baki ta yi, "Daddyyy, you mean wani lokacin bani da hankali ke nan?" Ta tambaya ta É—an É—aure fuska tare da tura baki,
"Haka ne mana." Kafin Dad ɗin nasu ya bata amsa Omar ya faɗi hakan, kallo mai kaman harara ta wurga masa dama ita ke bi mashi ba su cika jituwa ba, a faɗace ta ce, "To an ji ɗin." Gaba ɗaya Omar ɗin ya bata haushi don sai ta ji an muzanta ta a gaban Fahad, kallon dad din su ta yi ganin yana ƴar dariya ta ƙara ƙulewa kaman zata yi kuka ta ce, "Dad, you are the one who caused it and yet you are laughing." Maganar tata duk ta basu dariya, yana kallonta ya ce to shi mi ya yi ai ba a ji ya ce bata da hankali ba Omar ne ya faɗi hakan, tura baki ta yi tana ƙyaƙkyafta idanu, ta nufi jikin hannun kujerar gefen da Fahad yake ta zauna, ganin ya ruƙe lemun bai fara sha ba ya sa ta ce mashi ya sha mana, ya kai cup ɗin bakin shi ya fara kur6a a hankali, mom dai bakinta ya mutu sai bin Leemah take da ido ganin yadda take nema ta wuce gona da iri, sai ka ce ita kaɗai yake ɗan'uwanta da za ta yi ta faman rawan jiki haka,
"Amman dai ya Fahad kwana zaka yi ko?" Shiru ya ɗan yi ya dakata da shan lemun, kallonta ya yi bayan ya kawar da idonsa ya ce mata yau zai koma saboda aiki gobe, a shagwa6e ta ce, "To ba sai ka ɗauki excuse ba, yaushe rabon da ka zo nan gidan ka kwana." Ɗan murmushi kawai ya yi, Deen ya ce, "Pls ka bari sai gobe, dama akwai welcome dinner da aka shirya saboda ni sai mu je har da kai..." Tun kafin ya rufe baki mom ta tari numfashinsa, "To in bada shirin kwanan ya zo ba miyasa zaku matsa masa ne sai ya kwana? Ba ku ji ya ce daga wurin aiki ya taho nan ba, na san kayan jikin shi ne kawai ya taho da su, in ya tsaya ina zai samu wanda zai canza?" Duk kallonta suka yi irin na mamakin jin abun da ta ce, Fahad dai idonsa na ƙasa, a hankali ya ɗan yamutsa fuska jin maganarta, ba yau ne ta fara masa irin wannan kora da halin ba, shi ya sa bai son zuwa gidan ko da ya shigo Abuja bai wuce ya zo su gaisa ba, koda kwana zai yi in ya zo gidan daddy ya ce masa ya tsaya ya kwana wani lokacin sai ya ce mashi a ranar zai koma ko kuma ya ce sun zo wani taro ne an kama masu wurin da za su kwana, kusan in har ya zo gidan ya kwana to Deen na nan ne,
"Mom kaya ai ba problem bane, akwai clothing stores available da za a siya nan take ma a saka." Leemah ta faɗa tana watsa hannuwa, hannu Deen ya kai ya shafi sumarsa yana kallon Fahad da har lokacin kansa yake sadde ƙasa, ya ce masa ya ma kira wurin aikin ya ɗauki excuse anan zai kwana dama shima zai je Funtua ko goben sai su tafi tare, wani kallo mom din shi ta yi masa ba ta dai ce komai a.
"Bro Deen yanzu sai mu je a siya kayan da zai saka na dinner É—in ko?" A É—okance Leemah ta faÉ—a, kai Deen ya girgiza ya ce mata ba sai sun je sun siyo ba akwai kaya da ya siyo mashi daga can, daÉ—i ne ya kamata ta shiga sakin murmushi.