Sashe 138
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
isa, zata koma ta zauna ya ce ta kawo masa lemu mai ɗan sanyi, tana kallon shi ta ce akwai wanda ta haɗa masu ɗazun bari ta kawo masa ya ɗaga kai, bin ta ya yi da kallo ya yin da ta nufi kitchen, mom ta ɗan saci kallon sa ganin yadda ya bi Leemarh da ido ta juyar da fuskarta tana ɗan murmushin tabbatar da zargin da take yi, dawowa Leemarh ta yi riƙe da tray ta ɗauro glass jug ana ganin ruwan lemun ciki da cup, bayan ta zuba a cup ta bashi ya amsa yana murmushi ya yi mata godiya, komawa ta yi inda ta tashi ta zauna ta ci gaba da yin kallon, "Yaya Fahad ya yi daɗi ko?" Binafa ta tambayi Fahad ganin yana ƙara lemun ya ɗaga mata kai kawai, "Ai daughter masha Allah ta iya abubuwa masu daɗi." Momy ta faɗa tana kallon Leemarh da murmushi, Leemarh ta kalle ta tana murmushi ba tare da ta ce komai ba,, "Ban yi tunanin ma kina yin girki ba a gida." Momy ta sake faɗa, Leemarh ta ce, "Eh ba a saka ni, kawai ni ce ke son yi shine wani lokacin nike zuwa ina koya a wurin su chef Alima." Momy ta jinjina kai ta ce, "Aikuwa hakan abu ne mai kyau sosai, don iya girki shine cikar mace, ba zaki gane amfanin hakan ba sai idan kin yi aure, don yana ƙara ma mace ƙima da daraja a wurin mijinta." Leemarh ta sunkuyar da kai tana murmushi, a hankali ta ɗaga ido ta saci kallon Fahad ta ga ita yake kallo, ya saki ɗan murmushi tare da janye idanunsa, "Yauwa yaya Leemarh ga ƴar indiyan nan da muka ce maki kuna kama." Sadeeq ya faɗa da sauri, Leemarh ta ɗaga ido tana kallon wadda yake magana a tv, momy ta ce ai da gaske suna kama sosai, Binafa ta ce, "Har gashin ku ma tsawon shi ɗaya." Leemarh na murmushi ta ce anya wannan bata fita gashi ba, hannu Binafa ta kai ta cire mata hula tare da zame ribbon ɗin data naɗe sumarta tana faɗin bari a ga wanda ya fi gashi tsakaninta da ƴar indiyan, gashin Leemarh ya baje a bayanta, duk kowa ya ce kusan tsawon gashin su ɗaya da ita, "Amman daughter bakya yin kitso ne kwata kwata?" Momy ta tambaya idanunta akan gashin Leemarh, ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Ina daɗewa ban yi ba, saboda yawan gashin ina jin wahalan zama a yi mani kitso, idan aka yi mani sai in kasa kwance shi kan lokaci, shiyasa ma ban cika son yi ba." Momy ta gyaɗa kai alamar ta fahimta, ta ce ai da yake gashin nata kamar ba mai lalacewa bane idan ana barin shi ba kitso, Leemarh ta ce eh baya komai da ta gyara shi ta saka mai shike nan, "Dama ni ke da irin gashin ki yaya Leemarh " Binafa ta faɗa tana tatta6a gashin, momy ta ce da kuwa an ga kankamba duk suka yi dariya, "Ai da wani na iya cire gashi ya ba wani da na cire na baki, don ni takura mani yake yi, inda ba laifi mutum ya yanke gashi da na yanke shi na bar shi iya shoulders ena." Leemarh ta faɗa, momy da ke murmushi ta ce, "Ah daughter ki bar gashin ki, ai shima cikar kyawun mace ne." Murmushi kawai Leemarh ta yi, momy ta ce ma Binafa tatta6a gashin ya isa hakanan ta ƙulle mata abu, duk Fahad na kallon abubuwan da ke faruwa, bayan ɗan lokaci Sadeeq ya ce, "Yaya Leemarh yau wani abinci mai dadi zaki yi mana mu ci da dare?" Kafin ta ce wani abu momy ta riga cewa, "Yau ba wanda zai wahalar da ita, idan ba zaku ci tuwo ba ku bari, sai dai idan ita ce bata son tuwon." Tura baki Binafa ta yi sai kuma ta yi saurin kallon Leemarh ta ce, "Ai yaya Leemarh kema baki son tuwon ko?" Ƴar dariya ta yi ta ce tana son shi yana mata daɗi don ba a cika yi masu shi ba mom ɗinsu bata so sai idan dad ya ce yana so ake yi, roƙon ta suka shiga yi kan ta yi masu wani abun kamar yadda take masu duk dare ta haɗa masu wani abu mai daɗi saboda basu son cin tuwo, tambayar su ta yi akwai dankalin turawa ta ga kaman jiya ya kusa ƙarewa, da sauri Binafa ta ce ai an kawo ɗazun, ta ce to bari ta yi masu Sultan Chips, miƙewa suka yi tare da Binafa za su wuce kitchen, momy ta kalli Sadeeq ta ce shima ya bi su a yi wahalan da shi tun da sun hana ta ta yi kallonta, har Leemarh ta wuce sai kuma ta nufi wurin Fahad ta ce, "Zaka ci kai ma in yi da kai?" Ya bita da kallo kaman ba zai ce komai ba sai kuma ya ɗan ɗaga mata kai alamar eh, ta yi murmushi ta ce ok, mom dai ta kauda idonta, ba da jimawa ba aka fara kiran sallan magrib momy ta miƙe ta nufi part ɗinta shima Fahad ya fita zuwa masallaci. Bayan sallan issha Leemarh ta shigo cikin falon Fahad tana riƙe da madaidaicin tray, Fahad na zaune a saman doguwar kujera ya miƙe kafafunsa yana yin kallo ya juya yana kallon ta har ta ƙaraso, sauke ƙafafunsa ya yi ta daura tray ɗin a saman kujeran tana faɗin bari ta matso da table, tambayarta ya yi ita ta ci ne ta ce a'a tare ta zubo masu, nuna mata ɗayan side ɗin kujeran ya yi ya ce su ci a nan, zama ta yi ta yadda sun saka tray ɗin a tsakiya, buɗe plate da ta rufo abun ta yi nan da nan ƙamshin shi mai daɗi ya karaɗe wurin, a ido ma ya yi mashi kyau sosai, miƙa masa fork ta yi ya amsa suka fara ci a natse, lokaci bayan lokaci suke ɗaga ido su kalli juna cikin ido tare da sakar ma juna murmushi, bayan sun yi nisa cikin cin abincin ta ga ya dakata tare da ajiye fork ɗin ta ɗaga ido ta kalle sa, calmly ya ce "Why kike son ki yanke gashin ki?" Ɗan buɗa ido ta yi alamar mamakin ashe ya ji maganan ɗazun, da sigar shagwa6a ta ce, "Gashin ne ke takura mani gashi ina jin wahalan zaman kitso saboda yawan shi." Shiru ya yi yana ta kallonta, ta ɗaga mashi gira ta ce, "Ko baka son in rage ɗin?" Ɗan murmushi ta ga ya yi slowly ya ɗaga mata kai, sai kuma ya ce yana ƙara mata kyau, tana murmushi ta ce to bazata yanken ba ai dama babu kyau, "Zan koya yadda ake kitson sai in rinƙa yi maki idan kina so." Ta ɗan wara ido alamar mamaki, ba ta yi zaton zai iya furta mata maganar ba, ɗage gira ya yi ya ce ko bata so, tana murmushi ta ce tana so, sai kuma ta ce, "Yaushe zaka rinƙa yi mani tunda da hutu ya ƙare zan tafi." Ya yi shiru kaman ba zai ce komai ba yana ta kallonta, itama idanunta na a cikin nashi, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Bada jimawa ba zamu kasance tare." Shiru suka yi suna ta kallon juna cikin ido, kasa jure ma kallon Leemarh ta yi ta sunkuyar da kai zuciyarta na bugawa da sauri, ji take kamar ta furta masa kalmar da ta maƙale mata a baki, gani ta yi ya kawo fork din chips bakinta, ta ɗaga ido ta kalle shi kafin slowly ta buɗe baki ya saka mata......Aunty Kubra ta turo kofar bedroom ɗin ta shigo, dama bayan Sageer ya tafi Salma ta koma tana amfani da shi duk da tare suke kwana da aunty Kubra a ɗakinta, Salma dake zaune a bakin gado tana latsa wayarta ta juya tana kallonta da murmushi, ɗan zamanta a nan har wani fresh ta kara yi, tsayawa aunty Kubra ta yi gefenta jikinta sanye da fararen kayan aiki ta ɗaura baƙar after dress sai ƴar ƙaramar farar hijab, hannunta guda tana riƙe da ƴar babbar baƙar jaka, "Baby kin shirya?" Salma ta ɗaga mata kai alamar eh, sai kuma ta ɗan langa6ar da kai ta ce, "Aunty Allah zan iya kwana ki tafi." Wani kallo ta yi mata ta ce, "Ta ya zan bar ki ke kaɗai ki kwana a gida." Salma ta ce, "To ai ga su maman Esther a ɗayan block ko." Aunty ta ce, "Wannan da bata dawowa daga shago sai cikin dare, ni dai taso mu tafi ai ba yau na fara zuwa dake aikin ba." Dariya Salma ta yi tunowa da can baya lokacin da tana wurin ta wani lokacin idan tana aikin dare sai dai ta tafi da ita, ɗaukar gyalenta da ke ajiye gefe saman gadon ta yi ta sauko tare da yafawa a saman dogowar rigar jikinta, bayan sun fito cikin falo aunty Kubra ta nuna mata wani food carrier dake ajiye saman carpet ta ce ta ɗauko daga haka suka nufi ƙofa suka fita...