← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 197

Sashe 166

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

"To in ba mafarkin ba baby taya kawai zaki ce mani ya ce yana son ki, bacin tare dake nan muka kalli wasan su da daddare. Sannan mutumin da yake cikin wannan hidiman yaushe har ya samu wani lokacin da zai kira ki ya ce yana son ki, sai dai idan wasan kakan da kike mani wani lokacin ne ya motsa zaki mani yanzu." Ta kai maganar tare da kai chips baki, Salma ta ce, "Allah aunty da gaske nike, bari mu gama in ɗauko wayata in nuna maki kiran da ya yi mani." Aunty dai ɗan murmushi kawai ta yi tana ci gaba da cin abincinta, a ganinta taya hakan zai faru tsakanin jiya da daddare zuwa yanzu da safe ganin halin da Deen ɗin yake ciki. Bayan sun gama yin breakfast Salma ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke, lokacin da ta fito aunty na zaune a saman kujera ta bita da kallo, nufar hanyar ɗaki Salma ta yi, bayan ta fito tana riƙe da wayarta ta dawo wurin aunty ta zauna a gefenta, chat ɗinta da Deen ta shiga tana nuna ma aunty da kuma lokacin da suka yi magana, sannan ta je wurin whatsApp calls ɗinta ta nuna ma aunty contact ɗin Deen da ke a sama, shiga cikin kiran ta yi tana nuna mata lokacin da suka ɗauka suna yin video call, aunty data fara yarda da maganar Salma ta ɗan buɗa ido ta ce, "To da kuna yin video call ɗin sai kawai ya ce yana son ki?" Tiryan-tiryan Salma ta shiga bata labarin yadda komai ya faru, aunty ta ƙara waro ido sai kuma ta saki faffaɗan murmushi ta ce, "Babbar magana!" ta hau jinjina kai mamaki ya cika ta, after a while tana kallon Salma ta ce, "To yanzu idan ya fito zai aure ki, auren zaki yi ke nan?" Salma ta ɗan sunnar da kai sai kuma a hankali ta ɗaga mata kai alamar eh, aunty tana dariya ta ce, "To kuma ya zamu yi da Dr Hisham dake jiran lokacin da za a bashi dama?" Salma ta ɗan tura baki ta ce ita ai dama har yanzu bata ce mashi tana son shi ba ko yi mashi alƙawarin zata aure shi ba, aunty dake ta murmushi ta ce, "Da yake fa zuciya ta samu wanda take so ko?" Dariya Salma ta yi ta rufe fuska, "Yanzu dai ke nan kawai a dakata da shirin fara karatu, mu fara shirin kayan ɗaki. Amman baby anya baki ɗauko mana da girma ba?" Ta karasa tana jinjina kai, ita dai Salma ɗan murmushi kawai ta yi bata ce komai, ƴar ajiyar zuciya aunty ta yi ta ce, "Allah zai rufa asiri, kuma dai ai ya san wacece ke, ƙilan ma ki ga su ce basa buƙatar wasu kayan ɗaki, tun da na san da ƙyar idan kuka yi aure ku zauna a nan, koma dai ya aka yi ba abun da zai gagara in sha Allah." Bayan ta gama yin maganar ta yi shiru tana kallon wuri ɗaya, can ta saki wata dariyar bosawa ta ce, "Ko ba don komai ba na ji daɗin al'amarin nan saboda Sageer, gashi Allah Ya nuna masa ikonSa don uban sa...." Kallonta Salma ta yi tana dariya ta ce, "Aunty ashe baki manta ba." aunty ta ce, "Ta ya zan manta da wannan uban cika bakin da ya yi ma mutane, wani ba yadda za ai ya so ki, shi da yake ganin mata iri iri, wa ya mutu wa ya dawo, aikuwa zai ga ƙaryar iskancin sa wllh." Dariya duk suka yi, a sanyaye Salma ta ce, "Yanzu to aunty ya za a yi da Dr ɗin?" abun ya tsaya mata ne a rai tun ɗazun da aunty ta kawo maganarsa, "Ki bari na san ta yadda zan 6ullo ma al'amarin in sha Allah. In da na ji daɗin abun da ya kasance dama kina tare da Deen ɗin kina masa aiki ba yanzu daga baya kuka haɗu ba...zan dai san ta yadda zan fahimtar da shi a rabu lafiya, amman dai ba zan yi saurin yi mashi magana ba, mu jira mu ga abun ya kankama tsakanin ku tukun. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi." A hankali Salma ta ce, "Ameen." Aunty ta ɗan waro ido ta ce, "Anya baby, wato saboda muradin ran ki ne ko ƴar al kunya ma baza a nuna mani ba." Salma ta yi saurin rufe fuska, bayan ta cire hannunta ta sigar shagwa6a ta ce, "To aunty bake kika ce in an yi addu'ar da ta shafi rayuwata in daina jin kunya in rinƙa amsawa ba." Aunty dake kallon ta da murmushi ta ɗan ta6e baki, shiru suka yi kowa da abun da ke masa yawo a rai, aunty gani take kamar Deen ya fi ƙarfin Salma, amman da ta tuna cewa a wurin Allah komai mai yuwuwa ne sai ta ji ƙwarin gwiwa. Bayan kwana biyu da gama gasar, ranar asabar wuraren sha ɗayan safe tawagar su Deen suka iso Nigeria, wurin saukar jirgin ta cika da mutane, kama daga manyan masu muƙamai, zuwa manyan ƴan kasuwa, manyan celebrities da sauran su, har da shugaban ƙasa da ya riga ya dawo, red carpet reception aka shirya masu da ƴan mata masu sanye da kaya launin tutar ƙasa sun jera a bakin jirgin suna riƙe da flowers abun gwanin burgewa, lokacin da ƙofar jirgin ta buɗe tawagar ƴan ƙwallon suka fara fitowa wuyan su rataye da medals da aka basu yayin da Deen ke riƙe da kyautar da ya samu, kowa fuskarsa ta cika da annuri, nan take band dake gefe suka fara kaɗa ganguna ana busa taken Nigeria, shugaban ƙasa ne ya fara tarbar su cike da farin ciki akan fuskarsa, haka sauran mutanen dake a wurin duk suka tarbe su cikin farin ciki da kuma yabawa, kowa so yake ya rungumi Deen ko ya gaisa da shi, ana ta jinjina masa kan ƙwazon da ya yi, fuskar Deen ta cika da annuri yana ta murmushi, sai da aka ɗauki lokaci kafin ya ƙarasa wurin su mom ɗin sa da suma suna a wurin tun jiya su suka dawo, mom Jameela ta kasa rufe baki sai faffaɗan murmushin farin ciki take saki cike da alfahari, ƴan jarida da ke a wurin suna ta aikin ɗaukar rahoto da kuma yaɗa shi kai tsaye ga mutane, har da drone camera da ke ta shawagi a sama tana ɗaukar bidiyo. Bayan gama tarbarsu duk aka shiga motoci aka nufi barin wurin. A titin barin airport ɗin nan ma masoya da jama’a sun taru, wasu na ɗaga tambarin team ɗin wasu kuma tutocin Nigeria, wasu na riƙe da manyan hotunan su har da masu sanye da riguna da ke ɗauke da hotunan su, ƴan wasan na a cikin motoci masu buɗaɗɗen rufi suna ta gaisawa da mutane ta hanyar ɗaga masu hannuwa, daga airport victory parade aka yi wato aka ɗan zaga gari da yan wasan mutane na gaisawa da su tare da nuna murnar nasarar da suka yi, daga baya aka wuce Eagle Square inda aka shirya bikin tarba da kuma karramawa. Biki sosai aka yi da su kaɗe kaɗe da raye raye, sababbin wakokin da aka yi musamman saboda gasar sun karaɗe wurin, daga baya shugaban ƙasa ya yi masu karramawa ta musamman da babbar lambar yabo ta OON. Sosai suka samu manyan kyaututtuka daga gwamnati da manyan ƴan kasuwa da suka haɗa da motoci, gidaje, da manyan kuɗaɗe. A ranar sai dare Deen ya samu zuwa gidan bayan sun yi dinner tare da shugaban ƙasa da muƙarrabansa a fadarsa. familynsa sun cika da farin cikin nasarar da suka yi, musamman mom da kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ba kamar ganin irin kyaututtukan da ya samu masu tsoka. Bayan dawowar tasu wasu daga cikin gwamnoni suka gayyace su zuwa jahohin su suma suna son karrama su, ciki har da gwamnan Katsina. Lokacin da Deen ya je Katsina ya samu kyakkyawar tarba daga wurin gwamna tare da muƙarrabansa da kuma al'umma masoya ƙwallon ƙafa, a gidan gwamnati aka sauke shi, gwamna ya haɗa mashi dinner in da ya nuna farin sosai kan nasarar da suka yi da kuma ƙwazon da ya yi da ya kai su ga nasarar, ya bayyana yana alfahari da kasancewar Deen ɗan jaharsa, a nan ma Deen ya samu kyaututtuka daga manyan masu muƙamai da suka haɗa da motoci da kudaɗe, har da kyautar gida gwamna ya bashi a nan Katsina. Bayan Deen ya kai ziyarar gaisuwa masarautar Katsina, daga nan ya wuce masarautar Daura wadda take asalin masarautar hausa don kai gaisuwa da amsa saƙon gayyatar da sarkin Daura ya yi mashi, a nan sarkin ya bashi kyautar sarauta ta 'Zakin Wasannin Ƙasar Hausa,' Deen ya nuna jin daɗin sarautar sosai, nan aka saka lokacin da za a yi bikin naɗin shi...tuni hotuna da videon ziyara da kuma alkhairan da Deen ke ta samu duk suka karaɗe shafukan sada zumunta, mutane nata mashi laƙabi da mai sa'a, yayin da hakan ke ta ƙara zaburar da matasa masu burin zama kamar shi irin su Sageer. Daga Katsina Deen ya dawo Funtua, a satin ne suka tare a tamfatsetsen gidansu da Dad ya gina, babban ginin bene ne na zamani na gani na faɗa, wanda a duk garin babu kamar shi wurin kyau, ba don an san familyn su dad ɗin masu arziƙi bane da tabbas sai al'umma sun ce kuɗin su ya sata ya yi ginin, ƴan'uwa da abokan arziƙi anata zuwa ganin gida ana masu Allah Ya sanya alkhairi, su mom abun nema ya samu sai faman kauɗi take tana kallon mutane a ɗaɗɗage, musamman ganin mommyn su Fahad, dama sosai take kishi da ita, sai dai ita hajiya Ameena da yake ta yi gadon arziƙi da sarauta sam bata damuwa da duk abubuwanta, zumuncin da Allah Ya haɗa tsakanin su take yi da ita da zuciya ɗaya, duk abun nan Fahad baya nan, don bayan gama gasar world cup ƙasar India ya koma, amman duk abubuwan dake faruwa yana gani yana taya Deen murna. Bayan sati biyu da tarewar su sabon gidan Deen ya bar ƙasar don amsa gayyatar da wasu manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan turai suka yi mashi....A sanyaye Salma ta ajiye wayarta bayan ta gama kallon hoton Deen a ƙasar France da ya je, tun ranar da suka yi magana da shi har ya bayyana mata yana son ta basu ƙara yin magana ba, bayan da suka dawo daga gasar world cup da shugaban ƙasa ya karrama su ta tura masa saƙon taya murna, sai dai bai mata reply ba kuma ta ga ya duba saƙon, haka da aka bashi sarauta ma ta tura masa saƙon taya murna shi bata ma ga ya duba ba, duk da ta san yana cikin uzururruka, amman bata yi tunanin za su kai har yanzu ba tare da sun ƙara yin magana ba, gashi ya zo ya yi har kusan sati biyu ba tare da ya neme ta ba har ya koma, zuciyarta ce ta raya mata to ko dai ya fasa son nata ne? A tunaninta in dai kana son mutum ko yaya ne ai zaka samu lokacin shi, wannan tunani ba ƙaramin saka jikinta yin sanyi ya yi ba, gashi yanzu wani irin son shi take ji a zuciyarta, sai yanzu ta gane tun da ma ta kamu da son shi sai da shi ya bayyana mata hakan ta gane, ƙwalla ne suka taru a idanunta, a ranta take raya yanzu ita ya zata yi idan da gaske ya daina son nata, sharr hawayen suka zubo mata ta kai hannu tana gogewa, ƙarshe ta kwanta a saman gadon tare da rufe idanunta tana jin wani irin sabon son Deen na ratsa zuciyarta.
Chapter 166 · 0% Book details