Sashe 136
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Tun da su Salma suka hau hanya lokaci bayan lokaci aunty Kubra ke kira tana yi masu ya hanya tare da tambayar sun zo ina, daga ji ta ƙagara su isa, lokacin da suka isa Kaduna suna shiga cikin motor park ta sake kira Salma ta sanar da ita ga su yanzu sun iso tasha, ta ce ok itama gata nan daidai zata shigo cikin park ɗin, Salma na fitowa daga mota lokacin motan aunty Kubra ta shigo ciki, murmushi ta shiga saki aunty Kubra da ta hango ta ta nufo in da take, bayan ta faka motan gefe ta buɗe ta fito, tana sanye da Abaya mai kyau ta naɗa gyalenta fuskarta ta saka glasses ta fito a wayayyarta, da sassarfa Salma ta nufe ta itama aunty Kubra ta nufo ta ta wara mata hannu, Salma ta faɗa jikinta tana dariyar farin cikin ganin auntynta, sosai aunty Kubra ta rungume Salma tana jin wani irin farin ciki a ranta, ɗago ta aunty Kubra ta yi ta cire glasses din fuskarta, cike da farin ciki ta furta, "Welcome babynah, I'm so glad to see you." cikin washe baki Salma ta ce, "Nima haka aunty Kubrana." Ƙara rungume ta aunty Kubra ta yi tare da ɗan lumshe ido, "Da alama ita kaɗai kike murnar gani." Sagir ya faɗa yana tsaye kusa da su, jin maganar shi ya sa aunty Kubra ta ɗago Salma daga jikinta ta kai idanunta kan Sagir da ya ɗan ɗaure fuska, dariya ta yi tare da kai hannu ta taba kafaɗarsa ta ce, "I'm sorry man Sagir nawa, ka san idan na ga babyna idanuwan nawa rufewa suke." Sagir ya ce, "To ai da ba a gayyaci mutum ba..." Dariya ta saka tare da ɗan bugun shoulder ɗinsa ta ce, "Wai har yanzu baka daina kishi da baby ba ke nan." Dan murmushi ya yi ya ce wani abun ba dole mutum ya yi kishin ba, ta gayyato shi ya kawo ta amman ta ba banza ajiyarsa kamar Salman ce kaɗai ta zo, dariya sosai aunty Kubra ke yi ta ce, "To tuba nike kada in ja a ce baza a ƙara kawo mini ita ba." Tambayar shi ta yi kayan su ya nuna mata su a gefe an fito da su, tare da ita suka ɗauki kayan suka saka a cikin boot din motar ta, a seat ɗin gaba aunty Kubra ta sa Salma ta zauna shima sai da Sagir ya yi mita, aunty Kubra tana dariya ta ce mashi ya yi haƙuri ya zauna a bayan shi da ma aka bar ma gaba ɗaya back seat ɗin yadda zai wataya, Salma dai dariya take ta yi ganin yadda Sagir ke ta nuna jin haushin abubuwan da aunty Kubra ke mata, bayan Sagir ya shiga baya aunty Kubra ta shiga driver seat ta ja suka bar cikin tashar.....
09013804524, 08169856268 for more info.
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
44
09013804524, 08169856268 for more info.
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
44