← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 197

Sashe 54

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Salma ta gama karin kumallon, É—akinta ta koma ta sako hijab a saman kayan jikinta don tafiya islamiyyar hadda da suke yi asabar da lahadi kawai don ta yi sauka, "Innarmu zan tafi." Ta faÉ—a a daidai saitin É—akin innar tana gyara hijab É—inta, É—aga labule ta yi ta fito da murmushi ta ce mata, "To, sai kin dawo Allah Ya bada sa'a." Ta ce, "Amin, yauwa ba kin ce kina son waken suya ba? Ko ki kawo idan aka taso sai in wuce bakin tasha in siyo." ÆŠan jim innar ta yi kafin ta ce, "Je ki kawai a siyo ko gobe." Salma ta ce, "To wanda za a yi amfani yau fa?"

"Anya a yi awara yau, a dai bari ko gobe idan Allah Ya kaimu, kada shi mutumin da ya bamu kuɗi ya gan ki kina yi yayi tunanin mun cika son kuɗi." Ta ƙarasa tana ƴar dariya, itama Salma murmushi ne akan fuskarta ta ce, "To ai neman halak ne, kuma da ya bamu bai ce kada mu yi ba." Kai innarsu ta ɗaga alamar haka ne ta ce amman dai yau ta huta, sallama suka yi ta wuce innarsu ta bita da kallo tana murmushi, tana kai wa bakin ƙofa zata fita ta juya ta yi ma innar tasu bye bye tare da yi mata alamar kiss, murmushin jin daɗi ne akan fuskar innarsu ta furta, "Ina son Salmata. Allah Ya raya mani ke ya albarkaci rayuwarki." Amsa mata ta yi da, "Amin uwata da babu irinta.." Daga haka ta fuce innarsu ta ɗan girgiza kai tare da juyawa ta koma ɗaki.

Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana su Salma duk sun dawo daga islamiyya suna zaune a tsakar gida, baka jin muryar kowa sai ta Sagir da ta karaɗe wurin yana basu labarin yadda gasar su ta wakana, jikinsa ko riga babu sai wandon ƙwallo daga gefensa takalman kwallon da ya cire ne tare da safar ajiye, Salma dake ta murmushin jin daɗin jin Sagir ɗin na cikin waɗanda aka za6a yau, ta ce, "Amman Sagir har da shi kuka yi ƙwallon?" Tambayarta ya yi wa? ta ce shi jikan hajiya da ya haɗa gasar, Sagir ya ce, "Farko bai shiga ba kallo ya yi, sai bayan da aka gama za6ar waɗanda suka ci zagayen farko na gasar muka buga tare da shi...kuturun uba! Kai, wanda ya iya dai ya huta wllh, ai duk yadda muke ganin mu nan ƙwararru ne gurin ƙwallo a garin nan ƙur'an duk sai da muka raina kan mu...wai kun ga yadda mutumin yake sarrafa ball kuwa....!" Dakatawa ya yi ya ɗauki wayarsa dake a saman cinyarsa ya ɗan lallatsa, miƙo ma Salma ya yi ya ce ta kalla ga wani video nan da ya yi lokacin da suke bugawa tare da second team da suka ci, da sauri ta yunƙuro ta zo ta amsa ta koma saman tabarmar da take zaune tana kallo, innarsu da su Imrana ma duk suka sako kai suna kalla, Deen na sanye da jersey ɗin club din su na gida, sosai kayan suka amshi jikinsa sun ƙara fito masa da hasken fatarsa, murmushi ne akan fuskar Salma yayin da take kallon ƙwallon, a cikin ranta ta raya ke nan sake yin kitson ya yi don ta ganshi akan sa yanzu, kamar innarsu ta san mike a ran Salmar ta ce, "Wai kamar kitso nike gani a saman kansa ko?" Ta ɗago tana kallon Sagir, ya ce, "Eh kitso ne mana, ai dama yana yin kitso. Ni ma indai na shahara a ball sai na rinƙa yin kitso tun da ai ba haramun bane." Yana rufe baki Salma ta ɗago da alamun mamaki ta ce, "A wannan kan naka kamar goruba ne zaka rinƙa yin kitso." Daƙuwa ya yi mata ya ce, "Eh don ubanki, shegiya, dama ni ne da irin gashin ki, ni na rasa yadda aka yi ma komai naki ya fi namu kyau, koda kike mace ai yakamata muma mu ɗebo wasu abubuwan irin naki, amman daga ke sai Hamza duk aka tara ma abubuwa masu kyau." Ƙyalkyale masa da dariya Salma ta yi tare da yi masa gwalo, innarsu na murmushi ta ce, "Ai kuma ma sha Allah ba munana bane." Imrana ya kai hannu ya shafi sumarsa ya ce, "Amman dai gara gashi na da na yaya Sagir wllh..." Da sauri ya yi shiru ganin Sagir ɗin na niyyar rarumar takalmin ƙwallonsa ya san kuma yana iya jefo masa. Bayan salar Azhar Deen ya shigo cikin falon kamar ko yaushe jikinsa sanye da kayan shan iska don ba karamin jin zafin yanayin da ake ciki a Nigeria yake ba, a haka ma wai ruwa ya fara sauka kuma koda yaushe yana a cikin Ac, hajiya na zaune ta ɗaga kai ta kalle sa tana murmushi, wurin da take ya nufo yana zuwa ya miƙa mata hannu ya ce ta taso su je waje zata ga wani abu, kama hannun nasa ta yi ta miƙe tana faɗin Allah Ya sa ta ga alkhairi ya amsa da Amin yana murmushi, wajen part ɗin suka fito hajiya nata wurga ido ko zata ga wani baƙon abu, wurin parking space ya nufo da ita sai lokacin idanunta suka ga wani mutum dake a tsaye gefen wata rantsattsar mota fara sol sai uban sheƙi ta ke, kana gani ba sai an faɗa maka ba ka san sabuwa ce, mutumin na ganin Deen ya shiga washe baki, suna ƙarasowa ya ba mutumin hannu suka gaisa tare da yi masa ya hanya cikin washe baki mutumin ke amsawa, daga baya ya gaishe da hajiya har da ɗan russunawa ta amsa masa a mutunce, bin motar Deen ya yi da kallo mutumin ya ce ko a buɗe masa ya ƙara gani ya jinjina masa kai, buɗe cikin motan ya yi wanda ya matuƙar tsaruwa, nuna masa abubuwa mutumin ya shiga yi yana ƙara yi masa bayani, fuska a sake Deen ke ɗan jinjina kai alamar yana fahimtar bayanin, duk da dama ya riga ya san abubuwa da suka danganci motan, hajiya dai ta zuba ido itama tana kallon motar da sauraran mutumin, bayan ya gama yi ma Deen bayanin ya ce shi zai wuce, Deen ya ce masa ba zai tsaya ya huta ba ya ci abinci, cikin washe baki ya sanar da shi tare suka zo da wani abokin kasuwancin su shima ya kawo wata mota Zaria za su haɗu ne suna son su koma Abuja yau kada dare ya yi masu, bayan sun yi sallama mutumin ya tafi don dama tuni sun gama duk wani ciniki da boss ɗin su, shi ma kuma mutumin lokacin da ya kira Deen ya sanar da shi shine zai kawo masa mota ya tura masa kuɗi masu yawa.

"Ya kika ga motan, ya yi kyau?" Ya tambayi hajiya idonsa akan motar, kai ta shiga jinjinawa ta ce kyau ma ai ba a ma magana ita bata ma ta6a ganin irin motan ba, yana murmushi still holding her hand ya ce mata Avatr EV ce, wato motan da ake ma cajin lantarki, cike da al'ajabi hajiya ta ce, "Ikon Allah, yanzu nan sai a yi mata caji lafiya lau a yi amfani da ita?" Amsa ya bata da sosai, ta ɗan ta6e baki ta ce, "Bature dai ba zai bar mu mu huta da abubuwan al'ajabi ba, saura kuma jirgi mai caji shi ma na san ba wani babban aiki bane a wurin su." Yar dariya Deen ya yi ya ce mata ai wannan ba daga turawan bane daga yan China ne, hajiya ta ce ai dai duk taron su ne masu jan kunnuwa, zagayawa ya yi da ita ya buɗe mata ɗayan bangaren ta shiga da bismilla a bakinta, shima ya zagayo driver seat ya shiga yana ƙara kallon cikin motar, kai kawai hajiya ke jinjinawa tana ƙara yaba tsaruwar motan, screen ɗin dake a kusa da steering motan ya ɗan tatta6a kafin ya kalli hajiyan ta ciki ya ce mata, "Hi Sweety!" Hajiya ta gwalo ido cikin rashin fahimta, dariya ya saka ya yi mata playing vedion da mamaki ta ce wai camera ce a jikin screen ɗin ya ce mata eh, bayan ya rufo motan ya tashe ta suka fara zagayawa a cikin harabar gidan, su officer dake bakin gate duk sun leƙo suna ta kallon motan cikin washe baki sai kace bakunan nasu za su yage, tambayarta ya yi ko su fita su zaga gari ta ce a'a ya bari ta shirya tukun ko zuwa dare, bayan sun gama zagayawa ya dawo da su wurin parking, suna fitowa su officers suka ƙaraso cikin washe baki suka shiga yin santin motan tare da yin Allah Ya sa alkhairi, bayan su officer sun bar wurin hajiya ta ce, "Yanzu ita wannan motan amfani zaka yi da ita ne da ka siya?" Amsa ya bata da eh ya zo ba mota shi yasa ya siya ya yi amfani da ita a nan, hajiya na kallonsa ta ce, "Amman duk motocin dake a gidan nan Deeni? Idan ma na nan basu yi maka ba ai a can 6angaren iyayenka ba akwai wasu da bama amfani ake da su ba suna a lullu6e, in ma duk basu yi maka ba a can gidan ɗayan baban naku duk ba akwai motocin da zaka iya amfani da su ba kafin dai ka koma?" Murmushi ne akan fuskarsa ganin kallon da take masa mai kama da na tuhuma, ta ci gaba da cewa, "Ba laifi bane don mutum ya siya abun da ransa ke so, amman a rinƙa dubawa kada don an samu dama kuma a rinƙa yin almubazzaranci, tun da ai kana da motocin a Abuja da can ƙasar ma da kake, ai ina ganin su kala-kala a hotuna da video, har da wata mai suffa kamar ta wasan yara..." Dariya ya saka jin yadda ta fasalta motan ya kuma gane lamborghini ɗinsa take magana,
Chapter 54 · 0% Book details