← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 197

Sashe 126

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

London.

Galleliyar baƙar mota ce dake ta sheƙi ta ƙaraso bakin gate ɗin, nan take gate ɗin ya buɗe da kan shi kasantuwar automatic gate ne, cikin katafaren gidan motan ta kutsa kai. Katangar gidan bata rufe gidan gaba ɗaya ba, bangon bashi da tsawo ya kasance rabin katanga da aka yi da farin dutse mai sheƙi, daga sama kuma aka cike ta da ƙarafan alfarma masu launin baƙi da golden, waɗanda ke ƙyalli idan rana ta hasko su. Babban gate ɗin shiga gidan ya kasance na ƙarafa mai kyan gani, wanda aka ƙera jikin shi da salo na zamani.

Kana shiga cikin harabar gidan iska zata busu maka ƙamshin furanni da aka k
Ƙawata wurin da su cikin tsari mai matuƙar ƙayatarwa, hanyar da zata kai ka wurin harabar motoci ta kasance mai fadi, an yi ta da fararen duwatsu masu tsabta. A gefen dama akwai ƙaramin tsari na shuke-shuken ƙananun bishiyoyi da aka tsara cikin salo, yayin da gefen hagu kuma aka sa fitilu masu kyan gani. Ƙasan gidan gabaɗaya yana sakin sheki, an yi shi da farin dutse da gilashi, wanda yake ɗaukar hasken rana ya maida shi kamar wani ginin sarauta. Duk wanda ya tsaya a gaban ƙofar gidan ba sai an ce masa mai gidan attajiri bane don ginin da kansa ya nuna alfarma da darajar dake cikinsa. Kaitsaye gaban ginin gidan motar ta nufa ba parking space ba, tana tsayawa ƙofar 6angaren driver ta buɗe, wani gajeran baturen mutum ne ya fito jikinsa sanye da suit, da sauri ya zagayo ɗayan 6angaren motan, yana kokarin kai hannu ya buɗe ƙofar baya aka buɗe ƙofar daga ciki, fitowa ya yi jikinsa sanye da grey ɗin tom ford suit, ƙafafunsa na sanye cikin dakakkun rufaffun takalma, a fuskarsa ya rufe idanunsa da baƙin designer glasses, sosai ƙwarjininsa ya bayyana, kayan sun matuƙar amsar jikinsa kasancewarsa mutum mai matsakaicin tsawo da kuma ɗan kaurin jiki wanda da gani yana motsa jiki, ta cikin gilashin fuskarsa ya kalli mutumin da ya yi niyyar buɗe masa kofar, da ɗan murmushi ya furta, "Thank you, James." Mutumin ya ɗan rankwafar da kai, kai tsaye Maleek ya nufi gidan, a nutse ya fara tattaka steps ɗin da za su sada ka da ƙofar shiga, bayan ya isa gaban kofar wadda take mai matuƙar kyau da tsari, ɗan tsayawa ya yi yana fuskantar ta, after few seconds ta yi wata ƴar ƙara tare da sakin ɗan jan haske ta wani wuri mai kaman na'ura, ƙofar na ɗauke ne da na'urar tsaro mai tantance fuska (Facial recognition security system). Cikin falon gidan ya shigo wanda yake tsit ba kowa a ciki sai na'urori dake aiki, kuma yana shigowa fitilun cikin falon suka kawo haske wanda a da ba wadataccen haske a falon, hanyar da zata kai shi 6angarensa da ke a nan ƙasa ya nufa, wata gajerar baturiyar mata ce ta fito ta wani 6angare ta shigo cikin falon, tana ganin Maleek ta fara sakin murmushi tare da nufar sa, bayan ta iso daga ɗan gaban sa ya dakata, cikin fara'a da girmamawa ta ce, "Oh, sir welcome back...." Maleek ya jinjina mata kai tare da furta, "Thank you mrs. Helen." Still da fara'a a fuskarta ta ci gaba da cewa, "....The security system triggered an alert, i was in the kitchen so i came out to check." Ya yi ɗan faffaɗan murmushi ya ce mata,"Thank you mrs Helen. I appreciate your attentiveness." Ta jinjina kai tana murmushi, tambayarta ya yi akwai wani matsala ta ce masa a'a, daga haka ya wuce, ita kuma ta juya zata koma kitchen, taku biyu zuwa ukku ya yi ya dakata tare da kai idanunsa kan Helen da har ta fara tafiya ya ce, "Has my love returned home?" Yana tambayar ko Sapna ta dawo, Helen da ta dakata ta bashi amsa da, "No Sir, but Basma is back." Maimaita sunan Basma da ta ce mashi ta dawo ya yi kafin ya ce ok daga haka ya ci gaba da tafiya, ya ɗan yi mamakin jin Basma ɗin ta dawo, kasantuwar ranar asabar ne da kanshi ya ajiye ta a makarantar islamiyya, da yake duk weekend baya daɗewa a wurin aiki, da safe idan zai tafi yake tafiya da ita ya yi dropping nata, ƙarfe biyu ake tashin su shima kuma bai wuce lokacin sai ya je ya ɗauko ta su dawo gida, gaba ɗaya sauran wunin ranar za su kasance a tare a can hawan bene na ƙarshe su huta tare da yin abubuwan nishaɗi, wani lokacin kuma bayan gidan suke tafiya inda ke da swimming pool da liluna, akwai madaidaicin garden mai ɗauke da shuke-shuke masu tsari, sannan kuma akwai sports field inda suke yin wasannin motsa jiki, itama Sapna duk asabar bata daɗewa a wurin aiki, wani lokacin idan ya ɗauko Basma suke biyawa su ɗauko ta, wani lokacin kuma idan ta gama aiki da wuri tana rigan su dawowa, ko kuma su riga ta dawowa idan bata gama aikinta ba ranar lahadi kuwa gaba ɗaya shi da Sapna ɗin basu zuwa wurin aiki sai in abu na gaggawa ne ya taso da ke buƙatar dole su je, sanin cewa dama wani lokacin Basmar tana dawowa kafin lokacin tashin su daga islamiyya ta ce ko bata jin daɗi ko kuma wani uzurin, hakan ya sa shi yin tunanin yanzu ɗin ma wataƙila wani uzurin ne ya sa ta dawo. Kai tsaye 6angarensa ya nufa ya shige, ya dauki wasu mintuna masu ɗan tsayi kafin ya fito hannuwansa riƙe da wasu files yana tafiya yana duba su, dama abun da ya zo ɗauka ke nan don lokacin tasowarsa bai yi ba duka lokacin ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna na safiya, yana shigowa cikin falon ya yi tunanin zuwa ya duba Basma don ya ga ko lafiya ta dawo, saboda bai son ya 6ata lokaci kaitsaye daga wayarsa ya buƙaci elevator ya sauko, shiga ya yi ya nufi saman benen da shi, bayan ya tsaya ya fito ya nufi 6angaren da ɗakin Basma yake, yana zuwa bakin ƙofar ya cire glasses ɗin fuskarsa tare da kama handle ɗin zai buɗe ya ji ƙofar a rufe take, har zai yi knocking sai kuma ya fasa ya ɗaura babban yatsansa jikin wani ɗan wuri dake a hannun ƙofar nan take ƙofar ta buɗe, a nutse ya saka kai cikin ɗakin fuskarsa da ɗan murmushi, lokaci guda Maleek ya tsaya cak kamar an latsa masa pause, nan take murmushin fuskarsa ya gushe tamkar bai wanzu ba, zaro idanu ya yi cike da razani nan take hannunsa ya fara yin rawa bai san lokacin da ya saki files da glasses ɗin hannunsa ba, da wata irin muryar kiɗimar abun da idanunsa ke gane masa ya furta, "BASMA....!" Kai tsaye kiran ya daki dodon kunnen su, a firgice suka saki juna, idanu a zazzare Basma take kallon dad ɗin nata ta fara ƙoƙarin lalubar rigarta, duvet ta janyo ta rufe jikinta yayin da ɗayar ta yi saurin sauka daga saman gadon ta 6oye a jikin ɗayan 6angaren gadon, hannun Maleek na kerma ya nuna Basma fuskarsa a hautsine yayin da furucin bakinsa suka ƙafe sam ya kasa furta kalma, itama Basmar kerma jikinta ke yi sosai tana ƙara dukunkune kanta da duvet ɗin, wane irin bala'e ne wannan idanuwansa suka gane masa! Wace irin musiba ce wannan ke faruwa under his roof! Cikin karewar murya da tashin hankali da ƙyar ya furta, " “Basma… me nake gani haka?!” Ya faɗa his voice breaking in disbelief, Basma ta kasa magana jikinta sai faman kakkarwa yake, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, wani irin tsoro da bata taɓa fuskanta ba na ratsa ta, tunanin cewa mahaifinta ya gan ta a wannan hali ya matuƙar gigita ta, da ƙyar Maleek ya iya jan ƙafafunsa ya juya ya fita daga cikin ɗakin ko bin takan takardun da suka faɗi bai yi ba....sai lokacin Basma ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ɗayar da ta 6oye a gefen gado tana jin alamun ya fita da sauri ta ɗago tana zare idanu, ba zata wuce sa'ar Basma ɗin ba, sai dai ita fara ce jajur kuma tana da gashi mai launin coffee brown, ta jawo kayanta dake a gefe guda saman gadon, cikin rawar jiki ta fara sakawa wanda riga da wando ne, ta ɗauko wata doguwar riga ta ɗaura a sama, jawo gyalen rigar ta yi ba tare da ta bi ta kan jakar ta ba ta nufi ƙofa da sauri kana ganinta ka san a firgice take, da yake a saman benen akwai hanyar da zata fitar da kai ta bayan gidan kuma ta san da ita don sun sha biyowa ta nan, nufar hanyar ta yi tana tafiya kamar zata kife ƙasa. Sosai Basma ke ta yin kuka, wllh ta yi dana sanin ganinta da mahaifinta ya yi a halin, bata san ya aka yi ba bata ankare da na'urar tsaron gidan da ke sanar da shigowar mutum ba, wadda dama da ita take amfani tana gane idan wani ya shigo gidan duk tana aikata hakan, shi ya sa asirinta bai ta6a tonuwa ba a wurin iyayenta sai yau da aka samu 6acin rana....

*✨A CIKIN RAYUWA✨*

ZAINAB BATURE

41
Chapter 126 · 0% Book details