← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 197

Sashe 2

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan kammala taron mahaifiyar Salma wadda ta kasance farar mace sannan tana da ɗan jiki amma ba sosai ba, yanayin ta bata da tsawo amman kuma ba gajera bace, tana sanye da wani haɗaɗɗan lace, tun daga wuyanta zuwa hannunta zinari ne, kana ganin ta ka ga wayayyar mace ƴar boko, ta rungume Salma jikinta cike da farin ciki tana yaba mata kan ƙwazon da ta nuna a wurin, muryarta da tsananim farin ciki take faɗin, "I am really proud of you my baby. Allah Ya raya min ke ya ci gaba da albarkantar rayuwar ki. In sha Allahu sai kin zamo abun alfahari ga kowa, ina jin hakan a raina." Ɗagowa Salma ta yi da murmushinta mai burgewa ta ce, "Thank you my aunty Kubra, nima ina alfahari da ke." Ƙara rungume ta ta yi tana jin ƙaunar yarinyar na ƙara ninkuwa a cikin ranta, ƙawar aunty Kubra da suka zo tare mai suna Naja'atu itama ta kamo Salma jikinta ta taya ta murna tare da bata kyautar da ta kawo mata, ta yi mata addu'oin fatan allkhairi a rayuwarta.

"Aunty, daddy bai zo ba? Ban gan shi ba." Salma ta tambaya tana kallon Aunty Kubra da farin cikin dake kan fuskarta ya ɗan canza jin tambayar da Salma ta yi, ganin Salma ta kafe ta da ido alamar amsar ta take jira ta yi ɗan murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Wani uzuri ne ya taso masa bai samu zuwa ba, na san idan muka koma gida zai taya ki murna." Kai Salma ta jinjina tana murmushi, kallon juna suka yi ita da Naja'atu, ganin fuskar Kubra ta nuna alamun damuwa ta ɗan girgiza mata kai alamar kada ta yi hakan. Bayan gama komai suka nufi wurin da aunty Kubra ta faka motarta, a seat ɗin baya aka saka kyaututtukan Salma, aunty Kubra ta shiga mazaunin driver, Naja'atu ta zauna a kujerar gaba yayin da Salma ta zauna baya. Bayan sun hau hanya, akai akai Salma take kallon kyaututtukanta farin ciki ya bayyana a kan fuskarta, ta cikin madubin motar aunty Kubra ke ta kallonta yayin da a daidai wannan ga6ar ita kaɗai ta san abun da ke kai kawo a cikin zuciyarta. "Da alama kin ji daɗin kyaututtukan da kika samu ko baby?" Da sauri Salma ta kalli Aunty Naja'atu da ta juyo ta yi mata maganar, kai ta ɗaga mata tana yin ƴar dariya, aunty Naja'atu ta ce mata haka nasara take kawo ma mutum alkhairai don haka ta ci gaba da bada himma kan karatunta, Salma ta amsa mata da in sha Allah. Ba gida kai tsaye suka wuce ba, wani babban shopping mall aunty Kubra ta kai Salma ta ce ta zabi duk abun da take so, itama ta zabar mata wasu abubuwan, aunty Naja'atu ma ta ƙara siya mata wasu kyaututtukan, daga nan wani eatery mai kyau suka wuce suka ci abinci aunty Kubra ta yi ma Salma takeaway ɗin small chops da su ice cream kafin suka wuce gida.

Misalin ƙarfe tara na dare Aunty Kubra ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin, tana sanye da doguwar rigar bacci kanta ta saka hula, idonta akan Salma dake kwance a saman gado tana sanye da kayan bacci riga da wando da kuma hula a saman kanta, kitson gabanta sun ɗan rufe mata gefen fuskarta da ta ɗaura jikin ƙaton teddyn da ɗazun aka siya mata a mall, a bakin madaidaicin gadon kalar na yara aunty Kubra ta zauna tana ci gaba da kallon Salma da ke yin bacci hankali kwance, ta ɗan dauki lokaci tana kallon fuskarta yayin da a cikin zuciyarta ba abun da take yi face kukan zuci, yanzu shike nan dole ta rabu da yarinyar nan ta mayar da ita wurin iyayenta, dama tamkar ara mata ita aka yi saboda tsananin ƙaunar ta da take yi, gashi wa'adin da ta ɗauka na ruƙonta ya cika, ko ba haka ba, dole ta haƙura ta maida ta wurin iyayenta ko don saboda yawan sa6anin da zamanta ke haddasa masu da mijinta, ƙiri-kiri yake nuna yana yin kishi da yarinyar, a cewarsa Kubra ta fi fifita yarinyar fiye da kula da shi, ko da yaushe a cikin ƙorafi yake kan tafi bawa abu biyu muhimmanci, wato aikinta na asibiti kasantuwar ta babbar nurse, sai kuma Salma, a cewarsa koda yaushe idan tana gida to lokacin ta na Salma ne ba shi ba. Ta san duk ba komai bane ya sa take matuƙar ƙaunar yarinyar face haihuwa da Allah bai ta6a bata ba gashi har ta ɗan fara manyanta, idanunta ne suka ciko da ƙwalla, daga baya ta kifa kanta a saman gadon tana yin kuka a hankali, da sauri ta ɗago bayan ɗan lokaci jin an dafa mata kai, suka haɗa ido da Salma wadda ta farka tana kallonta da idanunta dake ɗauke da bacci, "Aunty Kubranah mi aka yi maki kike kuka?" Salma ta tambaya da muryarta da bacci bai saka ba, da sauri Kubra ta kai hannu tana share hawayen fuskarta tare da gyara zamanta, ɗan murmushi ta yi mata ta ce, "Ba abun da aka yi mani baby, ba kuka nake yi ba." Salma ta bita da ido ta ce, "Ba na ji kina yin kuka ba, kuma har kina share ƙwalla. Daddy ne ko?" Fuskar Kubra kamar zata ci gaba da yin kukan ta girgiza mata kai alamar a'a, "To don Allah autynah tell me, mi yasa kike yin kuka?" Ta kai maganar itama kaman zata fara yin kukan, ta san idan har bata faɗa mata ba itama kukan zata yi, hakan ya sa ta ƙara matsawa tare da kamo hannunta, cikin karyayyar murya ta ce, "Ba wani abu bane baby, kawai na ji har na fara missing ɗin ki ne, za ki tafi ki bar ni." Ɗan shiru Salma ta yi tana kallonta, sai kuma ta ce, "To idan baki son in tafi zan zauna nan ba zan koma ba." Da sauri ta girgiza mata kai, "No baby, iyayenki da ƴan'uwanki suma suna son ki a kusa da su, idan baki koma ba zan zama mai son kai, ke kan ki rayuwarki a nan cikin kaɗaici kike yin ta, koda yaushe daga ni sai ke, ga zarya da nike yi da ke wani lokacin sai dai in tafi da ke asibiti wani lokacin in kai ki gida, can kuwa kin ga kina da ƴan'uwa, zaku yi wasa ku ci abinci tare ku yi hira, gara ki koma cikin ƴan'uwanki don suma suna muradin ki a kusa da su, musamman Sageer, duk muka yi waya kin ga sai ya tambayi yaushe zaki koma." Shiru Salma ta yi tana kallonta, aunty Kubra ta ci gaba da kwantar mata da hankali, a hankali Salma ta ce, "To ki daina yin kuka aunty Kubra, ai zan rinƙa zuwa hutu nan, kuma zamu rinƙa yin waya har da vedio call." Da sauri ta ce mata ta bari ba zata ƙara yi ba, ɗan yatsa Salma ta miƙa mata ta ce ta yi mata promise ba zata ƙara yin kuka ba, faffaɗan murmushi Kubra ta yi, har da irin yadda yarinyar itama ta damu da ita ke ƙara mata ƙaunarta, yatsanta ta bata suka yi promise ɗin, tambayarta Salma ta yi daddy ya zo ta ce mata a'a yau ba nan zai kwana ba, Salma ta ce, "To ki kwanta a nan." Aunty Kubra na murmushi ta ce, "To ai zan takura maki kin ga gadon ƙarami ne, sai dai mu je can ɗakina mu kwanta." Salma ta ɗaga kai, dama duk idan ba a gidan mijin aunty Kubra ɗin zai kwana ba da yake yana da wata matar, a ɗakin aunty Kubra suke kwana, safkowa suka yi don tafiya bedroom din nata, aunty Kubra ta duƙa ta ce ma Salma ta hau bayanta, dariya Salma ta saka tare da hayewa saman bayan nata, bayan ta miƙe Salma dake ta dariya ta ce, "Aunty Kubra har yanzu wai ba ki jin nauyi na da kike goya ni?" Tana dariya itama yayin da take nufar kofa ta ce, "Ko kin fi haka zan goya ki babyna." Daɗi ya kama Salma ta kwantar da kanta saman bayanta daga haka suka fita.

Five years later (bayan shekaru biyar....)

Abuja Nigeria.

Nnamdi Azikwe International Airport.

Wednesday, 11:30am

Iskar safiyar laraba tana kaɗawa cikin natsuwa, a hankali gudun private jet ɗin da ya sauka ya fara ragewa yayin da yake yin tafiya akan hanyarsa, hasken ranar da ya haske jikin farin jirgin ya sa shi sai sakin sheƙi yake. A gefe guda cikin tarmac ɗin wasu mutane ne a tsaitsaye, wanda daga gani tarbar wani suka zo kuma mutanen masu matsayi ne kasantuwar ba kowa ake bari ba ya je wurin da jirgi ke sauka.
Chapter 2 · 0% Book details