← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 197

Sashe 33

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin suna karatu jami'a ɗaya da Soffy yasa ta koma tana tarewa a gidan su, ta ci abinci ta yi wanka har aron kayan Sophia ɗin take waɗanda za su yi mata don ta fita garin jiki, duk da yawanci ma in ta arar mata kaya cewa take ta bassu, da yake mahaifiyar su Sophia din mutuniyar kirki ce sam bata da matsala hakan yasa Jamila ke cin karanta babu babbaka a gidan, saidai mahaifin Sophia ɗin bai cika son yana ganinta a gidan shi ba, har ƙawancen da take da ƴar shi baya so saboda duk an san yaran gidan su basu da tarbiyya, akwai lokacin da har magana ya yi ma mom din Sophia, kan baya son ƙawancen da take da ƴar shi bai son ta gur6a ta mata tarbiyya, lokacin mom din Sophia ta nuna mashi cewa raba su lokaci guda abu ne mai wuya tun da tare suka taso, kuma za a iya raba su su zagaye su koma a tare ta bayan fage, kuma hakan na iya haifar da abun da ake gudu, ta nuna mashi gara a ƙyale su su ci gaba yadda suke ana saka ido ana sanin wane hali suke ciki. Lokacin ya ɗauki shawararta, saidai ita kanta Jameela ta fahimci baya son zuwa gidan shi da take don duk ta zo ta iske shi ta gaishe shi haka yake amsa mata ba yabo ba fallasa, hakan ya sa sam bata sakewa yadda ta saba in har yana a gida, da yake kuma mahaifin Sophia bai cika zama ba yana yawan fita ƙasashen waje harkar kasuwancin shi, har da wannan ke bata dama take sakata ta wataya son ranta, har wasu cikin samarinta yaran masu kuɗi nan take kawo su a zuwan nan gidan ƴan'uwanta ne anan take zaune, da yake kuma maigadin gidan Garbati mayen son kuɗi ne, kuma shima dai ba wani na kirki bane sosai hakan yasa yake bata goyon bayan da take so ba kamar da tana bashi kuɗi masu yawa, wani lokacin da taimakon mai gadin wasu cikin samarinta har shiga take da su cikin gidan su zauna a cikin rumfunan shaƙatarwar dake a can gefe guda ba tare da sanin masu gidan ba har su yi zancen su su gama.

Akwai wata rana da tana cikin yin zancen a gidan mahaifin Sophia ya ritsa da ita, ranshi ya 6aci sosai ganin har zance take mashi a gida, inda ta ci sa'a a ranar bai yi mata magana ba a gaban saurayin, sai da ya shiga ciki ya balbale mom ɗin Sophia da faɗa duk da ta nuna mashi bata da masaniya akan hakan amman bai yarda ba, shima mai gadin sai da ya sha faɗa sosai ya yi ta ba Alhajin haƙuri, yana cewa ya ga an bata dama tana zuwa gidan sosai shiyasa bai hana ta shigowa da samari ba a zaton shi Hajiya ta sani, lokacin alhajin ya gargaɗe shi akan kada ya sake bari ta shigo mashi da wani a gida in ba haka ba zai ja ma aikin shi, ya ƙara da cewa ko ɗiyar shi ya hana ta kula samari saboda karatu yake son ta yi akan me wata zata riƙa shigo mashi da ƙattakai cikin gida, jin hakan yasa Garbati mai gadi ya ce ma Jameela ta yi haƙuri ba zai ci gaba da barinta tana kawo samarinta ba kamar yadda suka saba ya faɗa mata yadda suka yi da Alhaji, sam a lokacin bata ji haushin alhajin ba don ta san gaskiya ya faɗa, ɗiyar shi Sophia ba ta kawo samarinta gidan duk da tana da su saidai su yi waya ko su haɗu a wasu wuraren.

Akwai wata rana bayan Alhaji Mahmud ya dawo daga tafiyar da ya yi ya É—an kwana biyu baya nan, lokacin ya je masallacin dake a jikin gidan shi, bayan gama yin sallar ne suka gaggaisa da mutane da yake shi É—in mutumin kirki ne da ya san hakkin makwabtaka, yana da taimakon mutane sosai musamman waÉ—anda basu da shi ko aka zo neman taimako wurin shi, bayan sun gaisa da limamin masallacin ne ya ce mashi in ba damuwa yana son za su É—an tattauna wani batu mai muhimmanci, jin hakan yasa Alhaji Mahmud fasa tafiya ya zauna tare da tattara hankalinsa akan liman, a nutse ya fara yi mashi magana,

"Wato Alhaji Mahmud dama magana nike son yi maka game da wani abu da ke faruwa, ina hango cewa idan aka yi sake al'amarin na iya haifar da gagarumar matsalar da ba a fata, hakan ya sa na yanke shawarar tunkararka da maganar a matsayin gyara kayan ka. Kuma ganin ana zama na amana da juna bai kamata a ce in an hango wani abu da ka iya zamewa matsala ba ai shiru ko don a fita hakkin juna...Dama game da Æ´ar wajenka ne Safiyya da kuma yarinyar gidan Abdullah Buzu..." Wani irin faÉ—uwa gaban Alhaji Mahmud ya yi jin abun da liman ya ce, dama sam hankalinshi bai kwanta da tarayyar su biyun ba, gyara zama ya yi sosai ya ce ma Liman wace matsala ce ya gani don Allah Ya faÉ—a masa kuma kada ya ji nauyin faÉ—a masa komai,

"Su ƴa'ƴa da Allah Ya bamu Amana ne a gare mu Alhaji Mahmud, kuma tabbas Allah zai tambaye mu akan yadda muka kula da wannan amanar, a matsayin mu na iyaye ya kamata muna kula sosai akan al'amuran yaranmu, mu kasance muna masu basu kariya daga dukkan wani mummunan abu da muka hango yana tunkaro su...Duk mun san irin halayen yaran dake a unguwar nan, ba zancen ganin ido ba Alhaji kowa ya san yarinyarka Safiyya tana da kyawawan halaye, kun yi ƙoƙari matsayin ku na iyayenta wurin ganin kun bata tarbiyya duk da kasancewarka ba mazauni ba, sai aka ci sa'a da mahaifiyarta ma jajirtatta ce wurin hakan...Ba sai na fito fili na bayyana maka irin halayen yaran Abdallah buzu ba don hakan a bayyane yake, kuma kai zaka ma fi mu sanin halayyar su tun da kusan a unguwar nan sun fi shiga gidan ka akan na kowa tun lokacin da mahaifin su yana aiki a ƙarƙashin ka..."

A nutse cikin kwantar da murya ya shiga nusar da Alhaji illar da yake hangowa a ƙawancen Safiyya da kuma Jameela, ya kuma nuna mashi irin ƙarfin tasirin da abokai suke yi wajen canza halayyar junan su wanda ko iyaye basu cika yin wannan tasirin ba, ya haɗa da kawo mashi hadisai dake magana kan abokantaka da irin mutanen da ya kamata a yi abota da su. Hankalin Alhaji Mahmud ya ƙara tashi, har zuciyar shi ta fara saƙa mashi tunanin kodai wani mummunan abu ya faru da bashi nan an 6oye mashi, kasa haƙura ya yi sai da ya yi ma malam Liman tambaya kan hakan, ya roƙe shi akan don Allah Ya sanar mashi in dai da abun da ya san ya faru da bashi nan, Liman ya tabbatar mashi da ba wani mummunan abu da shi dai ya ji ya faru, sai dai hango hakan na iya faruwan ne ya sa ya yanke yi mashi magana kamar yadda ya faɗa tun farko.

"Nagode sosai malam Liman, haƙiƙa kai masoyi nane na gaskiya da har ka hango illa da ka iya shafar ahalina ka sanar mani don daukar matakin guje ma faruwar hakan, haƙiƙa nima tun ba yanzu ba hankalina sam bai kwanta da tarayyar su ba, na so in raba su tuni, to sai mahaifiyar yarinyar ta nuna gara a ƙyale su ana saka masu ido akan a raba su, don suna iya zagayewa su koma tare ba tare da sanin mu ba, to wannan shawarar tata ita na ɗauka ya sa ka ga na ƙyale su amma ba wai don hankalina ya kwanta da hakan ba." Alhaji Mahmud ya yi bayanin da damuwa shimfiɗe akan fuskarsa,

"Ba wani abu Alhaji, ai duk yi ma kai ne, kuma fita hakkin juna ne a matsayin mu na maƙwabta. Sannan dama mu malamai a koda yaushe aikin mu ne idan mun hango wata matsala in muna da ikon gyara ta sai mu yi hakan, idan kuma bamu da wannan ikon sai mu tuntu6i wanda ke da ikon gyarawar don a ya gyara, idan ya ɗauka Alhamdulillah hakan muke so, idan kuma akasin hakan to mu dai mun yi aikin mu. Shi kan shi Abdullah Buzun na yi mashi nasiha ba sau ɗaya ba akan halayen yaran shi amman sam baya dauka, ƙarshe ma sai gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da zuwa wannan masallacin, wannan dalilin ne ya sa nima na rabu da shi, duk da mutane na yawan zuwa mani da ƙorafin yaran shi, to saidai in faɗi masu cewa na yi abun da zan iya sai dai kawai mu yi masu addu'a Allah Ubangiji Ya shirya su da zuri'ar mu baki ɗaya." Amsawa Alhaji ya yi da Amin, ya ƙara da cewa shima ya sha yi mashi magana akan hakan sai ya nuna kamar ya ɗauka, ƙarshe da ya fahimci ba ɗaukar shawara ko nasihar yake ba sai ya tattara ya rabu da shi.
Chapter 33 · 0% Book details