← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 197

Sashe 103

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari tun safe aka ci gaba da yin gasar da su Deen ke yi wadda ta kai har zuwa yammacin ranar, ƙarshe dai waɗanda suka haɗa gasar sune suka lashe kofin wato babban club ɗin da Deen ya buga mawa, ba wanda kuma ya ja da hakan don Deen sam bai sarara ma abokan karawar sa ba, dama kowa ya riga ya saka a ransa club ɗin su Deen ne zai yi nasara saboda kasancewar sa a cikin su, an bayar da lambobin yabo ga ƴan wasan da suka yi nasara da kuma sauran clubs da suka yi na biyu da na ukku, ban da wannan Deen ya karɓi babbar lambar yabo ta Player of the Tournament, bayan da ya kuma zama Man of the Match a wasan ƙarshe. Baya ga manyan lambobin yabo da ya samu a tournament ɗin, wasu daga cikin kamfanonin da suka ɗauki nauyin gasar sun karrama shi da lambobin yabo na musamman, suna yabon girmamawarsa, tasirinsa da ƙwarewarsa, tare da kuɗaɗe da kayayyaki masu tsoka, har da gwamnan jihar wanda ya kalli wasan ƙarshe kuma ya karrama wasu da suka yi nasara shima ya yi ma Deen karramawar sa. Bayan jawabin godiya daga Deen anan take ya sadaukar da kudaden da aka bashi ga team ɗin guragu da ke buga ƙwallon ƙafa, ya nuna yabawarsa a gare su kan yadda nakasar su bata saka sun kasance cikin ƙunci ko kuma za6ar su rinƙa yin bara a tituna, wannan tallafi da Deen ya bayar ba ƙaramin daɗi ya yi ma mutane ba da ƙara masa farinjini, a nan wasu manyan kamfanoni suka gabatar masa da tayin hulɗa daban-daban da suka haɗa da tayin zama jakadan kamfani wato Brand Ambassador offers, Sponsorship and Partnership offer da sauransu, in da ya nuna zai duba wasu. Bayan komawar sa hotel shiryawa ya yi cikin shiga ta musamman don kai ziyara babban asibitin gwamnatin garin tare da rakiyar jami'ai da wasu football officials da manyan ƴan kwallon jahar, da suka je asibitin kamar yadda ya ba marasa lafiya tallafi a Funtua haka nan ma ya ba marasa lafiya tallafin kuɗaɗe da biya ma wasu kuɗin aiki. Bayan sun gama daga nan gidan ƙanwar mahaifinsa aunty Murja ya wuce don gobe zai koma Abuja ita kuma tana zuwa aiki malamar jami'a ce bata nan da safe, daga shi sai jami'an da ke tare da shi suka je gidan dake a Nasarawa G.R.A, bayan motocinsu sun faka a cikin harabar gidan wanda yake babban flat ne mai kyau, aunty Murja da maigidanta tare da yaran su ukku da ke dakon zuwan shi bayan da ya kira ya sanar mata, suka tarbi Deen cikin nuna farin cikin ganin sa, shima murmushi ne akan fuskarsa ya gaishe da su, ɗan side hug aunty Murja ta yi masa kana ganinta zaka ga kamanin hajiyar ambasada akan fuskarta, "You are highly welcome tauraron ɗana." Ta faɗa bayan ta sake shi, mijinta Dr Mustapha shima ya yi mashi sannu da zuwa, "You are welcome yaya Deen." Babbar ɗiyarta mai suna Fateema da ake ce ma Zarah ta faɗa tana murmushi idanunta sanye cikin glass, a yanayin shekaru zata yi shekaru ashirin da ɗoriya, ta biyun mai suna Nabeela da ba zata wuce shekara sha takwas zuwa sha tara ba tana sanye da abaya itama ta yi mashi sannu da zuwa tana murmushi, sai na ukkun wanda shine auta wato Nabeel shima a shekaru zai yi shekara sha biyar yana sanye da ƙananun kaya riga da wando, ya nufi Deen da murmushi ya faɗa jikinsa yana mashi sannu da zuwa Deen ya rungume shi, gaba ɗaya iyayen kana ganin su ka ga wayayyun ƴan boko, haka yaran nasu ma jikin su ya nuna hutu, kana ganin su ka ga ƴan gayu tun daga kan yadda suke magana, sannan ba laifi suna da kyau sam ba munana bane, Zarah doguwa ce sannan bata da jiki, a yanayin fatar ta tana da ɗan haske ba sosai ba, sai Nabeela ita ta ɗan fi Zarah jiki sannan bata kai haskenta ba, Nabeel kuma sam ba shi da jiki don duk ya fi so sirantaka sai dai kuma shi kana ganinsa fari ne, bayan sun gama welcoming na shi Dr ya ce su shiga ciki. A babban falon gidan da ya sha lafiyayyun leather chairs tsaf da shi suka zauna aka shiga sake yi ma shi sannu da zuwa, miƙewa Zarah ta yi ta nufi ciki bada jimawa ba ta dawo hannuwanta riƙe da tray a sama lemu ne da cup, a saman center table ta ajiye a gaban Deen tana murmushi, bayan ta zuba masa ta ce mashi gashi ya ɗaga mata kai tare da yi mata godiya, "Deen ya ka baro mom da dad din ka, mun yi ma waya da shi ɗazun da safe." Aunty Murja ta fada, a nutse ya bata amsa da suna lafiya suna gaishe da su, ta jinjina kai tana murmushi kafin ta kara cewa, "Ya can ƙasar taku da kuma iyayen ka na can." Ya amsa mata da suna lafiya, "Deen ya ball?" Dr ya tambaya shima da murmushi, ya amsa masa da Alhamdulillah, Dr ya ce, "Ma sha Allah, ai duk muna kallon wasan ku, kuna kokari sosai, Allah Ya ƙara taimakawa Ya tsare, Ya ƙara ɗaukaka." Gaba ɗaya suka amsa da Ameen, "Ya Deen jiya da kuka fara tournament a stadiun mun je kallo ni da wani friend ɗina, na so in yi magana da kai amman ba a gama ba muka taho saboda dare ya yi, ɗazun da yamma da aka gama muna wurin ban samu damar da zan yi maka magana ba." Nabeel ya faɗa da muryarsa mai tattare da yanayin sangarta, murmushi kawai Deen ya yi masa, aunty Murja ta ce ai suma duk sun kalla a Tv tare da yaba masa kan tallafin da ya bayar har a Funtua ta yi masa addu'oi, shima Dr ya yaba sosai tare da yin nasa addu'oin, "Zarah kin kawo lemu saura ki shirya ma yayan naki abinci a table, ko a kawo maka nan son?" Aunty Murja ta tambayi Deen, ya ce mata ya ci abinci baya jin yunwa, "Amman ka san ba zan barka ka zo ka tafi baka ci abinci ba, yaushe rabon ka da gidan nan, it's been a long time sai kuma ka ce ba zaka ci abincin zumunci ba, ka dai ci ko ɗan yaya." Murmushi kawai ya yi, Zarah da ta miƙe tana kallon sa tana murmushi ta ce ta shirya masa a table ɗin ko ta kawo nan, kallon ta ya yi ya ce duk yadda ta yi ta amsa da ok, zata wuce cikin zolaya ya ce ta bi a hankali kada ta zubar da abincin don ya ga ta zama makauniya, dakatawa ta yi ta ɗan rausayar da kai tare da ɗan tura baki ta ce, "Kai ya Deen, a ina ka ga na makance don na saka medical glasses ai ina gani." Duk suka yi ƴar dariya shima Deen murmushi ne akan fuskarsa, wucewa ta yi tana faɗin in da ita makauniya ce ai da baƙin glass zai ganta, hira aunty Murja ta shiga yi masa bayan Zarah ta dawo ta sanar masa ga abincin can ta kai masa bata zubar ba, ya yi ɗan faffaɗan murmushi tare da yi mata godiya, tambayar game da karatun su ya yi Zarah ta ce masa tana a level 2 zata je 3 tana karantar medicine a jami'ar da mom ɗinta ke koyawa wato BUK, Nabeela ta ce ita tana a level 1 itama zata je 2 tana karantar English Language itama a nan jami'ar, Deen dake fuskantar su yana sauraron su ya ce ita mi yasa bata ɗauki medicine ba ko don bata son ta sha wahala, tana dariya ta ce ai shima English ɗin yana da wahala Allah, gyara zama Nabeel ya yi da aka zo kansa ya ce shi yanzu yana a aji huɗu na secondary wato s.s one zai je two, idan ya gama school of aviation zai tafi don pilot yake son zama wato matuƙin jirgi, Nabeela na dariya ta ce, "A haka zaka zama pilot ɗin, cikin kai da jirgin waye zai ja wani." Ya jefa mata harara tare da cewa an faɗa mata abun a jiki yake." Deen da ke murmushi ya ce ai idan ya ƙara girma zai ƙara jiki, a hasale Nabeel ya ce, "Kyale ta yaya Deen, sauƙin abun dai ni ba acici bane, yaya Deen ka ganta nan rumbu ce, duk ita ke cinye abincin gidan nan, har namu idan muka rage duk wawushewa take." Dariya Nabeela ke yi ta ce, "Lafiya gare ni shi ya sa, kuma ba gashi da bambanci a tsakanin mu ba abincin na mani aiki, wani ma yana ci amman kaman baya ci." Dariya suka sa Deen har fararen haƙoran sa suka ɗan bayyana, suma iyayen nasu dariyar suke, aunty Murja ta ce, "Son ka ƙyale wannan biyun haka suke kullum faɗa kaman kaji, ka je ka ci abincin ka." Yana murmushi ya ce mata haka Leemarh da Omar suke duk suka zauna tare, "Haka ne dama yawanci zaka ga tsakanin sako da sako ba su cika jituwa ba. Allah Sarki my daughter Leemarh an daɗe bamu haɗu ba sai ta phone, dama ita ce take ɗan zuwan mana lokaci bayan lokaci idan ta zo hutu nan." Miƙewa Zarah ta yi ta ce su je ta yi serving na shi, bayan ya miƙe suka nufi hanyar dining area ɗin yana tafiyar shi mai tattare da natsuwa, duk idanun mutanen falon na akan shi Nabeela sai ɗan murmushi take yi ta kasa janye idonta akan shi, miƙewa Nabeel ya yi mom din su ta tambayi ina zai je ya ce zai taya yaya Deen hira, wani kallo ta yi masa ta ce, "Dama idan ana cin abinci ana hira ne? Za ka je dai ka takura masa, koma ka zauna ka jira ya gama." Hararar Nabeela dake masa dariya har da ɗan gwalo ya yi kafin ya koma ya zauna, bayan Zarah ta yi serving na shi abincin zama ta yi a kan ɗaya daga cikin kujerun ya yin da ya fara ci a nutse, jefi jefi suke ɗan yin magana da juna, kallonta ya yi ya ce
Chapter 103 · 0% Book details