← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 197

Sashe 16

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai dama baka wahalar da bakinka ba Imrana, ko ka faɗa ba yarda zai yi ba, ka san shi da gardamar tsiya kaman makahon jaki, in banda sharri ko yaushe ake yin sati ana yin tuwo...." Salma da ta ɗauko maganar bata ƙarasa ba Sagir dake niyyar zama a gefen Auwalu ya aje kular tuwon hannunsa ya yo kukan kura kanta, yana zuwa ya tangare mata ƙeya da ƙarfi har saida hular kanta ta cire, tufkar kitson shaden dake kanta ta baje har gadon bayanta, a fusace ya ce mata uban waye makahon jakin! Da sauri ta janye jikinta gefe tare da kare kanta tana dariya ta ce, "To ai dai bani na fara faɗan haka ba ko, innarmu ce ke cewa ka cika gardama kamar maka...." Kanta ya yo yana fadin, "Wllh kika ƙara faɗar maganar nan sai na fasa maki baki!" Innarsu dake dariya ta ce mashi kada ya sake ya ƙara ta6a ta, rai a bace ya ce to ta ce ma Salmar kada ta ƙara ce mashi haka in ba haka ba sai ya gota ta Allah, kallon Salma ta yi ta ce mata kada ta kara faɗin haka ta gyaɗa kai tana ta dariya, ƙwafa Sagir ɗin ya yi ya koma inda ya ajiye tuwon ya zauna ya fara ci, ganin yadda yake ta buga loma Salma dake kallon shi cike da tsokana ta ce, "Ah, man Sagir ya na ga kana ta buga loma kuma, ai na yi zaton tun da ran ka bai son tuwon zaka ɗan tsakura ne kawai don dole..." Ganin yana laluben takalmi yasa ta yi shiru ta 6oye a gefen innarsu tana ƙyalƙyata dariya, cikin ɗan ɗaga murya innarsu ta ce mashi kada ya jefo masu takalmi cikin abinci, fasa ɗaukar takalmin ya yi ya ci gaba da cin tuwon yana yi yana leƙo abun da Auwalu ke kallo a wayarsa.

"Yau mutumina Habu bai leƙo ba da daddare." Salma ta faɗa tana ci gaba da cin tuwon,

"Ai gara ma da bai zo ba, ni wllh bani son yana zuwa, kullum bai tashi zuwa sai lokacin da muke cin abinci kamar ya san lokacin da ake gama mana abinci, kuma duk in ya zo innarmu sai ta bashi abincin, wani lokacin ma in babu sai ta kwashe cikin namu ta bashi." Imrana ne ya yi maganar yana tura baki, da ɗan murmushi innar tasu ta ce, "Ai yanzu ma in ya shigo babu tuwon, cikin naku zan ɗebar mashi..." Da sauri ya ce, "Kam, Allah ni dai ba za a ɗibar mashi ba, in kuma mu bamu ƙoshi ba fa, saidai yaya Salma ta bashi dama ita ta saba haƙura da abincinta in ya shigo babu ta bashi har ta ce ya je su ci shi da ƙannanshi..."

"Munahukar ba, tana nuna kamar ita ta Allah ce mai tausayi, dama tun da wurin soya awara tana samu ta ci ta ƙoshi ta kuma zame wasu cikin cinikin ta siya abun da take so ba dole ta rinƙa yin neman suna da abincinta ba." Sagir da ya maido da hankalinsa akan su ya faɗa yana ci gaba da cin tuwon gaban sa.

"Kai Sagir! Banda sharri, ba wata awara da Salma ke ci, kuma koda ta ci sai ta sanar mani, sannan ko ta nawa na saka mata haka zata kawo mani kuÉ—ina daidai ba tare da ta É—auki ko naira biyar ba sai in ni ce na bata. Ita haka Allah ya yi ta da tausayi abun ta bai dame ta ba, kuma hakan abu ne mai kyau don duk abun da ka bada shine naka, idan kana badawa sai Allah Ya yi ta buÉ—a maka shi yasa itama bata rasawa, ko ban bata kuÉ—i ba bata rasa Æ´an kuÉ—aÉ—enta da zata siya abun da ranta ke so cikin wanda Auntynta Kubra ke turo mata." Murmushi kawai Salma ke yi jin abun da innarsu ke faÉ—a game da ita, mita Sagir É—in ya ci gaba da yi yana faÉ—in dama bata ganin laifinta shiyasa zata ce haka amman shi ya san tana cinye mata awara kuma tana zarar kuÉ—i cikin ciniki.

"Bara Ubannan...!" Bayan É—an lokaci Suka ji Sagir É—in ya furta tare da Æ´ar zabura idon shi akan wayar Auwalu,

"SubhanAllahi! Sagir wane irin furuci ne haka? Mi ya faru?" Ɗan girgiza mata kai ya yi yana washe baki ba tare da ya kalle ta ba ya ce mata ba komai, a ƙagauce ya ce ma Auwalu, "Wai mutumin har ya iso ke nan?" Kai Auwalu ya ɗaga masa alamar eh, a ɗokance Sagir ɗin ya ci gaba, "Wllh ni ban san ya iso ba, nasan dai da maganar zai zo Najeriya, da yake tun jiya ban hau online ba banda data, ɗazun kuma ban samu zuwa fili da wuri ba kuma match zamu buga ina zuwa muka fara dama ni ake jira shiyasa na san ban ji zancen zuwan nashi ba." Yadda yake maganar kana gani zaka fahimci ba ƙaramin dadin zuwan wanda yake magana akai ya ji ba,

"Waye kuke magana akai ne?" Innarsu ta tambaya, da sauri Sagir ya bata amsa da, "Tauraron ɗan ƙwallon mu na ƙasar waje Nuree Jr." Bin shi ta yi da ido ta ce shine yake ta wannan rawar jikin?

"Ba zaki gane bane innarmu, ina mugun yin shine wllh, bama ni kaÉ—ai ba, yanzu a duniyar kwallo yana É—aya daga cikin taurarin dake lokaci, mutanen da basu haÉ—a komai ma da shi ba sun mutu akan shi balle kuma ni..." Da yanayin mamaki Salma ta ce, "To kai É—in ma wani abun ka haÉ—a da shi ne?"

"Ah! Ka ji yarinyar nan, ai kuwa na haɗa wani abu da shi tun da ɗan ƙasata ne ƙarewa garinmu ne tushen shi, uwa uba kuma gidansu a unguwarmu yake."

"Wai ba jikan Hajiyar Ambasada É—an kwallon nan kake magana ba?" Innarsu ce ta tambaya, ya bata amsa da shi fa.

"Ma sha Allah, ka ce dai shima ya ɗaukaka..." Auwalu ne ya ɗago ya bata amsa, "Daukaka sosai ma, don yanzu dai a duniyar ƙwallo yana ɗaya daga cikin waɗanda ake ji da su ake kuma maganar su saboda ya iya ta sosai.."

Sagir ya yi saurin kar6ewa, "Ai tukunna ma dai, ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba Nuree Jr nan gaba ba ƙaramar shahara zai yi ba sai ya samu title din GOAT in sha Allah. A yanzu ma da ba wasu shekaru sosai ya ɗauka a duniyar kwallon ba ya fara breaking records, ko gasar Champions league da ba a daɗe da gamawa ba team din su ne suka ƙara ci, kuma shi ya ƙara samun kyautar Golden boot wato kyautar ɗan kwallon da ya fi zura kwallo a raga, kuma ba wannan ne na farko ba dama ya taba samu ban da wanda ya samu a gasar premier league, haka bayan kammala kakar wasannin bara ya samu Ballon d'or nomination, duk da bai samu kyautar ba, amman in sha Allahu muna saka ran zai samu bada daɗewa ba in dai ba an saka son kai ba kasancewarsa ɗan Africa ...." Haka ya ci gaba da faɗi ma innar tasu nasarorin da Nureen ya samu daban-daban, gaba ɗaya ma ya dakata da cin tuwon, ita dai Salma tana ta cin tuwon ta don abun da suke magana a kai ba damunta ya yi ba hasalima in suna hirar ƙwallon a gidan wani lokacin a ɗakin su na soro su da abokansu yadda suke hargowa da waƙe- waƙe haushi suke bata ta ji kamar ta je ta hau su da bugu.

"Allah Ubangiji Ya ƙara ɗaukaka shi Ya kare shi. Ni da yake ba sanin ta kan kwallon na yi ba ban san haka ya shahara ba, kawai dai na san ana faɗin ya iya ta sosai ba kamar lokacin da ya ci ma Nigeria wata ƙwallo bansan dai ko wacce ba ce akai ta maganar shi..." Innarsu ta faɗa bayan Sagir ya gama bata labarin.

"AFCON kike magana, wannan gasar zakarun nahiyar Africa ce da ake yi duk bayan shekara biyu, itace ya taba ci ma Nigeria, sai kuma gasar cin kofin duniya FIFA World cup, itama ya ta6a buga ma Nigeria sau ɗaya duk da basu yi nasara ba amman sun yi ƙokari sosai don sai da suka kai har quaterfinals wato mataki na biyun ƙarshe..." Auwalu bai kai ƙarshen maganar ba Sagir ya kar6e, "Ai duk kokarin da suka yi a lokacin shine ya yi shi, to lokacin ma bai kai gogewar da ya yi yanzu ba, nasan yadda ya ƙara ƙwarewa muna da hope din in sha Allahu a gasar cin kofin duniya da ke zuwa nan da shekara ɗaya zai ci ma Nigeria bi'iznillAh...Ai Nuree ɗan baiwa ne a ƙwallo, nima ina fatan wata rana in zama kamar sa, koma ban kai shi ba nima dai ina roƙon Allah Ya sa in zama shahararran ɗan kwallon kafa.." Innarsu na murmushi ta amsa mashi da Amin Ya Allah in hakan alkhairi ne a gare shi, Auwalu ma ya amsa da Amin kafin ya ɗaura da fadin, "Shi Nuraddeen harda farinjini da Allah Ya yi masa, yana da kyau na fuska da jiki ma sha Allah, bana tunanin akwai ɗan ƙwallon da ya kai shi kyau sai dai ko a samu mai irin ƙirar jikinshi amman dai kyawun fuska gaskiya da ƙyar ne."
Chapter 16 · 0% Book details