← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 197

Sashe 53

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kina zama a kusa da wuta with this, ba ki tsoron ya kama wutan?" Ya yi maganan yana nuni da hijabin jikinta, damm! gaban Salma ya faɗi, ai ko a cikin magagin bacci ta ji muryarsa wllh sai ta gane, kokonton anya kuwa shine ta shiga yi, to mi zai kawo shi nan idan shi ne? Ya ma za ai ya san wurin? To amman kuma tabbas wannan muryarsa ce, tana cikin yin wasi-wasin wani mai mashin ya shigo cikin layin hasken babur ɗin ya haske mashi rabin fuska farar fatarsa ta bayyana, tabbas shi ne! zuciyarta ta gasgata hakan, ƙirjinta ya shiga yin bugu fat, fat, sai ta ji ma kamar ƙafafuwanta na barazanar kasa riƙe ta, ɗage mata gira ya yi ya ce bata ji abun da ya ce ba? ta shiga motsa baki da ƙyar ta tattaro kalaman bakinta ta ce mashi ai tana kula sosai, kauda kai ya yi ta ji ya ce It’s not safe to go near fire da dogon abu irin haka, kamar yar ƙadangaruwa ta gyaɗa kai ta ce mashi to ta gode za ta daina saka irin shi idan za ta yi tuyan, hannu ya saka cikin aljihun gaban wandon shi, miƙo mata abun da ya fito da shi ya yi ta matso ta amsa, lokaci guda ta gane kuɗi ne masu yawa, a dabarbarce ta ce, "Awaran bata kai ta haka ba, duka ma wadda ta rage bata da yawa." Ya ce mata ta raba ma mutane shi, daga haka ya maida mask ɗin, ganin yana ƙoƙarin juyawa da sauri ta ce, "To kuɗin sun yi yawa ai, duka awaran ma bata wuce ta dubu ɗaya ba idan ma ta kai..." A taƙaice ya ce ta kai kuɗin gida, daga haka ya yi gaba abun shi ba tare da ya tsaya sauraren abun da za ta ƙara cewa ba, tamkar rainon sakarya haka ta bi shi da kallo yayin da yake tafiya bakinta a buɗe tsabar mamaki.....

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_

ZAINAB BATURE

19

Da tsananin mamaki innarsu Salma ke juya kuɗin da ta kawo mata wanda rafar yan dubu dubu ce guda biyu. "Yanzu kika ce haka nan ya zo ya baki wannan uban kuɗin ya ce ki kawo?" Ta tambaya idonta a kan Salma dake tsaye a gabanta bakin baranda, kai ta ɗaga ta ce, "Wllh innarmu yadda na faɗa maki." Hannu ta kai ta riƙe haba ta ce, "To amman ya akai ya san nan gidan har ya zo?" Ta tambaya da mamaki a kan fuskarta, Salma ta ce, "Ni ma wllh abun da nike ta mamaki ke nan innarmu, kuma na faɗa maki ai maganganun da muka yi da hajiya ɗazun sam shi bai ma saka baki ba lokacin da take mani maganar tuyan awaran." Gyaɗa kai innar ta yi ta ce, "To wataƙil dai daga hiran taku ne yana sauraro, kuma ƙilan bayan kin taho ya tambayi hajiyan har ya san in da kike yin tuyar shine ya zo. Dama Sagir yana ta faɗin irin uban alkhairin da yake ta yi ma mutane, an gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi ya ƙara masa ɗaukaka. Idan kuka sake haɗuwa sai ki yi masa godiya sosai." Amsawa Salma ta yi da to, tana shirin juyawa innar ta tambaye ta ina zata je ta ce mata za ta je wurin awaran ne, "To ku ƙarasa soya sauran sai ku rabar ma mutane tun da haka ya ce, ki ba Hamza ya kai gidansu Habu." Amsawa ta yi da to cike da jin daɗi ta nufi hanyar waje, ci gaba da juya kuɗin innar tasu ta yi tana mamakin irin kirkin Deen, haka nan ya ɗauki kuɗi masu yawa lokaci guda ya ba su! tabbas shi ɗin na daban ne ta ayyana a ranta tare da juyawa ta nufi ɗaki. Bayan Salma sun dawo gida suka zauna cin abinci har da su Sagir da suka dawo, suma sun yi mamaki sosai bayan da innarsu ta sanar masu zancen kuɗin da Deen ya basu, Sagir ya ce ai wannan ba wani abu bane a wurinsa, ya shiga basu labarin irin abubuwan alkhairi da yake ta yi ma mutane, gaba ɗaya suma su Auwalu sun yanke cewa maganar da Salma ta yi da hajiya ce ta sa ya zo ya bata kuɗin, sai dai sun yi matuƙar mamakin yadda ya iya takowa ya zo ƙofar gidan nasu, Sagir ji yake inama sun haɗu da shi. Bayan Salma ta gama cin abincin banɗaki ta wuce ta yo wanka, dama ta yi sallar isha tun lokacin da Deen ya zo aka ce tana cikin gida to salla ta je yi, sam bata wasa da salla da lokacin ta ya yi take barin abun da take yi ta je ta yi, shiryawa ta yi da doguwar rigar bacci ta saka hula a kanta jikinta na ta ƙamshin humra da ta shafa, littafinta ta ɗauko don ta yi karatun test da za a yi masu, sai da ta yi addu'a kafin ta kwanta a saman ɗan gadonta da ya sha shimfiɗar wankakken zanin gado, musamman babanta ya haɗa mata gadon da ɗan mirror har da ƴar wardrobe mai gida biyu, hannunta ɗaya riƙe da wayar innarsu keypad ta kunna torch tana haska littafin, sai dai tana fara yin karatun zuciyarta ta ƙi bata goyon baya ta hanyar jan akalar tunaninta zuwa faɗawa tunanin Deen, sai ma ta rinƙa ganin fuskarsa a jikin littafin, ƙarshe dole ta ajiye shi a gefe ta ci gaba da ba zuciyarta goyon baya, abubuwan da suka faru tsakaninsu yau ta shiga tunanowa tana sakin murmushi kamar wata zautatta, komai na shi ba ƙaramin burge ta yake ba, ba ƙaramin tafiya ya yi da ita ba lokacin da ya yi ma kansa kitson nan, ko ina ma kitson? ta raya don ba alamun shi lokacin da ya zo ƙofar gidansu, wata zuciyar ta bata amsa da ƙilan ya kwance da zai fita waje, jinjina irin kirkin sa ta shiga yi yadda har ya iya takowa kofar gidan nasu ya bata kuɗi, Fahad ne ya faɗo mata a rai nan take ta yanke hukuncin Deen ya fi shi kirki nesa ba kusa ba, a ranta take raya tabbas duk wadda ta aure shi wllh ba ƙaramin dacewa ta yi ba. Tana ta tunane-tunane a haka bacci ya yi awon gaba da ita.

Washe gari Asabar, misalin ƙarfe tara saura na safe su Salma na zaune a ɗakin innarsu, wanda ba laifi ɗakin babba ne, akwai gado mai kyau da dressing mirror da side drawers ɗinsa, sai wardrobe mai gida biyu, daga farkon shiga dakin a gaban gado akwai kujeru mai mazaunin mutum biyu da masu mazaunin mutum ɗaya guda biyu, Salma na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum ɗaya, yayin da Imran da Hamza ke zaune a tsakiyar kujerun saman ɗan madaidaicin carpet dake a saman ledar tsakar ɗakin, gaba ɗaya suna sanye da uniform ɗin islamiyya, kowannan su kofi ne a hannunsa suna yin karin kumallo,

"Faka-faka, ina abun karin kumallo na?" Sagir da ya faɗo cikin ɗakin ya faɗa, ƙafafunsa na sanye da dogayen safuna sai wandon ƙwallo hannunsa na riƙe da rigar bai kai ga sakawa ba, duk suka kalle sa, zama ya yi a saman kujera kusa da Salma, "Innarmu ina nawa?" Tana kallonsa ta tambayi saurin mi yake yi haka? Amsa ya bata da, "Wllh gasa ce zamu yi gaba ɗaya team ɗin ƙwallon garin nan, a cikin waɗanda suka yi nasara Nuree Jr zai zabi ƴan wasan sabon club ɗinsa mai suna 'FT STRIKERS." Kai Innarsu ta jinjina alamar ta gane,

"Tare da shi zaku yi ƙwallon?" Salma da ta kur6i kunu ta tambaya, ya bata amsa da a'a amman a gabansa za a yi gasar yana kallo, bayan an zuba masa kunnun ya ɗauka yana sha tare da ƙosai, ba tare da 6ata lokaci ba ya miƙe innarsu ta tambayi har ya gama ya ce mata eh, ta tambayi ko a ƙara masa ya ce mata a'a bai son ya cika cikinsa sosai ya kasa yin abun kirki,

"To ni zan tafi innarmu ki yi mani addu'ar nasara, dama baba tun da muka je sallar asuba na sanar masa shima ya yi mani addu'a." Tana murmushi ta ce, "To Allah Ubangiji Ya baku sa'a Sagir." Da sauri ya amsa da Amin yana ƙoƙarin saka rigar kwallon, "To ni ba zaka ce in yi maka addu'ar ba?" Salma ta faɗa tana wurga masa yar harara,

"Ke dalla wake ta wata addu'arki, ga mai kankat nan wadda da ta yi an kar6a ba shamaki." GyaÉ—a kai Salma ta yi ta ce to shike nan, Innarsu dake murmushi ta ce, "A'a Sagir, wannan yarinyar tawa fa yar baiwa ce Allah, kada ka raina addu'arta don Allah na amsa mata addu'ointa." Bayan ya gama saka rigar ya kalli Salma yana Æ´ar dariya ya ce to ta yi masa addu'an,

"Ban yi!" A fusace ta faɗa, hannu ya kai ya kama kanta yana dariya ya ce,"Haba my lovely sis, ni da ke ai bata 6aci kin san wasa nike maki ina buƙatar addu'ar ku ƴan'uwana." Tana murmushi ta ce masa Allah Ya basu sa'a, amsawa ya yi da Amin tare da sakar mata kai, sai kuma ya ce, "Da kar ki yi mini addu'ar ki ci na jaki." Harara ta wurga masa tare da faɗin, "Kamm! To na ma janye addu'ar tawa." Nufar ƙofa ya yi yana dariya yana faɗin ta baya ta rago, su Imrana suka ɗaga murya suna yi mashi Allah Ya bada sa'a ya amsa lokacin ya fice.
Chapter 53 · 0% Book details