← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 197

Sashe 4

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kafin ya ƙaraso ƙannansa Leemarh da Batool suka rugo wurin sa, ganin su ya sa shi ware masu hannu yana sakar masu murmushinsa mai saka mutum shagala wurin kallon sa, ɗan rankwafawa ya yi lokacin da suka ƙaraso jikinsa ya haɗe su tare da rungume su, ɗagowa ya yi suna kallon juna cikin washe masa baki suka furta, "You are welcome big bro." Amsa masu ya yi. "Thank you my lovely sisters, Leemarh and Batool, I'm so glad to see you guys." Suna ta washe baki suma suka ce sun ji daɗin ganin shi, Leemah wadda ke da ɗan tsawo ta kai hannu ta cire glasses ɗin da ya rufe idanunsa, tsarki ya tabbata ga ubangijin da ke tsara halitta, abun da na ayyana a raina ke nan a lokacin da na yi tozali da kyawawan manyan idanunsa da suke farare tas tamkar an ɗiga zaiba, ƙwayar cikin su baƙa ce wuluk har sheƙi take yi. Kama hannuwansu ya yi suka nufi wurin sauran mutanen. A cikin waɗanda suka zo tarbar shi akwai mahaifinsa Hon. Ibrahim Nuraddeen Ambasada sai mahaifiyarsa Hajiya Jameela da sauran ƙannansa, ministan wasanni na tsaye daga gaba cikin shigar baƙaƙen suit, tare da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF President), sai jami'an ƙwallon ƙafa, akwai wakilan wasu manyan kamfuna dake da alaƙa da harkar wasanni, sai manyan ƴan jarida da kuma shuwagabannin ƙungiyar matasa masu son ƙwallon ƙafa. Suna isowa wurin sauran mutanen ya saki hannuwan ƙannan nasa ya nufi mahaifinsa dake ta sakin murmushin farincikin ganin tauraron ɗan nasa, rungume juna suka yi dad din ya furta, "Welcome home, son." Ya yi maganar yana shafa bayan shi, ɗagowa Deen ya yi yana murmushi ya yi ma mahaifin nashi godiya tare da furta yana farin cikin ganin su, cike da jin daɗi Dad din ya furta suma sun yi matuƙar farin cikin ganin sa, maida idon shi ya yi kan mahaifiyarsa dake gefe ta yi shiga ta hamshaƙan manyan mata, doguwar rigar rantsattsiyar lace ce Abuja boubou a jikinta ta soke ɗaurin kallabi ya zauna daram akanta, saukar da gyalenta ya yi saman kafaɗa ya bayyana yalwataccen gashinta dake tufke ƙasan kanta, lokacin da idanuna suka sauka a kan fuskarta har saida na furta Ma sha Allah ganin irin tsantsar kyawun halittarta, mace ce irin giant ɗin nan wato tana da tsawo da jiki, gata fara ce jajur da ita sannan ta bangaren fuska abun ba a magana don irin matan nan ne masu manyan kyau wanda kana kallon su ko ka hango su tun daga nesa zaka shaida kyawun su, tana da manyan idanuwa da dogon hanci wanda daga ƙasa ya ɗan yi faɗi kaɗan, haka bakinta ma madaidaici ne da zanen labbanta suka fita raɗam, daga yanayin gashin girarta ma zaka fahimci tana da yalwatacciyar suma, ɗan ɗigon baƙin dake gareta a gefen gemunta ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tata, gaba ɗaya tun daga wuyanta, kunnuwanta zuwa hannuwanta duk gold ne. Hajiya Jameela ta kasance jinsin mutanen nan da ake kira da sadakar yalla, mahaifinsu Deen ya auro ta ne daga jahar Kano wanda asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane.

Wani kallo Mom É—in nasa ta yi mashi mai kama da harara, murmushi Deen ya sakar mata don ya fahimci dalilin kallon saboda ba ita ya fara runguma ba, nufar ta ya yi ya É—an rungumo ta tare da fadin, "I missed u sweetheart." Murmushi ta saki, ya É—ago suka haÉ—a ido shima da murmushi akan fuskar tasa ta ce,

"Welcome home, my pride." Godiya ya yi mata kafin ya ɗaura idanunshi akan ƙannansa Omar da Sultan, duk suka yi mashi sannu da zuwa cikin nuna farinciki duk ya rungume su, wurin ministan wasanni ya nufa, cikin washe baki ministan ya ba Deen hannu suka gaisa, cikin nutsattsiyar muryar shi mai taushi da daɗin sauraro ya ba ministan haƙuri kan rashin zuwa wurin su da wuri, da fara'a ministan wanda kirista ne ya furta, "Don't worry, first things first, and family is always first." Gaba ɗaya mutanen wurin suka yi murmushi tare da jinjina kai alamar gamsuwa da abun da minista ya faɗi, cikin nuna farin ciki NFF President ya ba Deen hannu tare da faɗin, "Nigeria is proud of you. Welcome home our champion." Da murmushi Deen ya yi masa godiya, haka duk ya gaggaisa da sauran mutanen suka yi masa barka da zuwa tare da nuna farin cikin ganinsa da yabon shi kan irin ƙoƙarin da yake yi a harkar ƙwallon ƙafa, ƴan jarida nata ɗaukar su hotuna da vedios. Sun ɗan dauki lokaci suna gaisawa da yin hotuna, kafin daga baya suka nufi hanyar barin tarmac ɗin wasu daga cikin security personnel ɗin Dad ɗin sa ne suka jawo jakunkunan kayansa da aka fito da su. Suna cikin tafiyar ne minista ke ƙara jinjina ma Deen Jr. kan irin ƙwazon shi a harkar ƙwallo da irin yadda yake saka ƙasa alfahari, yana maganar yana nuni da hannuwansa yayin da Deen ke ɗan murmushin jin daɗi.

Lokacin da suka iso arrivals hall nan ma wasu tarin masoyan shi ne da masu goyon bayan ƙungiyarsa da suka zo tarbarsa, nan hayaniyar masoya ta cika wurin, cike da farin ciki suka shiga ɗaga hannuwa cikin ɗaga murya suka shiga yin sowar farin cikin ganin shi tare da koɗa shi da kuma kungiyarsa ta ILFC, har da masu rera waƙokin club din su, wasu daga cikin mutanen na ruƙe da babbar banner mai ɗauke da hotonsa jikinsa sanye da kayan ƙungiyarsu ya ɗaura ƙafarsa guda a saman ƙwallo yayin da bakinsa ke a buɗe, daga yanayin yadda ya rankwafa a cikin hoton zaka fahimci yana cikin yin gudu a cikin filin wasa aka yi shi, wasu kuma suna ruƙe da placards gaba ɗaya an yi rubutun barka da zuwa tare da yabo da jinjina a gare shi, da kuma masu ruƙe da tutar tambarin kungiyarsu mai dauke da shield wato garkuwa mai launin fari da zinari, daga tsakiya akwai zaki mai riƙe da ƙwallo wanda ke nuni da jarumta da jagoranci, daga saman tambarin akwai ƙaramin kambu(crown) wanda ke nuni da haɗin kulob din da masarautar Biritaniya. A ƙasan tambarin an rubuta a Latin, "Virtus et Gloria" (wanda yake nufin ƙarfi da ƙwazanta) tutar sai shawagi ta ke a sama. Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hargowar masoyan Deen hakan ya jawo hankalin sauran mutane dake kai kawo a cikin arrivals ɗin duk hankulansu suka dawo kan fitaccen ɗan ƙwallon, tuni ƴan jarida sun zagaye shi wasu na mashi tambayoyi yayin da wasu ke ɗaukar hotunansa da video, ƙayataccen murmushi ne akan fuskar Deen yana ta ɗaga ma masoyan nashi hannu tare da yi masu godiya, cike da alfaharin ɗan nasu iyayensa da ƴan'uwansa ke ta sakin murmushin jin dadi ganin yadda mutane ke nuna haukan son shi, mutane sai tutsetseniya suke don ganin sun samu saka hannunsa wato autograph wasu kuma hoto suke son yi da shi, cikin sakin fuska yake saka ma masoyan nashi hannu a wurare daban daban, wasu a jikin rigunansu, wasu a jikin hanky wasu a jotter da sauran su, wasu 'Deen Jr.' yake rubuta masu yayin da wasu yake rubuta masu, 'Nuree Jr." Wasu ma, 'Ambassador Jr.' yake saka masu a autograph din. Da ƙyar jami'ai suka dakatar da mutanen suka wuce da shi.

Bayan sun fito daga cikin arrivals din kai tsaye wurin da motocin da suka zo da su suke suka nufa, anan ya yi bankwana da minista da sauran muƙarrabanshi bayan sun sanar da shi game da welcome dinner da aka shirya mashi da daddare a Transcorp Hilton Hotel. A jere motocin suka fita daga cikin airport ɗin kowa ya kama hanyar da zai nufa. A cikin wata dankareriyar baƙar jeep wadda gaba ɗaya glass din ta yake baƙi baka iya hango wanda ke cikin motar Deen da ƙannansa ke a ciki, yayin da iyayensu suke a motar dake biye da bayan ta su, gaba da bayan su motocin escort ne a jere suke tafiya.

_Bossladieswriter_

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

*_Dedication_*

_Ga duk wanda ya taɓa fuskantar zafi amma har yanzu yana murmushi,_
_To everyone who has loved deeply and lost painfully,_
ga duk wanda ya faÉ—i,_amma hakan bai hana sa tashi ba, this story is for you._

_A cikin rayuwa, kowace ƙaddara tana da dalili, every tear carries a hidden lesson, and even in the darkest nights, there’s always a light waiting to shine again._

_May this story remind you that nothing in life is wasted, duk abinda Allah Ya bari ya faru, has a meaning that only time can explain._

_Zainab Bature (Zeelaluh)_

Page 2

.....Lokacin da motocinsu suka ƙaraso bakin katafaren gate ɗin gidan Alhaji Ibrahim Nuraddeen dake a maitama, tun a bakin gate za ka fara sakin baki tsabar haɗuwar sa, bayan jami'an dake a bakin gate sun buɗe masu kai tsaye motocin suka kutsa ciki, al'ajabi ne ya kama ni ganin irin luxurious mansion ɗin tamkar ba a Nigeria ba, fassalta tsaruwar ginin gidan ba ƙaramin aiki bane saidai a ɗan kwatanta, gidan na da girma sosai sannan an tsara shi da shuke-shuken fulawoyi masu matuƙar kyau da tsari, ƙasan gidan kan shi ba irin wanda idanu suka saba gani ba ne, wani irin design aka yi ta yadda wani bangare na ƙasan wani irin abu mai salƙi ne tamkar in ka taka zai kada ka, wani bangaren ƙasan kuma an kawata shi da shukar korayen ciyayi gwanin burgewa, gidan ya ƙawatu matuƙa ta yadda duk wanda ya tsinci kan shi a gidan zai tabbatar da naira ta sha kashi a wurin ƙera gidan. Kai tsaye entryhall din gidan motocin suka nufa a tare suka faka, cikin escort ɗin wasu suka fito tare da nufar motocin da iyalan suke suka bubbuɗe masu ƙofofi, lokacin da Deen ya fito wani irin lumshe ido ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya furta, "Home, sweet home." Ƴar dariya duk suka yi Dad ɗin shi ya dafa kafaɗarsa ya ce ya yi missing ɗin gidan ne, buɗe kyawawan idanunsa ya yi akan Dad din nasa ya furta sosai ma,
Chapter 4 · 0% Book details