← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 197

Sashe 141

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ake wulaƙanta ta, ba don sanin ƴaƴa rahama ne ba wa zai yarda ya sha baƙar wahalan da ake sha wurin haihuwan..." Dakatawa ta yi tare da juya fuskarta tana kallon wuri daban, Salma nata kallonta tana jin tausayin ta a rai, can aunty ta sauke ƴar gajeruwar ajiyar zuciya ta ce, "Allah Ya sa kowace mace ta ci ribar haihuwa, ni dai na gode ma Allah don tuni na fara cin riban hakan..." Ta juyo ta kalli Salma tana murmushi, itama Salma murmushin ta yi don ta gane da ita take, hannu aunty ta kai ta kwanto da ita jikinta ta yi mata side hug, cikin sanyin murya ta ce, "Allah Ya ƙara ma rayuwar ki albarka baby, kullum addu'ata a gare ki Allah Ya baki miji wanda zai ƙaunace ki, ya kula da rayuwar ki ya ji tausayin ki." Salma ta yi saurin lumshe ido jin hawaye na niyyar taho mata, bata san wace irin ƙauna auntyn tata ke yi mata ba, ta damu da ita sosai wanda ko iyayenta iya damuwar da suke nuna mata ke nan, ɗan leƙen fuskarta aunty ta yi ta ce bata ce Amin ba, buɗe ido Salma ta yi tare da yin ɗan murmushi, aunty ta fahimci kunyar amsawa take, ta ce mata ta amsa ai addu'a ce aka yi da ta shafi rayuwar ta ba batun kunya, a hankali Salma ta ce, "Amin Ya Rabb, na gode da ƙaunar da kike mani aunty Kubra, ina roƙon Allah Ya biya maki dukkanin buƙatun ki na alkhairi." Aunty tana murmushi ta amsa mata da Amin tare da ɗan shafa fuskarta, "Kin sha shayin ne?" Salma ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta ce, "Zaki sha in haɗa mana?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, ɗago ta aunty ta yi ta ce tana zuwa, miƙewa ta yi ta nufi jakar ta ta bude ta ɗauki abu bayan ta rufe ta nufi toilet idanun Salma akanta, after some minutes aunty ta fito tana ɗaure da zani saman rigar aikinta ta yafo ɗan gyale a kanta, fuskarta da hannunta ɗauke da lemar ruwa, bayan ta zauna ta buɗe food carrier ta ciro flask ɗin ruwan zafi da cups ta fara haɗa masu tea. Washe gari da safe bayan aunty ta tashi daga aiki tare suka fito zuwa inda motarta take, nan suka haɗe da Dr Hisham shima zai tafi, dakatawa ya yi wurin su suka gaisa da aunty, ya kalli Salma suka haɗa ido, a hankali ta gaishe da shi ya amsa yana murmushi ya ce, "Baƙuwar mu kin daina kukan ko?" Ta ɗan ɗaga masa kai tare da sauke idanunta, ya ce haka yakamata ta yi masu addu'a Allah Ya basu lafiya, ta ɗaga masa kai ba tare da ta kalle sa ba, kallon aunty ya yi ya ce mata sai anjima ta amsa tare da yi mashi Allah huta gajiya, ya amsa yana nufar motarsa, Salma ta ɗago tana kallon navy blue motar da ya buɗe ya shiga mai kyau da ita, bayan aunty ta buɗe motarta suka shiga suma suka tafi. Sai da aunty ta biya da su wani babban wurin siyar da abinci da ta saba zuwa tana siyan abinci musamman idan ta taso daga aikin kwana, waina da miya da nama ta siya masu, ta tambayi Salma ko tana son wani abu a siya ta ce mata a'a wainar ma ya isa, bayan sun gama suka nufi gida. Ranar Asabar wuraren ƙarfe goma saura Leemarh ta gama shiryawa cikin wani haɗaɗɗan sky blue lace da ya matuƙar yi mata kyau, gaba ɗaya gyale da takalma da jaka kalar golden ta saka wanda shine adon leshin, ta yi kyau kamar a sace ta, bayan ta fito daga ɗakin da take zaune ita da Binafa, 6angaren momy ta nufa don ta yi mata sallamar tafiya Zaria da za su yi ita da Fahad, momy na zaune a falonta ta ɗaga ido tana amsa sallamar ta, ciki ta ƙaraso ta zauna akan kujera momy nata kallonta tana murmushi, gaishe da ita Leemarh ta yi momy ta amsa tare da cewa, "Daughter an gama shiryawa?" Ta ɗaga mata kai tana murmushi, momy ta sake cewa, "Ma sha Allah kin yi kyau sosai." Murmushinta ya ɗan faɗaɗa ta ce mata ta gode, tambayarta ta yi Fahad ɗin ya fito Leemarh ta ce a'a sai dai ta yi mashi magana, momy ta ce bari kawai ta kira shi, wayarta ta ɗauka ta fara kiran shi, bayan ya ɗaga ta kai kunne ta ce mashi idan ya gama ga Leemarh nan tana jiran sa, ba a jima ba ya shigo cikin falon, ya yi shigar aiki don zai shiga asibiti duk da ba ranar aiki ba ce yana da aikin da zai je yi shine za su tafi tare da Leemarh zai kai ta makarantar su Sadeeya kamar yadda Sadeeya ɗin ta roƙe sa ya kai mata ita, Binafa ma ta so a tafi da ita amman ranar suna zuwa tahfiz tuni ma har sun tafi, cikin falon ya ƙaraso sai faman sakin ƙamshi yake yi fuskarsa ta yi wani fresh, sumar kan shi da ta fuska sun sha gyara sai ƙyalli suke yi, idanun Leemarh na akan shi har ya ƙaraso cikin falon ya zauna kan kujera, cikin ladabi ya gaishe da momy ta amsa mashi, a hankali ya juya ya kalli Leemarh ta yi masa murmushi ta gaishe da shi ya amsa, bin juna suka yi da kallo kowannan su na ɗan murmushi Fahad ya ce mata ta yi kyau, kunya ce ta kama Leemarh saboda momy dake a wurin ta sauke idanunta, ita dai momy tuni ma ta janye idanunta daga kan su ta maida kan tv, miƙewa Fahad ya yi ya ce mata sai sun dawo itama Leemarh ta miƙe, momy ta kalle su ta ce bari ta ɗauko saƙon da za a kai ma Sadeeya, bayan ta fito da saƙon a cikin wata ƴar babbar leda Leemarh ta kai hannu zata amsa momy ta yi murmushi ta ce ta bar shi bari ta raka su, matsawa Leemarh ta yi saida ta bata ledan ta riƙe sannan suka tafi ta raka su har waje tana masu Allah Ya tsare hanya. A nutse Fahad ke driving gaba daya cikin motan ya karaɗe da daddaɗan ƙamshi haɗi da sanyin Ac, lokaci lokaci yake juyawa ya kalli Leemarh su haɗa ido tare da sakar ma juna sanyayyan murmushi, wasu lokutan ta cikin mirror yake satar kallonta ya yin da idanunta ke kallon hanya, ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, a yanzu ji yake ya shirya ma kowane irin ƙalubale zai fuskanta akanta don tuni son ta ya kanainaiye masa zuciya, komai game da ita ya yi masa ɗari bisa ɗari, kyawunta, tsabtarta, iya girkinta, iya kwalliyarta, sauƙin mu'amallarta, gashi ya fahimci ba ƙaramar kulawa zai samu a wurinta ba, don a yanzu ma da basu furta ma juna so ba ba ƙaramar tarairaya yake samu daga wurinta ba, da duk bai yi tunanin hakan daga gare ta ba ganin ta ba wata babba ba. Bayan sun iso Zaria Fahad ya ce su je su yi ma Sadeeya siyayya, wani mall ya kai su tare suka shiga da Leemarh, idan ka kalle su sai ka sake kallon su yadda suka yi kyau kana ganin su ka ga waɗanda hutu ya zauna masu, siyayya mai yawa suka yi, bayan sun fito har da fruit suma masu yawa ya siya sannan kai tsaye suka wuce Abu, a wuraren da hostel ɗin su Sadeeya yake ya faka motan ya kira ta a waya, ba a ɗauki lokaci ba sai gata ta nufo in da suke tare da wata friend ɗinta, cike da farin ciki ta ƙaraso wurin motar ta rungume Leemarh da ta fito tana faɗin, "Welcome my beautiful sis." bayan sun saki juna Leemarh ta gaishe da ita tare da ƙawarta da ta kafe Leemarh da ido sai kallonta take don Sadeeya ta sanar mata ko wacece Leemarh, Sadeeya ta leƙa ta ƙofa ta gaishe da Fahad ya yi mata ya karatu, tambayarta Khaleel ya yi ta ce ɗazun suka tafi Kaduna da wasu friends ɗinsa za su dubo mamar wani abokin su da bata lafiya amman anjima za su dawo, ƙawar Sadeeya itama ta ɗan duƙa ta ƙofa ta gaishe da Fahad ya amsa tare da yi mata ya karatu, "Amman ya Fahad nan zaka barta sai gobe ko?" Dan girgiza mata kai ya yi ya ce anjima da yamma zai zo ya ɗauke ta, a marairaice Sadeeya ta ce, "Tun da weekend ne ka bar mani ita sai ka dawo gobe ka dauke ta pls." Fahad ya ce to miye amfanin ta kwana a nan, idan ta wunin mata ai ya isa, dole Sadeeya ta haƙura amman ta ce masa to sai magrib zai dawo ɗaukar ta shi dai bai ce komai ba, nuna ma Sadeeya kayan dake a seat ɗin baya yai ya ce ta ɗauka, bayan ta fiddo su ta yi masa godiya, leƙawa Leemarh ta yi suka haɗa ido tana murmushi ta ce masa sai ya dawo, ya ɗan yi shiru yana kallonta cikin ido, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ko kina son ki kwana?" Saida ta ɗan saci kallon inda Sadeeya ta ke sannan ta juyo ta ɗan girgiza masa kai alamar a'a, murmushi ya yi don daga yadda ta yi ya fahimci saboda shine bata son kwana, slowly ya ce, "Ok, till I come back, take care." Ta ɗaga masa kai, Sadeeya da friend ɗinta suka ɗauki ledojin kayan, ta kama hannun Leemarh da ɗayan hannunta suka nufi hostel, ƙawar Sadeeya ta kasa janye idanunta akan Leemarh sai murmushi take mata, suna zuwa cikin hostel Ruƙayya ƙawar Sadeeya ta fara yayata ma ƴan hostel zuwan Leemarh da ko ita wacece, ai fa nan aka fara tururuwar zuwa ganin ƙanwar Deen Jr, mutane sai santin kyawun ta suke suna faɗin kamanninta da Deen, har daga wasu hostels ake ta zuwa ganin Leemarh anata yin hotuna da ita, sam an ƙi bari ma Sadeeya ta samu lokaci da ita su zauna su yi hira daga a ja ta nan sai a ja ta nan, ƙarshe da Sadeeya ta ga idan ta zuba ido ba za a bari ta samu lokaci da
Chapter 141 · 0% Book details