← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 197

Sashe 146

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Amman yadda baki da ƴar'uwa mace da kina da wata kamar best friend haka zata zame maki kamar ƴar'uwa, kuma zaki ɗan rinƙa samu nishaɗi daga wurin ta, I mean zaku rinƙa yin hira ku je wurare tare tun da su ƴan'uwan naki mazan ba lalle ki yi haka da su ba." Salma ta ɗan girgiza masa kai sai kuma innocently ta ce, "Suma muna yin hiran da su sosai, kuma ma ina yin sana'a hakan na saka ni nishaɗin." Dr ya ɗan gyara tsayuwarsa yana ta kallonta bayan ya tambayi sana'ar da take yi ta bashi amsa, ba wai sana'ar tata ta bashi mamaki ba, kawai yadda ta ce masa a ƙofar gida take yi ne ya ɗan sa shi jin mamaki, ganin yadda take tubarkalla kyakkyawar budurwa mai natsuwa amman take iya zama a ƙofar gida tana tuyan awara, yana murmushi ya ce mata bata jin kunya ta zauna a waje ta yi awara ba ya fi a cikin gida ba, ta ce masa ai haka ta saba yi kuma ita bata jin wata kunya tun da neman halak ne, Dr ya jinjina kai, sai kuma ya ji ta sake cewa, "Har da fara ma nike saidawa." Fuskarsa a sake ya tambaye ta wani irin fara tana wasa da yatsunta ta ce masa irin wadda ake soyawa, ya ce, "Ke kike soyawan?" Ta ɗaga ido ta kalle sa tare da ɗaga masa kai alamar eh, ɗan jinjina kai ya yi yana murmushi ya ce, "Ni ban ta6a cin shi ba, ina dai gani mutane na ci, amman kuma tana da amfani sosai a jiki don tana ɗauke da sinadarai masu mahimmanci irin su protein, fat, fiber, iron zinc da sauran su." Salma ta kafe sa da ido don ita dai haka nan take cin fara don kwaɗayi ba tare da sanin tana da wani muhimmanci ba a jiki, "Amman tun da kina soya shi dole in koya ci. Yaushe za a bani?" Tana ɗan murmshi ta ce to ai ba a nan take soyawa ba saboda itama aunty bata ci, Dr ya ce, "Sai idan na je Funtua ke nan?" ta ce masa saboda faran zai zo Funtua, Dr ya ce, "No, tun da ina burin mallakar ki matsayin matata ai dole in je gaisuwa da roƙon iri wurin su yaya Sageer." Yadda ya canki sunan Sageer kamar ya san tsakanin su da Salman, ganin ta yi shiru ta sauke idanunta ya ce ko bata son ya je, batare da ta kalle shi ba a hankali ta ce a'a, daga haka kuma kamar ya rufe mata baki bata ƙara cewa komai ba, shi dai yana ta kallonta don komai nata burge shi yake, can ta ɗaga ido ta ce masa zata shiga gida ta fara jin bacci, Dr ya ce kodai ya cika ta da surutu shiyasa zata masa kora da hali, da sauri ta ce masa a'a da gaske bacci take ji, ya ce ok tare da tambayar yaushe take maraba da shi ya dawo, ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce duk sadda ya dawo, ya ce shike nan tare da ce mata ya gode, sai da safe ta yi masa har zata tafi ya dakatar da ita, back door ya buɗe ya fiddo wasu ƴan manyan ledoji guda biyu ya miƙa mata suka haɗa ido ya ce, "I got you this..." Ta ƙi amsa ta ce ya bar shi, "Sai in yi yaya da su tun da ke na kawo mawa? Kuma ai ba a maida kyauta balle kuma ta wanda ke son ka." Sauke idonta ta yi ta amsa ta ce masa ta gode, Ya ce, "Gud night, sleep tight." Ta ɗaga ido ta kalle shi idanunsu suka haɗu daga haka ta juya ya bita da kallo, Dr ya ji ta ƙara burge shi saboda halinta na ɗaukar rayuwa da sauƙi, musamman yadda bata ji komai ba ta faɗa masa sana'oin da take yi, nan take a zuciyarsa ya yanke in dai Allah Ya nufa suka yi aure kafin ta ci gaba da karatu, zai canza mata ra'ayi daga karatun nursing ta karanci medicine kuma ƙasar waje zai kaita kamar yadda shima ba a nan ya yi karatu ba, daga haka ya koma motarsa ya tafi.......

*✨A CIKIN RAYUWA✨*

ZAINAB BATURE

47
Chapter 146 · 0% Book details