← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 197

Sashe 152

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji, cikin nasara har Salma ta kammala karatun secondary ɗinta, yanzu haka tana a Kaduna wurin auntynta Kubra tana zaman jiran result ɗin su ya fito ta ci gaba da karatu, a 6angaren aikin da take yi ma Deen, har yanzu tana yin aikin sai dai ku san aikin ya koma hannun Sageer tun da ita bata nan, a duk wata yake turo mata da albashinta, sai dai har yanzu ba wani lokacin yin magana da shi take samu ba, har yanzu idan ta tura masa saƙo wani sa'in sai an ɗauki lokaci yake dubawa ya yi mata reply, ko da ya bata number din da ya ce idan tana son magana da shi ta yi amfani da ita, sam bata wani yin amfani da layin sosai don gani take koma ta yi amfani da number ɗin to mi zata ce masa, dama dai ko saƙo zata tura masa bai wuce kan aikin da take yi masa ba sai kuma gaisuwa, hakan ya sa tafi yin amfani da layin da ta saba yin magana da shi kawai. A 6angaren Dr Hisham kuwa har yanzu suna tare, duk da har lokacin bata wani sakin jiki da shi sosai kuma bata buɗe baki ta faɗi masa tana son sa ba, amman dai tana kula shi kuma duk hidindimun da ya saba yi mata bai fasa ba sai ma abun da ya ci gaba, yanzu haka jira yake result ɗin ta ya fito ya ɗauki nauyin karatun ta. Maleek na riƙe da hannun Sapna da Basma suka fito wajen gidan, James da ke a tsaye bakin mota yana jiran Maleek ya fito ya kai sa airport ya nufo Sapna ya kar6i jakar Maleek da take riƙe da, dama tuni an fito da suitcase ɗin kayansa an saka a boot, jikin Maleek na sanye da bakaƙen suit masu kyau ya kalli Sapna da murmushi ya furta, "Sai na dawo my love." Cikin marairaice fuska ta ce, "We will miss you honey. Allah Ya tsare Ya kai ka lafiya." Ya amsa da Ameen tare da yin hugging ɗinta ya sumbaci gefe da gefen fuskarta, sakin ta ya yi ya maida kallon sa kan Basma suka haɗa ido, cikin sanyin murya da turanci ta furta, "Sai ka dawo dad, Allah Ya kai ka lafiya." Kai ya jinjina mata tare da kai hannu ya rungumo ta jikinsa, ƙasa da murya ya furta, "Take care..." Daga haka ya ɗago, Basma ta kalle shi cikin ido tana tuno da maganganun da ya yi mata jiya da daddare, daga haka ya nufi motar suna ɗaga ma juna hannu, bayan James ya buɗe masa back seat ya shiga ya zauna, shima ya zagaya 6angaren driver ya shiga, suna ta ɗaga ma juna hannu yayin da motar ta fara tafiya har suka fita daga cikin gida, Sapna ta juya ta kalli Basma, kama hannunta ta yi suka nufi komawa cikin gidan. Wuraren ƙarfe ukkun rana wata napep ta faka a gefen titi, bayan ɗan lokaci wata budurwa ta fito daga ciki, a yanayin halitta tana da matsakaicin tsawo sam ba gajera bace, sannan ba za a kira ta da siririya can ba don tana da ɗan cikan jiki, fatarta fara ce tas irin farin nan mai tafiya bai ɗaya, tana da kyawun fuska wadda take round face mai ɗauke da manyan idanu da dogon hanci tare da ƙaramin baki, daga yanayin gashin idonta da na girarta zaka fahimci tana da yalwatacciyar sumar kai, a jikinta tana sanye da doguwar riga A-shape ta atampa mai kyau, ɗaurin kallabin dake a kanta ya bayyana sumarta dake a naɗe, ta yafa gyale da ya hau da kayanta a saman kafaɗa ta rataya jaka, juyawa ta yi tana kallon ginin da aka ajiye ta a gaban shi wanda rabin katangarsa aka yi fencing mai kyau, tafiya ta fara yi a nutse ta nufi gate ɗin shiga wurin wanda shima yake mai kyau ta shige, harabar wurin na da girma sannan an ƙawata ta da rumfuna masu ɗauke da kujeru da tebura masu kyawun gaske, akwai tsarin shuke-shuke na fulawowi masu matuƙar kyau da ƙayatarwa da suka sanyaya wurin, wasu cikin flowers ɗin sun yi ma rumfunan wurin ƙawanya gwanin burgewa, rubutun da ke a saman ginin wurin ya bayyana cewa wurin shaƙatawa ne da kuma cin abinci, a saman kujerun da ke wurin akwai mutane maza da mata, wasu suna cin abubuwan ci da sha, wasu suna hira, wasu kana ganin su ka san masoya ne, daga can gefen ginin swimming pool ne da aka ƙawata wurin da rumfuna da kuma kujerun kwanciya wato sunbeds, ba ƙarya dai wurin ya ƙawatu iya ƙawatuwa, yayin da matashiyar budurwar ta shigo ciki tana tafiya a nutse, wasu daga cikin samarin dake zaune a wurin sun kasa ɗauke idanunsu akanta, har da masu yi mata magana suna mata tayin kan su, ita dai bata kula kowa ba tafiyar ta take idanunta na kallon gabanta, bayan ta kai ƙarshen hanyar da take bi ta ɗaga ido tana kallo cikin veranda din ginin in da nan ma wasu kujeru da teburan zama ne, hango wanda take nema ta yi a zaune, dama yawanci nan take yawan samun sa, lokaci guda ta ji jikinta ya yi sanyi don tare da mace ta hango sa zaune, duk da tama saba da iske shi tare da mace wani lokacin bama ɗaya ba, a sanyaye ta nufi steps ɗin hawa veranda ɗin, tana shiga suka haɗa ido da shi ta nufi inda suke tana tafiya a hankali, daga gefe ta tsaya suna kallon juna, cikin muryarta mai tattare da natsuwa ta ce, "Yaya Bash ina yini." Amsa mata ya yi, idon shi a kanta ya ce, "Ya school, daga can ma kike ko?" Kai ta ɗaga masa ta ce eh, juyawa ya yi ya kalli wadda suke zaune ya ce, "Zee meet my cousin sis Fadeela." Zee ɗin wadda kana ganinta ka san farinta na kanti ne, gashi ta yi wata shiga wadda idan ba ka santa ba ba zaka gane ita din musulma ce ko akasin haka, ta ɗan yamutsa fuska ta furta ok tare da ɗan ɗaga hannu tana bin Fadeela da wani kallo mai kaman na kishin mutum ya fika ɗin nan, "Fadeela have a seat." Bash ya faɗa yana kallonta, jim ta yi ba tare da ta zaunan ba, ganin hakan ya ce, "Ko da wani abu ne?" Idonta akan shi a hankali ta ce, "Ina son yin magana da kai ne." Shiru ya ɗan yi sai kuma ya ce ok, kallon Zee da ta wani haɗe fuska ya yi ya ce mata ta ɗan bashi lokaci yana zuwa, miƙewa ya yi tare da yi ma Fadeela alamun su je da hannu, fita suka yi daga cikin veranda ɗin suka nufi harabar wurin, a saman kujerun dake a wurin ya zauna itama Fadeela ta zauna suna fuskantar juna, "Mi kike so a kawo maki?" Tana kallon shi cikin ido ta ɗan girgiza masa kai ta ce ya basshi, shiru suka ɗan yi ta kasa tsayar da idanunta wuri guda kamar irin ta rasa ta ina zata fara masa magana, "Ina jin ki, kin ce kina son yin magana da ni." Ya faɗa tare da ɗage gira, ɗago fararen idanunta ta yi ta kalle shi, cikin sanyin murya ta ce, "Dama ba wani abu bane, kan maganan da muka yi da kai ne, ka ce zaka zo gida amman shiru baka zo ba, kuma na kira ka ka ƙara ce mani kana nan zuwa, gashi yanzu har an yi sati guda..." Bin ta ya yi da ido yana mata wani kallo, can ya ɗan kauda idon shi tare da ɗage gira ya ce, "Yanzu zuwa kika yi ki ji dalilin rashin zuwan nawa ke nan?" Kaman bazata ce komai ba sai kuma a hankali ta ce masa eh, juyowa ya yi suna kallon juna cikin ido ya ce, "Dama ba zuwan zan yi ba, kawai na faɗa maki hakan ne don ki bar ni na huta." Fadeela ta ɗan buɗa ido alamar mamakin maganar, sauke idonta ta yi na ɗan lokaci kafin ta ɗago idanunta da har sun cika da ƙwalla, cikin rawar murya ta ce, "Ya Bash mi yasa kake wulaƙanta ni? Kawai don ina son ka shine laifi na?" Tana kai maganar ƙwallan suka zubo mata sharr, hannu ta kai tana gogewa tare da juyar da fuskarta, Bash da ke kallon ta ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "In da ina wulaƙanta ki Fadeela ba zan rinƙa baki lokaci na ba ina saurarar ki ba, kuma ni ban ce son da kike mani laifi bane saboda nima ina son ki, kawai na gaji da yadda kike sa muke ta maimaita abu guda ne, koda yaushe kina nuna kina sona, amman just abu ƙarami na buƙata a wurin ki kin kasa bani, a hakan kuma kike son in yarda da kina so na, bayan idan har da gaske ana son mutum ko mi ya buƙata bashi ake." Juyowa ta yi ta kalle shi cikin raunin murya ta ce, "Amman ya Bash kai ma ka san ba zaka ce bani son ka ba, saboda kai ne ko saurarar masu cewa suna so na bana yi...abun da ka buƙata a wurina miyasa ba zaka bari mu yi aure ba, lokacin gaba ɗaya ma zan zama taka." Ɗan ta6e baki ya yi ya ce, "Miye don na buƙaci hakan yanzu a wurin wadda zan aura?" Ta ce, "Amman ya Bash ka san hakan haramun ne tun da ba auren juna muka yi ba." Yana mata wani kallo ya haɗe fuska ya ce, "Ke matsalar ki ke nan, komai ki ce zaki nuna kin fi mutum sanin daidai, a tunanin ki kema akan daidai kike? Yanzu haka a tattare da ke akwai abubuwan da ba daidai bane, kin fito da gashin kan ki, kin yafa ɗan gyale, sannan jikin ki na ƙamshi, dukkan wannan abubuwan suma haramun ne kin kuma san da hakan, amman saboda abubuwa ne da zamani ya kawo an mayar da su daidai ne. Yanzu ba wani abu bane don mutum ya buƙaci sanin wadda zai aura, wasu ma tun suna fara tarayya da juna suke sanin juna har su yi aure, ai zamani
Chapter 152 · 0% Book details