← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 197

Sashe 28

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sautin zazzaƙar muryar mace ne ya karaɗe cikin motar daga wayar Deen, irin muryar na'ura ne ke faɗin,

"Sweetheart is calling..."

Saida muryar ta sake maimaitawa sannan Deen ya buÉ—e idanunsa, É—agowa ya yi tare da gyara zaman shi ya kai idanunsa kan wayar tashi da ke ajiye gefen shi, lokacin da ya kai hannu ya É—auko ta muryar ta sake sanar da shi contact mai sunan sweetheart na kira, a nutse ya furta, "Tell sweetheart I'm not available, am out of reach." Yana gama faÉ—in haka ya É—aura wayar saman cinyar shi tare da mayar da kansa jikin headrest, daga sunan da aka sanar da shi ya san mom É—insa ce ke kira, kuma ko ya É—auka ya san 6acin rai ne shi yasa ya ce a sanar da ita haka,

_"Message sent: ' You're not available, you're out of reach."_

Muryar ta sake karaɗe cikin motar tana sanar da shi cewa ta tura saƙon abun da ya ce a faɗi ma sweetheart, shiru ya ɗan yadda suka yi da ita a daren jiya na sake dawo masa. Lokacin da saƙon da Deen ya ce a fadi mata ya riske ta na cewa baya available tamkar ta kurma ihu ta ji, sam ta kasa zama har lokacin sintiri take ta yi bata da burin da ya wuce Deen ya ɗauki wayar ta bashi umarnin ya juyo kada ya ƙarasa Funtua, sau wurin ukku tana kira duk saƙo ɗaya ake turo mata cewa he's out of reach, sanin cewa yana akan hanya ya sa bata kawo komai a ranta ba ta yarda da abun da ake faɗa mata, ranta ne ya bata ta gwada kiran Fahad tun da suna tare wataƙil shi ta same shi, hannunta har ƴar rawa yake wurin kokarin kiran Fahad, wanda ba zata iya tuna yaushe ne ƙarshe da ta yi waya da shi ba, akasi! Shima dai sanar mata ake da cewa baya available duk ta kira. Dama sanin zata iya kiran Fahad ya sa Deen ɗaukar wayar Fahad ɗin ya saka ta a flight mode shiyasa shima ta kasa samun shi. Ƙarshe jefa wayar ta yi saman gado tsabar takaici ta zauna a baki tana ta huci kamar zakanya. Lokacin da suka iso Kaduna Fahad ya yi mashi maganar bari su je wani eatery su yi breakfast, Deen ya ce mashi a can Zaria ba eatery mai kyau, Fahad ɗin ya amsa mashi da akwai har a cikin asibitinsu, Deen ya ce mashi ok lafiya lau shi baya jin wata yunwa sosai za su iya bari su ƙarasa in dai ba shi yana jin yunwa ba,

"Kai dai ka faɗi gaskiya idan kana jin yunwa, na san ƴan ƙwallo cin abinci gare ku sosai." Fahad ya faɗa tare da ɗan murmushi idanunsa akan hanya yayin da suke tafiya cikin garin Kaduna, ɗan murmushi Deen ya yi jin abun da ya faɗa, kuma gaskiya ne shi kan shi baya wasa da abinci, ce mashi ya yi lafiya lau zai iya kaiwa Zaria ai still safiya ne, suka ci gaba da tafiya......

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_By Zainab Bature_

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 10

Alhamdulillah sun iso Zaria lafiya. Kaitsaye ABUTH dake Shika suka nufa, inda anan Fahad ke aiki matsayin Specialist a Family Medicine, bayan sun isa cikin asibitin, General Outpatient Department (GOPD) suka nufa, Fahad ya parker motan a inda aka tanada don hakan, Deen ya ɗauki hularsa ya saka kafin ya fito, yadda gashin shi da ya faka ya ɗan fito daga baya ba ƙaramin kyau ya yi ba, Fahad da shima ya fito yana kallon sa da dan murmushi ya yi masa sannu da gajiyan hanya, shima murmushin ya mayar masa ba tare da ya ce komai ba suka nufi shiga wurin, nan fa Deen ya zama abun kallo a wurin mutanen da ke kai kawo a arean, duk da ba a gane ko waye saboda hular shi ta ɗan yi curved daga gaba kuma ya ɗan sauke fuskarsa, idan ba ya ɗaga kai ba ba a ganin fuskar tashi sosai, duk in da suka wuce sai sun bar ƙamshin jikinsu sai faman kallon su ake, hatta mutane masu aji kallon su suke, suna shiga block ɗin suka haɗu da wani likita ya yi shigar light blue ɗin dress shirt da dogon baƙin wando sai nicktie, a wuyansa ya rataya stethoscope, gaisawa suka yi da Fahad cikin harshen turanci, dama bayerabe ne sunan shi Dr. Hakeem kamar yadda Fahad ɗin ya kira shi da suna gaisawa, yana ɗaura idanunsa akan Deen za su gaisa ya gane shi, da alamun ɗan mamaki ya kalli Fahad da har za su wuce ya ce, "This man looks like your footballer brother?" (Wannan mutumin kaman ɗan uwanka ɗan ƙwallon ƙafa?"

"Yes." Fahad ya amsa mashi fuska a sake.

"Ahhh! Nice to meet you. I am a huge fan of yours and support your club, I love your playing style." Dr Hakeem ɗin ya faɗa ya ɗan kama bakin shi dake a washe cike da farin cikin ganin Deen, da ɗan murmushi Deen ya yi mashi godiya ya nuna shima ya ji daɗin haɗuwa da shi, yadda Dr. Hakeem ɗin yake magana da yake yana da budaɗɗiyar murya hakan ya jawo hankalin wasu dake wurin da basu lura da shigowar su Deen ɗin ba, kan ka ce mi, ai Dr. Hakeem har ya fara shelar zuwan Deen, gaba ɗaya hankulan mutanen wurin ma'aikata da wanda suka zo ganin likita ya dawo kan su, nan fa aka shiga zuwa ana gaisawa da shi kowa yana nuna farin cikin ganinsa tare da yabon shi, nan fa wurin ya cika da ma'aikata manya da ƙananu har da mata, daga bangarori daban daban na asibitin ake ta zuwa ganin Deen, mutane sai yin hotuna suke da shi, Fahad dai na tsaye gefe yana murmushin jin dadin yadda ake ta nuna haukan son ɗan'uwan nasa, ana haka sai ga Medical Director (MD) na asibitin, babban mutum ne ya ɗan manyanta kuma yana son kwallon ƙafa, sannan yana goyon bayan kungiyarsu Deen, yana kuma bala'en yin Deen sosai, yana shigowa wurin aka shiga bashi girma ana gaida shi, cike da zolaya yake ce ma mutane shi bata so yake ba su matsa ya ga tauraron shi, duk mutane suka yi dariya, yana zuwa wurin Deen ya jawo shi jikin shi tare da rungume shi, bayan ya ɗago shi cike da farin ciki yake faɗi mashi yadda yake son wasan shi da kuma kungiyarsu, sosai ya shiga yabon Deen da ke ta sakin murmushi, hotuna ya saka aka shiga yi masu da wayarsa, bayan an gama janye Deen ɗin ya yi ya ce duk mai son ganin shi ya zo office ɗin shi, tafiyar su taba Fahad damar fara yin abubuwan da ke gaban shi, workstation ya nufa don shirya fara duba marasa lafiya. Bayan zuwan su office din MD a can ya sa aka kawo ma Deen lafiyayyun abincin breakfast suka ci a tare dama MD din yana cikin cin abinci aka sanar da shi game da zuwan Deen ya tashi ba tare da ya ƙarasa.

Fahad bai daɗe sosai ba yana duba marasa lafiya a consultation room ya tashi, dama bashi kaɗai bane akwai wasu likitocin a sauran ɗakunan da suke duba wasu marasa lafiyan, office ɗin MD ya wuce wurin Deen, a can shima ya yi breakfast duk da rana ta riga ta yi, saida suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi kafin suka hawo hanya zuwa Funtua. Wuraren ƙarfe biyu saura suka iso garin Funtua, lokacin Deen ne ke yin driving ɗin, tun bayan da za su baro Zaria ya amsa har Fahad na ce mashi zai iya driving mai tsawo kuwa a titin Nigeria, yana murmushi ya ce mashi lafiya lau zai iya, ga shi har Allah Ya kawo su lafiya.
Chapter 28 · 0% Book details