← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 197

Sashe 174

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mashi, ya ɗan dago ido a hankali ya ce, "Gidana..." Salma ta yi murmushi tare da sauke idonta, can kuma ta ɗago tana kallon shi ta ce, "Ba ma sai ka saka ni ba, kawai zaka ga na yi maka ita." Ya ɗan jinjina kai ba tare da ya ce komai ba...bayan ya gama ta miƙe ta zuba mashi drink a hadaddan glass cup, ta miƙa mashi tana faɗin wannan ita ce ta haɗa shi, ya yi murmushi ya amsa ya kai baki, bayan ya ɗan sha ya dakata ya kalle ta, ta ce masa ya yi daɗi ya ɗaga mata kai, "To hada shi zan yi maka." ya ce zata rinƙa yi mashi ai ba sau ɗaya ne za a yi ba, ta yi ɗan faffaɗan murmushi ta ce to, sai da ya shanye wanda ta zuba mashi, za ta kara ya ce mata ya isa ta nuna lemun kwali ta ce to bai sha wannan ba, yana kallon ta cikin ido ya ce bai san ina zai sa shi ba, ko don ta ji hajiya ta ce mashi acici ai yana ƙoshi, yar dariya ta yi, ya sa ta miƙa masa tissue box ya yaga ya goge baki, daga haka ya miƙe itama haka suka nufi cikin falon, Salma ta nuna masa kujera ya ce mata zai tafi ne, ta ce to bari ta faɗa ma aunty, tare suka dawo da ita aunty na murmushi ta ce, "Deen, har za a tafi." a nutse ya ce mata eh tare da yi mata godiya, itama godiya ta yi mashi ta ce amman dai ba Abuja zai koma ba yanzu ko ta ga yamma ya yi sosai, ya ce mata eh sai gobe zai tafi, daga haka suka yi sallama ya nufi ƙofa sun jera da Salma, aunty ta bi su da kallo fuskarta da murmushi har suka fita, zama ta yi akan kujera still tana murmushi a cikin ranta ta raya ko ya baby zata yi da wannan gabjejen mutumin...Salma ce ta dawo cikin falon aunty ta ɗaga ido tana kallonta, tambayar ta ta yi lafiya, Salma ta ce, "Aunty wai na ga awaran ta yi mashi daɗi don kusan ita kaɗai ya ci sosai sai fried rice ba sosai ba, shine na yi tunanin ko tun da akwai a zuba mashi ya tafi da ita." Aunty ta miƙe tana faɗin lafiya lau ai in dai zai tafin da ita, Salma ta ce zata sa ya tafi da ita bari ta dauko takeaway pack a zuba sai a saka a leda, da sauri aunty ta ce, "Ya za ai a zuba mashi a nan, bari a zuba a cikin warmer zai fi." Suka nufi dining, a cikin wasu warmers biyu masu shegen kyau aka zuba awaran, ɗaya aka zuba chicken sauce, ba a zuba mashi coleslaw ba a cewar aunty zai iya bugawa, Salma ta sa aka haɗa mashi da juice ɗin da ya sha bayan an zuba a wani glass bottle, wani basket shima mai kyau da aji aunty ta ɗauko aka zuba kayan a ciki Salma ta tafi, lokacin da ta fito haraban a bakin mota ta ganshi tsaye ya jingina yana latsa wayan shi, dama bayan sun fito kafin su iso wurin motan ne ta ce mashi tana zuwa shine ta koma ta yi ma aunty maganar, a gefen shi ta tsaya ya ɗago ya kalle ta, tana murmushi ta ce, "Aunty ce ta ce in kawo maka awaran ka tafi da ita don saboda kai aka yi." Ya ɗan buɗe ido ba tare da ya ce komai ba, "A ina ka sauka?" Ta tambaya tana kallon shi ya bata amsa da hotel, suka ɗan yi shiru kafin ta ji ya ce mata yana son za su fita gobe da rana idan zai yuwu, Salma da ke kallon shi ta ɗaga mashi kai, ya ce idan ta koma sai ta faɗi ma auntynta ta ce to, ɗaga kai ya yi ya kalli bodguard ɗin da ke a 6angaren da suke yana tsaye daga wurin boot ɗin motan, da turanci Deen ya ce mashi su fiddo abun da ke a cikin boot su kai ciki, cikin girmamawa ya amsa ma Deen da kai, Salma ta bi su da ido tana kallon wasu haɗaɗɗun akwatuna da suka ɗauko lokacin da za su wuce ciki, ɗaya yana riƙe da akwatunan guda biyu sai ɗayan kuma guda ɗaya da wata babbar jaka mai ɗauke da hoton Deen daga gani ta naɗin sarautar shi ce, Salma ta janye idanunta bayan sun wuce....aunty na zaune tana latsa wayarta ta ji murya an furta, "Excuse..." Ta yi saurin ɗagowa, har saida gaban ta ya faɗi ganin mutumin da ke a bakin ƙofar, miƙewa ta yi tana kallon shi kana ganin fuskarta ka san ta tsorata, mutumin ya ɗan ɗaga box ɗin hannun shi ta cikin takunkumin ya ce an ce su kawo, aunty ta ɗaga mashi kai ya kutsa cikin falon ɗayan na biye da shi, a nan gefen carpet suka ajiye kayan daga haka suka ɗan sunkuya ma aunty kai suka juya, aunty ta kasa furta masu komai ta bi su da ido suna tafiya a wani bubbuɗe sai ka ce wasu robot...bayan sun dawo Deen ya miƙe daga jikin motan ya ce mata za su wuce sai sun yi magana, ta ɗan langa6e kai ta ce ok sai kuma ta ce ta saka basket ɗin cikin motan ko boot ya ce ta saka a back seat kada ya manta da shi, ta nufi ƙofan 6angaren da suke shi kuma ya zagaya aka buɗe mashi ya shiga, daga gefe a back seat ta ajiye basket ɗin ta ɗago tana kallon shi, softly ya ce, "Thank you princess." tana murmushi ta ce, "Welcome ur highness." Deen ya yi ƴar dariya har fararen haƙoransa suka ɗan bayyana, ta ce, "Sai Allah Ya kaimu goben?" Ya ɗaga mata kai kafin ya ɗan lumshe mata ido slowly ya furta, "I love you." Kawai Salma sai gani ta yi itama ta ɗan lumshe ido yadda ya yi ta furta, "I love more..." Ita kanta bata san ya aka yi ta samu karsashin hakan ba, zuba mata ido ya yi yana jin sonta na ƙaruwan mashi a zuciya, Salma ta yi kokarin ta dake wurin mayar masa da martanin kallon amman ta kasa sakamakon yadda kallon nashi ya kashe mata jiki, a hankali ta yi murmushi tare da janye jikinta ta fita daga motan, ta ɗan ɗaga hannu tana yi ma Deen da ya jingina jikin seat bye bye, shi dai kallon ta kawai yake da ɗan murmushi, sai da bodyguards ɗin nasa suka ga ta fito sannan na mazaunin driver ya shiga, dayan ya zo ya kulle ma Deen ƙofa kafin shima ya shiga front seat, Salma na tsaye har motan ta juya ta tunkari gate, driver ɗin ne ya fito ya buɗe gate, bayan sun fita ya dawo ya rufe ya ɗan ɗaga ma Salma hannu alamar sallama....Salma ta ɗan sauke yar ajiyar zuciya bayan sun tafi ta juya ta nufi ciki, a falo ta iske aunty zaune, ta ɗaga kai tana kallon Salma, nufar ta Salma ta yi tana zuwa ta faɗa kanta, aunty ta saki faffaɗan murmushi tana tambayarta ya aka yi, jin shiru bata ɗago ba ya sa aunty ta kai hannu ta ɗago da face ɗin ta, lokaci guda aunty ta ɗan zaro ido ganin hawaye a idon Salma ga murmushi kuma tana yi, aunty ta yi dariya ta ce, "Duk farin ciki ne haka baby." Salma ta kasa cewa komai sai dariya take, zaunar da ita aunty ta yi tana kallon ta ta ce, "Sun tafi?" Ta ɗaga mata kai, ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "To ya kuka yi da shi, ya yi maki maganar wanccan ɗin ne?" Salma ta bata labarin yadda suka yi, aunty na murmushi ta ce, "Ni dama na san har da uzururruka ya sa bai neme ki ba, kuma haka nan ba zai ce yana son ki ba kuma wai ya dawo ya ce ya fasa. Yanzu ke nan kin amince ya aure ku ku biyun?" A hankali Salma ta ɗaga mata kai alamar eh, aunty ta ɗan yi shiru tana kallon wuri guda, ganin haka ya sa jikin Salma yin ɗan sanyi, a hankali ta ce, "Amman...ni gani nike kaman dangin shi ba za su amince ba tun da ita yar'uwar shi ce." Kamar Salma ta san abun da ke ran aunty, kallon ta ta yi tana ƙoƙarin basar da tunanin da take yi ta dafa ta ta ce, "Kar ki damu, tun da bamu san ya dangin nasa suke ba, kuma kakarsa ai ta san ki kuna mutunci da ita. Mu ci gaba da yin addu'a, idan Allah Ya ƙaddaro shi mijinki ne kamar yadda na faɗa maki ba wanda zai hana hakan faruwa." Salma ta ɗaga mata kai, "Ya yi maki magana kan lokacin da yake son ku yi auren ne?" Salma ta ce, "a'a, ya dai ce karatu na a London zan ci gaba." Aunty ta ɗan gwalo ido sai kuma ta saki dariya ta ce,"Inyee, ki ce London zamu kai amarya." Salma ta yi ƴar dariya, aunty ta kalli akwatunan da aka ajiye ta ce mata na minene, Salma ta ce kawai ta ji ya ce a kawo, miƙewa aunty ta yi tana faɗin bari su duba, bayan ta jawo akwatunan ta shiga ƙoƙarin buɗe su amman ta kasa, kallon Salma ta yi da ɗan mamaki ta ce to ya aka yi zip ɗin ya ƙi buɗewa, Salma ta ce bata sani ba, itama Salma ta shiga ƙoƙarin buɗewa abun duniya ya gagara, aunty ta ce, "To ko dai zip din suna da matsala ne, tun da ai ga wurin rufe su nan kuma ba a rufen ba...amman kuma a ce gaba ɗaya zip ɗin su ke da matsala..to ko dai akwai yadda ake buɗe su ne bamu sani ba." Salma dai ta yi shiru....ba irin kokarin da aunty bata yi ba amman fir zip ɗin ya ƙi jawowa balle ya buɗe, ta kalli Salma ta ce, "Yau an bani an kawo ma ƴan kauye abu." Salma ta saka dariya, aunty ta fara dudduba jikin akwatin tana neman irin ɗan katin da ake sakawa na bayani, sai gashi ta
Chapter 174 · 0% Book details