Sashe 191
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan tafiyan aunty da kwana biyu, da daddare Salma na gaban wardrobe tana shiryawa da kayan bacci wayarta ta fara ringing, bayan ta gama saka hula akanta ta nufi bakin gado inda wayan ke ajiye, gabanta ne ya ɗan faɗi ta yi jimm tana kallon screen ɗin bayan ta ga wanda ke kiran ta wato Dr Hisham, sun ɗan kwana biyu basu yi magana da shi ba, duk da bata san ko aunty ta yi mashi wata magana ba, kamar ba zata ɗauka ba, can dai ta yi ƙarfin halin yin picking tare da zama a bakin gado, daga ɗaya 6angaren ta ji yayi mata sallama cikin nutsattsiyar muryar shi, a hankali ta amsa ta ji ya ce, "Salmah.." ta ce, "Na'am..ina yini, ya aiki." Ya amsa da Alhamdulillah, kafin ya tambayi yadda take da ƴan'uwanta ta ce mashi lafiya lau, shiru suka ɗan yi ta ji yay sigh ya ce, "Dama na kira ne in maki Allah Ya sa alkhairi, aunty ta sanar da ni an saka bikin ki." Salma ta ɗan runtse ido tare da ɗan cije baki, sai ta ji kamar ta yaudare shi, ta ji ya ce, "Salmah are you there?" Da ƙyar ta ce, "Uhm.." ya ce, "Ya aka yi kika yi shiru, ko baki son Allah Sanya alkhairin nawa?" Da sauri ta ce a'a sai kuma murya na ɗan rawa ta ce, "Don Allah Ka yi haƙuri..." Tana jin ɗan sautin guntun murmushin da ya yi ya ce, "Kin yi mani wani abu ne?" Ta ɗan yi shiru sai ta ji kaman da biyu ya yi maganar, ta ce, "Da..ban aure ka ba." Wani murmushin ya ƙara yi calmly ya ce, "Kada ki damu, ai na san wani baya auren matar wani, kuma aunty Kubra ta faɗa mani dama kina tare da shi kina mashi aiki daga baya soyayya ya shiga tsakanin ku, ni I'm very happy for you da irin mijin da zaki aura, duk da I won't hide it from you...na matuƙar son na mallake ki matsayin mata, amman na ɗauki ƙaddara, Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi, yanzu kin zama kamar sister ɗina ta jini, in sha Allahu da mu za a yi bikin idan Allah Ya kaimu." Lokaci guda Salma ta ji hawaye sun ciko idonta, ita kanta ta san Dr Hisham na son ta sosai, amman ta rasa yadda aka yi ta kasa bashi damar auren ta, duk da daga baya har cikin ranta ta yanke zata aure shi ko don ganin aunty Kubra na son ta da shi, to kuma sai ga yadda abu ya zo ya kasance tsakanin ta da Deen, wataƙila dama shi ne Allah Ya ƙaddaro zai zama mijin ki shiyasa ma har kika kasa bashi damar auren naki, wata zuciyar ce ta raya mata hakan, Dr Hisham ne ya ƙara kiran sunanta ta amsa, jin yanayin muryarta ya ce, "Kada ki da mu kin ji." Ta ɗan ɗaga kai ta ce, "To...nagode." Ya amsa da, "Yauwa, bari in bar ki ki yi bacci, ki gaishe mani da angon naki and everyone at home, gud nyt." Daga haka ya kashe wayar, Salma ta bi screen ɗin da kallo, duk sai ta ji ba daɗi, jiki a sanyaye ta kai kwance tare da lumshe ido. Ranar Friday lokacin sati guda da saka auren Salma, bayan sallan juma'a suna zaune a cikin baranda dukkan su suna cin abinci har da baban su, bayan Salma ta gama ta kalli innarsu ta ce, "Wai inna an daina yin awara ne." Innar su ta ɗan yi murmushi ta ce, "Muna yi, wai na ga an saka biki ma ci gaba da yi kuwa." Salma ta ɗan tura baki tana murmushi kafin ta ce, "To mi zai sa a daina innarmu." Sageer da ya tura abinci ya ce, "Kawai sai a ga ana wata awara bacin an san wanda zaki aura." Salma ta juya ta yi mashi wani kallo ta ce, "To abun kunya ne yin awaran, kuma ba sana'a bace, sannan ai dama kowa ya san sana'armu ce ko." Kallon innarsu ta yi ta ce, "Don Allah Innarmu a ci gaba da yi, kar ki biye ma Sageer, tun da ai dai neman halak ne." Sageer ya sake cewa, "To in ma sana'a ce ba a iya canza wata, salon dai ja ma mutane surutu." Salma na mashi wani kallo ta ce to ita sana'ar awaran mi ta yi, kuma dai ai duk sana'a sana'a ce, kallon baban su dake ta sauraran su yana murmushi ta yi ta ce, "Don Allah babanmu dan an yi awara abun kunya ne, ba sana'a bace?" Yar dariya ya yi ya ce, "Haka ne mamana, sana'a sana'a ce, kuma ta fi yin roƙo ko maula, kawai shi abun da na fahimci yake nufi shine saboda wanda zaki aura shiyasa yake ganin kamar abun kunya ne idan aka ci gaba da yi, to sai dai kuma ai ba kowa ya san da an saka bikin ba, kuma dalilin hakan ba a ce a daina yin sana'a ba tun da ba kan shi zamu maida ɗawainiyar mu ba." Salma ta gyaɗa akai alamar ato, "Dama ai na san goyo mata baya zaka yi, amman dai ci gaba da yin wata awara ja ma kai ƙasƙanci ne." Yana rufe baki Auwalu ya ce, "Ita awaran ba ita ce ku san ta yi sanadiyyar haɗuwar ta da shi ba, kuma ai an san da ana yin sana'ar awaran amman hakan bai sa an ƙi amincewa ya aure ta ba." Salma ta yi ma Sageer gwalo, ta juya cikin marairaicewa tana ce ma innarsu don Allah su ci gaba da yin sana'ar su kar ta biye ma Sageer shi dama ɗan ƙarya ne, ya kai hannu zai ɗauki takalmi babansu ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar ce mashi bai ji gargaɗin da aka yi mashi ba akan bugunta ko, Sageer ɗin ya mike yana faɗin kowa zata aura hakan ba zai hana shi hora ta ba idan ta yi mashi iskanci, ƙarshe innarsu ta amince kan zata ci gaba da yin awaran, ta ce ma Salma amma ba ita ce zata rinƙa yi ba sai dai Imrana da Hamza su ci gaba da yi. Tun bayan tsaida lokacin auren Deen dad ke tunanin ta yadda zai sanar da mom Jameela, da shi ya yanke ba zai sanar mata ba har sai bikin ya zo, amman hajiya ta ce masa ya sanar mata don tana da hakkin ta sani matsayinta na mahaifiyarsa, a cewar hajiya gara ta sani yanzu akan sai lokacin ya zo, hakan zai fi yi mata zafi ta ga an yi mata ba daidai ba, amman idan ta sani yanzu sai ya yi ƙoƙarin yadda zai shawo kanta ta amince. Ranar asabar lokacin sati guda da kwana ɗaya da saka bikin, wurin ukkun rana lokacin dad na gida ya nufi part ɗin mom Jameela, tana hakimce a saman kujera a falonta hannunta riƙe da waya, kallo ɗaya ta yi ma dad ta maida idonta akan wayan, a kujeran kusa da ita ya zauna, fuskarsa da murmushi ya ce, "My queen, hutawa ake.." shiru kaman bazata tanka shi ba, can ta ɗago manyan idanunta ta kalle shi tare da ɗage masa gira, yana murmushi ya ce ya yi kyau, shiru na ɗan lokaci kafin ya ce mata dama yana son za su yi magana ne, nan ma sai da ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta kalle shi a taƙaice ta ce, "I'm all ears." Dad ya gyara zama tare da ɗan yin shiru kamar mai tattaro ƙwarin gwiwar yi mata magana, daga yanayin shi ta fahimci kaman abun da zai faɗa yana da nauyi, hakan ya sa ta maido hankalinta gaba ɗaya kansa ta kafe sa da idanunta masu kaman na macijiya, a nutse ya fara magana, "Dama ina son sanar dake ne cewa....an saka ranar auren Deen." Dumm mom ta ji kanta ya yi, ta bishi da kallo with shock and confusion, yamutsa fuska ta yi, "Wani Deen ke nan?" Ta tambaya, dad ya ɗan gyara zama don bai hango zata kar6i abun ta sauƙi ba, "Muna da wani Deen ne bayan ɗan mu?" Mom ta wani kallan buɗa ido tare ɗan karkata kai alamar mamaki ya kashe mutum, "Deen ɗana ne aka saka ranar auren sa ba tare da sani na ba?" Dad ya ce, "Amman ai kin san da maganar yana son yarinyar da aure ko." Ta wani kalan juya kai, kallon shi ta yi a zafafe ta ce, "Wllh wasa ne, ba wanda ya isa ya nuna mani iko da ɗan dana haifa, raina ni ma aka yi da har wai za a saka masa rana ba tare da sani na ba, to wllh ƙarya ne....ba wani isasshe da ya isa ya tsaya mashi ya auri yarinyar nan matuƙar ni ce mahaifiyarsa." Ta ƙare maganar tare da buga hannun kujera da ƙarfi, dad ya yamutsa fuska don ya fahimci inda maganar ta ta dosa, da ɗan amon 6acin rai ya ce, "Wai mi yake damun ki ne Jameela? Yaron nan ya nuna yana son yarinyar, kuma an yi duk wani bincike akanta an tabbatar tana da halin kirki, kuma suma iyayenta mutanan kirki ne, to akan minene zaki ƙi amince masa aurenta?" A fusace ta ce, "Akan bana son shi da yarinyar, saboda na riga na zaba masa mata, wllh muddin ina numfashi bashi da matar aure ban da Basma, kuma ita kaɗai ce matarsa a duniya don ita kaɗai ce na yarda tana son shi tsakani da Allah kuma bazata mallake mani ɗa ba, duk wata mace da zata so Deen ni na san ba tsakani da Allah bane, saboda arziƙi da ɗaukakar sa ne, don haka ban haifar ma kowace mace shi ba balle a cutar mani da shi ko a raba ni da shi." Dad ya yi gwale yana bin ta da ido, sai ya ji maganganun nata kamar izna ne a gare sa, sauke ƴar ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ke ta ya kike da tabbaci ita yarinyar ba tsakani da Allah take son shi ba? Jameela kada ki zama mai son kai saboda wani dalili naki mara hujja, idan ita Basma za6in ki ce, mi yasa shima ba zaki goya ma zabin shi baya