Sashe 196
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo cikin gidan, fuskarsa da alamun tashin hankali, innarsu da Salma har da Sageer duk suna zaune jugum a cikin baranda, har da Imrana da innarsu ta sa ya kwaso kayan tuyan awaran, har lokacin Salma kuka ta ke ta yi a hankali ta saka kanta a cikin ƙafafunta, ƙarasowa Auwalu ya yi ya tsaya daga gaban su ya ce, "Innarmu wai mi yake faruwa ne? Yanzu nan ake gaya mani wata mata ta zo ko kun yi faɗa da ita." Innarsu ta bi shi da kallo idanunta jiƙe da ƙwalla sun yi jajir, cikin hura hanci Sageer ya shiga faɗa masa abun da ya faru, Aliyu ne ya shigo cikin gidan da sauri ya nufo cikin barandan da yanayin tashin hankali ya ce, "Ga ƴan sanda nan wai sun zo tafiya da Sageer!" A tare gaba ɗaya suka kalle shi tare da miƙewa lokaci guda ban da Sageer, hankali a matuƙar tashe innarsu Salma ta furta, "Ƴan sanda..!" Aliyu ya ce mata eh har da mota suka so, ta saki salati da ƙarfi tare da fashewa da kuka, Salma da itama ta miƙe ta saki wani matsanancin kuka, haka Imrana da Hamza, Auwalu da ke kallon Aliyu ya ce, "To mi ya yi da za su kama shi?" Daidai nan suka ji an rafka uwar sallama daga waje ana faɗin Sageer ya fito idan ba haka ba za su shigo, Innarsu da duk ta gama kiɗimewa ta kalli Sageer tana faɗin bari ta kira baban su, Salma da itama duk ta gigice ta shiga yarfa hannu tana ci gaba da yin kuka, miƙewa Sageer ya yi yana cika ya ce ma innarsu bari ya je ai dai ba a isa a yi masa abun da Allah bai yi masa ba, Salma ta yi saurin riƙe masa hannu cikin kuka tana faɗin, "Don Allah Yaya Sageer kar ka je, tafiya fa za su yi da kai." Haka Imrana da Hamza ma suna kuka suna roƙon kada ya je, a hankali ya zame hannun Salma da ta so tsinka masa zuciya ya yi ɗan murmushin ƙarfin hali ya ce ta kwantar da hankalinta ba abun da zai faru da shi in sha Allah, daga haka ya nufi ƙofar fita Auwalu da Aliyu na biye da shi, gaba ɗaya su Salma suma suka rufa masu baya, yana fitowa ƴan sanda biyu dake tsaye a bakin zauren gidan suka tambayi shine Sageer ya ce eh, ɗaya ya ce, "Ok zamu tafi station da kai." Sageer da ya ɗaure fuska ya ce, "Akan mi, wani laifi na aikata?" Guda a cikin su wani ɗan baƙi tatirna ya ce, "Idan muka je can zaka ji laifin ka." Daga haka ya fara ƙokarin saka masa handcuff, da sauri Sageer ya janye hannuwansa yana masa wani kallo ya ce, "Sai ka ce dai wani criminal za a saka mani ankwa, kuma ni ban san laifin da na aikata ba ma." Ɗan sandan ya ɗaure fuska yana cewa ya tsaya ya saka masa, Sageer ya ce, "Gaskiya ni ba zaku saka mani ankwa ba ba tare da na san laifina ba, haka kawai salon mutane su fara zargin wani mummunan laifin na aikata, ko a ma yi tunanin kidnapper ne ni ko informer." Ɗan sandan ya bishi da wani kallo irin na ka ƙule mutum, Auwalu ya ce yakamata su faɗi masu laifin da ya aikata, ɗan sandan ya yi ƙwafa kafin ya ce ma Auwalu ai shi ya san laifin da ya yi ma matar ɗan majalissar tarayya kuma ita ta saka a zo a kama shi, haka suka tasa Sageer ba tare da ya yarda sun saka masa handcuff ɗin ba, wasu cikin makwabta har sun fiffito an fara tambayar mi ke faruwa aka kama Sageer, su innarsu duk sun yi tsaittsaye suna ta kuka, motar yan sandan na tafiya Salma ta zame ƙasa a bakin zauren tana rera wani sabon kuka, Auwalu ya hau mashin ɗin Aliyu ya ce su bi bayan su...zumbur Salma ta miƙe tare da rugawa cikin gida zata je ta kira Deen ta sanar masa abun da ke faruwa. Tun bayan da mom ta bar falon, hajiya ta yi zaune tana dogon tunani, ta san halin Jameela tana iya zuwa ta aikata abun da zai tada ma mutane hankali, lokacin Balaraba ta shigo cikin falon, har zata wuce kitchen sai kuma ta dawo ta tsaya daga gefen hajiya, ganin alamun kaman da magana a bakin ta hajiya ta tambaye ta ya aka yi, ta ce mata dama yanzu hajiya ta Abuja ta saka ta raka ta gidan su Salma, hajiya ta yi shiru tana kallon Balaraba jin abun da ta ce, can ta ce, "To mi ta je yi masu gida?" Balaraba ta ce itama bata sani ba don basu ƙarasa gidan ba ta ce ta dawo, daidai lokacin direban hajiya Sule ya shigo cikin falon duk suka ɗaga kai suna kallon shi har ya ƙaraso, da yanayin damuwa ya ce ma hajiya dama ya zo sanar mata ne ga hajiya can ta Abuja ta saka an kama Sageer yayan Salma, jin haka ya sa hajiya yin saurin miƙewa, nan da nan 6acin rai ya bayyana akan fuskarta ta ce ma Sule mi Sageer ɗin ya yi mata, wayar shi da ya ke riƙe da ya ɗago tare da miƙa ma hajiya, ta shiga kallon video ɗin da Ibrahim ya yi ma mom Jameela ba tare da sanin kowa ba, ta bayanta ya ɗauki video ɗin hakan ya sa ba a ganin fuskarta sai dai bayanta, daga lokacin da suka shiga gidan tare da Sageer videon ya fara, muryar mom Jameela ta fito raɗam lokacin da take ƙarasa yin maganganun da suka iske tana yi da kuma wanda Sageer ya mayar mata, shi Sageer ana hangen fuskar shi, amman Salma da innarsu basu fito ba don ta gefe ɗaya aka yi videon...6acin rai ne sosai ya bayyana akan fuskar hajiya bayan ta gama kalla, miƙa ma Sule wayan ta yi ba tare da ta ce komai ba ta juya ta nufi ɗakinta. Su Salma duk suna zaune a cikin baranda har da baban su da Auwalu, basu daɗe da dawowa daga police station ba sun je yin belin Sageer amman an hana su an ce sai mom ta bada izinin sakin shi, gaba ɗaya kana ganin su ka san suna a cikin tsananin tashin hankali, har lokacin innarsu da Salma da su Imrana basu daina matse ƙwalla ba, baban su ya sauke nannauyar ajiyar zuciya a karo na ba adadi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..." Ya furta yana jinjina kai, tun da aka faɗa mashi abun da ya faru ba abun da yake face salati, fuskarsa a hautsine ya furta, "Da ina nan abun duk da bai kai haka ba wllh, kuma shima Sageer ya yi kuskure, da bai saka mata baki ba tun da ya san waɗannan mutanen sun fi ƙarfin mu." Cikin raunanniyar murya innarsu ta ce itama bata so ya saka mata baki ba amman ya san Sageer da zuciyar tsiya, baban su ya yi jigum ya rasa mike masa daɗi, gashi koda Salma ta kira Deen ta kasa samun shi, har saƙo ta tura masa amman baya online, kiran Auwalu aka yi a waya ya ɗaga tare da kai ta kunne, da sauri ya cire ya shiga lallatsa ta don duba abun da aka sanar da shi, "Gashi har an samu wani ma ya yi videon abun da ya faru ya ɗaura a social media." Ya faɗa idanunsa akan videon, da sauri duk suka kalli Auwalu da ya yi maganar, da sauri baban su ya tambayi miye aka ɗaura Auwalu ya miƙa masa, bayan ya gama kalla cikin tashin hankali ya ƙara rafka salati yana faɗin, "To waye kuma ya yi video har ya yaɗa, hakan ai ba abun da zai yi face rura wutar wata matsalar kuma." Duk fuskokin su innarsu suka nuna rashin jin daɗi da ƙarin tashin hankali bayan sun kalla videon, miƙewa baban su ya yi yana faɗin bari ya je ya samu yayansa Sani su san ta yadda za su 6ullo ma al'amarin....hajiya na shiga ɗakinta ta kai hannu ta warto wayarta dake a gefen gado, dad ta shiga kira, dakatawa ta yi tana jiran shi ya biyo kiran bayan ta ji ya yanke, after few seconds sai gashi ya kira, bayan ta amsa gaisuwar da ya yi mata, cikin tsananin fushi ta ce, "Dama so nike in ji da sanin ka matarka ta zo ta aikata abun da ta aikata?" Dad ya yi saurin cewa, "Wallahi hajiya ban sani ba, nima yanzun nan ake sanar mani kuma na kalla video ɗin, sannan kwata kwata ma ba da izini na ta zo nan ba, ni sam ban san ma ta taho Funtua ba wllh, kawai ɗazun bayan na sanar mata game da saka ranan auren Deen kamar yadda kika saka in yi, shine ashe ta kamo hanya ta taho, don ni tun bayan da na yi mata maganan abun ya nemi zama 6acin rai na bar gidan, har yanzu maganar da na ke yi maku ban koma gidan ba wllh sai dai kawai labarin tana Funtua ya riske ni...don Allah ku yi haƙuri." Sosai hankalin dad ya tashi musamman yadda ya ji hajiya ta yi magana da alamun tsananin bacin rai, gashi ya san tana da hawan jini, a kausashe ta ce, "To ka yi gaggawar bata umarnin ta sa a sakar masu yaro, laifin mi ya yi mata? Duk abun da ma ya yi mata ba ita ta ja ma kanta ba, in ba son ta zubar mana da mutunci ta mayar da mu ƙananun mutane ba miye hakan da ta aikata! kuma itama ba don saboda ɗanta ta je yi masu rashin mutunci ba, wanda kuma basu ne suka kira ɗan nata ya je ya so yarinyar su ba, sai shi kuma ya yi shiru tana ci ma mahaifiyarsa mutunci, ai hakan da ya yi mata shine daidai kuma haka ake son ɗan halak, don haka ka sata ta sakar masu yaro idan ba haka ba wllh zan ɗauki mummunan matakin da bata ta6a zato ba a kanta, don ba zan ci gaba da zura mata ido tana zubar mana da mutunci ba." Haƙuri dad yake ta bata tare da tabbatar