Sashe 101
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya ɗago tare da girgiza mata kai cikin sanyin murya ya ce, "A'a Ammi, Allah ne shaida na ni don zumunci nike zuwa." Ammi ta ce, "Da kuma saka ido ko? Wato yadda mahaifinka kafin Allah Ya ɗauki ransa ya saka mana ido, ƙiri ƙiri ya rinƙa nuna mana hassada baya son ci gabanmu, ya fi son mu ci gaba da zama a ƙarƙashin sa muna roƙonsa yana taimaka mana, shine kai ma yanzu zaka dasa daga inda ya tsaya ko?" Shiru Mukhtar ya yi idanunsa a ƙasa, ta ci gaba, "To ni ba zan lamunci a saka ma zuri'a ta ido ba, don muma ba wanda muka saka ma ido, hasali ma bamu san ya kuke gudanar da rayuwar ku ba, don haka ka cire idanuwanka daga kan rayuwar iyalina, ku ma ai ba wanda ya san abun da kuke aikatawa a 6oye, sai mutum ya rinƙa nuna shi na Allah ne alhali Allah kaɗai ya san mugun abun da yake aikatawa a baɗini. Kuma da kake mata maganar ta yi aure ita ƙanwarka Fadeela ba tana zaune a gida ba har yanzu bata yi auren ba, ita miyasa baka saka ta ta yi auren ba tun da ka san shine alkhairi a wurin mace? To daga yau in dai ka san abun da ke kawo ka gidan nan ke nan kada ka sake zuwa, zumuncin da ka yi mana mun gode Allah Ya bada lada, shima mahaifinka ku san hakan ce ta faru a tsakaninmu da shi, ba dalili bamu saka ma kowa ido ba mu a saka mana, sam ni ban lamuntar hakan. Ka gaida gida." Tana kai wa nan ta ja hannun Aseeya suka nufi ciki tana ƴan maganganu, ba ƙaramin sanyi jikin Mukhtar ya yi ba, da ƙyar ya miƙe ya ja kafafunsa da ya ji sun masa nauyi ya fita, yana saman mashin ɗinsa bayan ya kamo hanya, a hankali ya ke kai hannu yana goge ƙwallan da ke zubo masa, ba komai ne ya sa shi zubar da ƙwalla ba sai jin ƙazafin da Ammi ta yi ma mahaifinsu, wanda Ummansu ta basu labarin irin jajircewar da ya yi wurin tallafa ma rayuwar su amman shine suka saka masa da hakan. Tun daga wannan ranar bai ƙara zuwa gidan ba, farko bai yi niyyar abun da ya faru ya sa shi yanke zumunci da su ba, amman saboda maganganun da ta yi akan mahaifinsu ne ya sa ya haƙura da zuwa gidan, ko Ummansu da sauran ƴan'uwansu bai sanar da su abun da ya faru ba, don bai son gaba ɗaya su yanke zamunci da su, duk da dama ita ummansu tuni ta fita sha'anin su, suma sauran ƴan'uwan shi ba wani zumunci suke da su ba sosai, da Sapna tana tallafa masu sosai, wani lokacin idan ta zo har gidan take zuwa ta yi masu alkhairi mai yawa, itama daga baya basu san mi ya faru ba ta janye masu jiki ta daina yi masu duk abun da take masu, amman ƙanwar mahaifinsu Maryam wadda a yanzu ba a ƙasar suke zaune ba tana tallafa masu sosai kuma idan suka zo ƙasar tana ziyartar su ko kuma su su je. Nannauyar ajiyar zuciya Mukhtar ya sauke bayan ya gama tunano abun da ya faru, ji ya yi gaba ɗaya jikinsa bai masa daɗi hakan ya sa shi fita ya kulle shagon, gidansu da ke a gefen shagon ya shiga, gidan nada ɗan girma ba laifi kuma yana da kyau, gaba ɗaya tsakar gidan broken tiles ne kuma ginin bai ji jiki ba duk da tun gidan da mahaifinsu ya rasu ya bar masu ne, amman ana mashi gyara lokaci bayan lokaci. Bayan rasuwar mahaifinsu ummansu ta ƙara yin wani aure bayan wasu shekaru, amman ba ta bar gidan ba har Allah ya yi ma mijin da ta aura rasuwa shekarun baya, tun daga nan bata sake yin wani aure ba yanzu ma har ta manyanta, gaba ɗaya sun taru sun rufa ma kan su asiri sun jajirce suna yin sana'oi sannan akwai masu yin aiki a cikin su, dama su biyar ne mahaifin su ya bari, babban yayan su da mai bi mashi sai mace guda duk sun yi aure, yanzu daga Mukhtar wanda ya kammala karatunsa na degree bai kai ga samun aiki ba, sai autar su Fadeela da ke cikin yin karatu a BUK suka rage a gidan, itama Fadeela da tuni ta yi aure don tana da samari masu son ta da yake suma yaran gidan tubarkalla kyawawa ne sosai, wasu farare ne tas yayin da wasu farin nasu ya gauraya da kalar mahaifiyarsu da take wankan tarwaɗa hakan ya sa hasken su ya fita daban, sam Fadeela bata sauraran masu son ta don ita ba wanda Allah Ya jarabe ta da son shi sai Bashir na gidan su mom, ba ƙaramar wahala zuciyarta ke bata ba akan son shi, gashi shi kuma sai faman gara ta yake yi, ba irin faɗan da ba a yi mata ba a gida kan ta rabu da shi amman ta kasa, yanzu haka cikin dagar da ake ta yi da ita ke nan a gida kan ta rabu da Bashir ta fidda miji a cikin masu sonta amma abu ya ci tura......