← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 197

Sashe 175

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

gani a cikin wani ɗan aljihu, fiddo katin ta yi tana dubawa, lokaci ɗaya ta saki dariya bayan ta karanta yadda za a buɗe da sauran bayanai, kallon Salma ta yi ta ce mata ashe wai akwatunan smart suitcase ne, wato masu amfani da fasaha da ake ma caji, suna da na’urar gano wuri wato GPS da kuma bluetooth, sannan suna da USB port don cajin waya ko wata na’ura yayin tafiya, suna da kuma smart lock da za a iya kullewa ko buɗewa ta app ɗin waya, akwai kuma na’ura mai auna nauyi ta nuna maka nauyin kayan cikin akwatin, sannan suna iya bin ka kai tsaye ba tare da ka ja su ba, aunty nata dariya ta ce, "Wannan ai da ya bari sai kin je London ɗin ya siya maki irin su tun da mu nan duk ƴan kauye ne." latsa wurin da ta ga an sa ta nan ake buɗewa ta yi, sai gashi tana jan zip ɗin ya zuge, aunty ta ƙara sakin dariya tana faɗin ba don Allah Ya sa mutum ya yi ilimi ba aka kawo masa wannan da ya zai yi, da sai dai wurin kokarin budewa ya yi banna ko kuma ya haƙura ya bi su da kallo....wani irin ƙamshi ne ya baɗe wurin bayan aunty ta buɗe babban ciki, jinjina kai ta hau yi bayan ta ga uban kayan da ke ciki, hannu ta kai ta fara ɗaɗɗagawa, ubansun designer kaya ne a ciki, akwai Abayu guda biyar, sai engliss dress da za su kai kala bakwai, har da scarfs masu aji kusan biyar, sannan akwai sleeping dress, kana ganin kayan ba sai an faɗa ba kasan masu tsada ne sosai, ga su unique kaya ba irin wanda zaka iya gani ko ina ba, gaba ɗaya al'ajabin kayan ne ya kama su, akwati na biyu aunty ta buɗe nan kuma ubansun designer shoes and bags ne guda biyar abun sai wanda ya gani kawai ga takalman duk heels, sai turarurruka da mayuka na jiki da kai har da na tsabtar baki, ƙaramin akwatin ƙarshe nan earings ne wato ƴan kunne na ƴan gayu da su abun hannu, zobba, da agoguna har da hankys, gaba ɗaya kayan designers ne, kallon ƙatuwan jakar da ke dauke da hoton naɗin sarautar Deen aunty ta yi kafin ta buɗe ta, nan duk su abubuwan souvenirs ne na sarautar shi, kaya ne da yawa su table calander, jotter, pen, hanky, mugs, paper bags, key holders kowanne sun kai guda biyar biyar...nannauyar ajiyar zuciya aunty ta saki tare da juyawa ta kalli Salma da tai gwale jikinta duk ya yi sanyi ganin uban kayan, aunty ta jinjina kai ta ce, "Abun na yi ne? Kin ga kaya baby, wai nan tsaraba ce...to ina ga kuma lefe!" Salma ta kasa cewa komai da ido kawai take bin komai, "Yanzu ina ganin ya kamata a kira su yaya Fiddausy a sanar masu, dama na bari ne abun sai ya kankama." Sai lokacin Salma ta tuna da maganar fitan da ya ce za su yi gobe ta faɗi ma aunty, "Ina ya ce zaku je?" Salma ta ce itama bata sani ba ya dai ce ta tambaya, aunty ta ce to bari ta dakata sai an ga abun da zai wakana goben sannan ta kira Funtua ta sanar masu, suka yi shiru suna bin kayan da ƙamshin su duk ya karaɗe wurin da kallo......
Chapter 175 · 0% Book details