← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 197

Sashe 37

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan ai rashin ƴanci ne, kuɗi dai naka ne kuma yanzu ai ka mallaki hankalin kan ka tun da har kana da iyali, sai a damƙa maka hakkin ka ka rinƙa yin hidindimun ka, don haka sai ka kira dad ɗin ka nuna mashi kana buƙatan kuɗi sai ka bani." Shiru ya yi idon shi akan ta yayin da yake a tsaye ita kuma tana zaune a bakin gado ta juya mashi kai, cikinta har ya fito jikinta ya ƙara yin kyau sosai fatar nan kamar ka ta6a jini ya zubo, duk fa abun da ya ja wannan taƙaddamar kawai don ya zo yana neman ta bashi hakkinsa ne wanda tun da ta samu ciki sai ta gadama take bashi daman hakan, ya san indai ba yi mata yadda take so ya yi ba shima ba zai samu abun da yake so ba, tunanin yadda zai tunkari mahaifin shi da buƙatar kudi har miliyan ɗaya yake yi, yasan koda zai bashi to sai ya ji mi zai yi da su, jiki a mace ya nufi hanyar barin bedroom ɗin ta juyo ta bi shi da kallo fuska a ɗaure, ƙwafa ta yi bayan ya fita a fili ta ce wllh in dai ana son zaman lafiya to dole a yi mata abun da take so, kuma duk fa abun nan ba kowa ne ya haddasa shi face Amminsu, dama tun bayan auren take sata ta tura mata kuɗi daga dubu ɗari, ɗari da hamsin, dubu ɗari biyu, kuma duk yana bata, wannan karon sai ta ce wai ta sa ya bata miliyan ɗaya saboda tafiya zata yi buƙatu na iya haye masu.

A falo ya zaune yay zugudum bawan Allah, haƙiƙa har ya fara gajiya da halayen Jameela, saidai kuma son da yake mata ya sa baya iya yin wani katabus kan hakan, ya ɗauki tsawon lokaci yana wasi-wasin kan shawarar da ya yanke ta kiran dad din su, cike da fargaba ya ɗauki waya ya kira shi, bayan sun gaisa ya yi shiru, dad ɗin ya fahimci da maganar da yake son yi ya kasa ya tambaye shi lafiya, da ƙyar ya ce mashi dama kuɗi yake so miliyan ɗaya, ɗan jimn dad ɗin ya yi kafin ya tambaye shi mi zai yi da kudi haka, cikin in ina ya ce mashi dama yana son zai ba wife ɗin shi wasu in sun je bankwana ta ba iyayenta sai kuma akwai uzururrukan da zai yi da sauran, bayan ya gama yi mashi bayani dad ɗin ya ce zai yi mashi magana suka yi sallama, suna gama yin wayar ya kira matar shi hajiya dama tsakaninsu ba su 6oye ma juna komai, ya sanar mata game da buƙatar Ibraheem ya ce mata in tana ganin lafiya lou ta tura mashi kuɗin, cike da 6acin rai ta ce mashi ya ƙyale shi ba za a bashi kudi ba haka, daga yanayin yadda ya yi magana ya fahimci da wani abu, ya tambaye ta mike faruwa, ta ce mashi Ibrahim so yake ya zama shashasha wanda mace zata rinƙa juyawa, ta tabbatar matar ce ta buƙaci waɗannan kuɗaɗen, in ba haka ba har wani uzuri ne gare shi na kuɗi da ba zai iya yi da kuɗaɗen hannun shi ba, nan ta shiga faɗa mashi irin abubuwan dake faruwa har da buƙatar da ta kawo na a taho da ƙanwarta, ɗan murmushin dattako ambasada ya yi don ya daɗe da sanin kowace uwa bata son ta ga mace na juya mata ɗa, kwantar mata da hankali ya yi ya ce shi yana ganin a bashi kuɗin kawai tun da dama na shi ne, yama yanke shawarar zai mallaka mashi dukkan dukiyar shi ta ci gaba da kasancewa a wurin shi tun da ya mallaki hankali har ya aje iyali, hajiya bata nuna amincewa akan hakan ba ta ce mashi maganar ya mallaki hankali da saura tun da ya bari mace na juya shi, yana murmushi ya ce mata so ne ya ja mashi hakan ta rabu da shi a hankali zai dawo cikin hayyacin shi. Ƙarshe Jameela ta yi nasarar karbar kudin.

Bayan sati guda suka tafi ƙasar Australia, farin ciki a wurin Jameela kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta a ƙasar waje, sosai ake kula da ita bayan ta fara zuwa asibiti, sai dai duk yadda take murna da zuwan ta ƙasar saida murnar ta so komawa ciki saboda yadda take muzanta sakamakon rashin iya turanci, kowa ya ganta bai yin tunanin bata iya turanci ba haka zatai ta faman raba idanu idan ana yi mata saboda bata iya komai ba in ba irin su 'Yes, come, thank you..' da sauran irin ƴan guntayen kalmomi, dole koda yaushe tana tare da Ibrahim saboda haka, ko a gida in suka yi baƙi haka zata yi wuriri sai dai hajiya ce ke zame mata tafinta in ana mata magana, hakan yasa duk ta bi ta raina kanta. Ba a ɗau lokaci ba ta roƙi Ibrahim kan ya rinƙa koya mata turanci, da yake tana tsananin son ta iya ta hakan ne shima yake samun yadda yake so a tare da ita ba tare da ta ja mashi rai ba, cikin daɗin rai ya fara koya mata, amman daga baya abun ya fara gundurar sa saboda yadda kan nata baya saurin ɗauka, daga baya kawai sai ya samo mata baturiyar malama da take zuwa tana koya mata, ita kanta malamar ba a ɗau lokaci ba ta fahimci kan Jameela baya saurin ɗaukar karatu, haka dai tai ta ƙoƙari tana koya mata tun da biyanta ake.

Bayan cikinta ya kai wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta san6alo santalelen jaririnta kamar ɗan aljanu tsabar kyau, hatta turawa haka sukai ta yabon kyawun yaron, bangaren uwar yaron wato Jameela kuwa ba a magana sam fuskarta ta kasa boye farin ciki da zumuɗin babyn, ba kamar da farko ba da bata so samun cikin ba, ita kanta kakar shi wato Hajiya ba ƙaramin farinciki ta shiga ba da ganin kyakkyawan jikan nata tamkar ɗan balarabe, a Nigeria ma duk wanda ya ga hoton babyn sai ya yaba da irin kyawun shi sai murna dangi suke. Bayan yin haihuwar da kwana ukku Sa'ad suka iso ƙasar daga kasar France da a lokacin can yake aiki tare da matarsa Amina da kuma yaron su Fahad wanda a lokacin yake da shekaru ukku da ƴan watanni, shima Fahad tubarkalla kyakkyawa da shi don ya ɗauko haske da kyawun mahaifiyarsa duk da akwai kamanin Sa'ad a tare da shi, kuma shima mahaifin na shi yana da kyau ba laifi, tun da Fahad ya ɗaura idanun shi akan babyn ya fara son shi ya maƙale mashi, koda wani lokaci yana a wurin baby da an yi yunƙurin ɗaukar shi zai kama kuka sai da ƙyar ake raba shi da babyn ko idan ya yi bacci. Bayan sati ɗaya da yin haihuwar gaba ɗaya suka taho Nigeria, nan yan'uwa da abokan arziki suka shiga zuwa barka, da sati ya zagayo aka yi taron suna inda yaro ya ci sunan kakan shi wato Nuraddeen (Deen) A lokacin Jameela ta ji haushin ƙin bin ra'ayin ta da ba a yi ba na a saka sunan mahaifinta ko kakanta, dad ɗin Deen ya bata haƙuri kan in suka ƙara haihuwar namiji sai a saka mashi, ƴan'uwanta na Kano duk sun zo har da Ammin su, suna na gani na faɗa aka yi inda saboda jin daɗin saka sunan Ambasada da aka yi ya bada ƙaton shanu aka yanka ma baby, ba ƙaramar zalama dangin Jameela suka nuna ba a wurin sunan inda duk suka kwashe naman suka ba su Hajiya ɗan kaɗan, kowa kuma ya fahimci abun da suka aikata har da shi kan shi dad ɗin Deen, amman ba wanda ya tanka masu don sun fi ƙarfin hakan, bayan gama suna haka suka ƙi tafiya har da Ammin ta su sai bayan kwana biyar sannan suka tafi, Amminsu duk ta tattare kayan suna da Jameela ta samu abun takaici har da kayan baby da aka kakkawo mashi don zalama su basu kawo ba amman sun kwasa.

A lokacin an bar ma Jameela ƙanwarta Naila ta zauna mata duk da akwai dattijuwa da hajiya ta sa aka kawo mata tana kula da ita, lokacin Naila bata wuce shekaru tara ba amman bata jin magana tsagera ce ta gaske sam bata da kunya, ƙiri-ƙiri idan ƴan'uwan hajiya suka zo barka sai su hana su ganin jaririn koda yana a hannun wani tsakanin Jameela da Naila basu ba da shi a gan shi, akwai watarana da wasu ƴan'uwan hajiya suka zo daga ƙauye hajiya ta saka ƴar aikinta Asabe ta rako su part din su Ibrahim don su yi barka, a wulaƙance Jameela ta tarbe su, a lokacin ba don ganin idon ƴar aikin hajiya ba da ba abun da zai sa ta bari su zauna mata akan kujera, yadda take bin su da ƙasƙantaccen kallo tana yamutsa fuska sai ka ce ta ga kashi, dama lokacin tubarkalla jikinta ya ƙara cikowa ta yi dumurmur, suka gaisa ta amsa masu a daƙile, bayan ɗan lokaci ɗaya daga cikin matan ta kalli Naila dake zaune riƙe da Deen ko kallon su dama bata yi ba tun da suka shigo idonta na akan tv, dama ba iya gaida mutane ta yi ba, da yar fara'a matar ta ce mata ta kawo masu jaririn su gani ta yi kamar bata ji ta ba, sai da Asabe mai aiki ta sake maimaitawa ta ce bata ji ana mata magana, sannan ta juyo ta yi masu kallon hadarin kaji bata da niyyar tasowa ta kawo shi, ganin haka yasa Asabe ta nufe ta da niyyar kar6o masu shi, aikuwa Jameela ta yi saurin dakatar da ita cikin haɗe rai ta ce ita ta hana ta rinƙa ba mutane shi saboda idan baƙi suka ɗauke shi sai ya yi ta kuka har kan shi yay ciwo, gaba ɗaya sai da suka ɗan buɗe ido mamakin jin furucinta,
Chapter 37 · 0% Book details