← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 197

Sashe 36

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A 6angaren amarya da ango suna ta shan soyayyar su, saidai tun ba a je ko'ina ba hajiya ta fara fahimtar wasu daga cikin halayen Jameela, ƙiri-ƙiri take nuna bata son dangin su dake zuwa a fakaice take yi masu wulaƙanci da kora da hali, farkon kawo ta sosai take ma Hajiya biyayya kullum sai ta je ta gaishe da ita ta tambayi ko akwai abun da za ta yi mata, ko da hajiyar ta ce mata babu komai sai ta je kicin ta taya mai aikinta wani abun, a hankali ta fara janye ƙafa sai ta gadama sannan ta je ta gaishe da ita, sanin tana zuwa ya sa idan Hajiya ta ga an kwana an wuni bata je ba sai ta tambayi Ibrahim ko lafiya idan shi ya je gaishe da ita, wani lokacin har ƙarya yake mata ya ce Jameelar ce bata jin daɗi, daga baya hajiya ta fahimci hakanan ganin dama ne ya sa bata zuwa gaishe ta kaman yadda ta saba sai itama ta fita batun ta, iyaka idan Ibrahim ɗin ya je ta tambaye shi suna lafiya. Sai da ta kai har sai ya matsa ma Jameelar sannan wani lokacin zata je gaishe da hajiyan. Watan su biyu da yin aure ta samu juna biyu, a lokacin sai abun da ya ci gaba na iskancin ta, farko ma bata yi murna da cikin ba wai ita ba yanzu take son samun ciki ba gaskiya karatu take son ci gaba da yi, lalla6a ta ya yi ya rarrashe ta kan ta yi haƙuri ta haifi wannan daga shi sai su bari bayan ta kammala karatun sai ta sake haihuwan. Ba ƙaramin wahalar da shi take ba da buƙatun cikin, gaba ɗaya ta daina yin girki dama ba wani cika yi take ba sai ta gadama don ana kawo masu daga part ɗin hajiya, ga ƙazantar tsiya ko jikinta bata damu da ta gyara ba, gashi irin laulayin tofar da yawu take haka zata tofar a duk in da ta samu, yalwatacciyar sumar kanta ma duk ta barta ta harmutse bata gyarawa, ba uwar da take yi daga kwanciya sai cin abun da ta ga dama, ko wanka ma sai an ci sa'a dole Hajiya ta sa aka samo mata mai aiki, wani lokacin in hajiya ta je duba ta ita zata matsa mata kan ta daure ta tashi ta gyara jikinta, haka za ta tashi tana ta ture-turen baki, ba ƙaramin jin jiki Ibrahim yake ba akan cikin don kuwa hakkin shi ma wannan ba a maganar shi gaba ɗaya ta hana shi wai bai tausaya mata.

Tun ana gama bikin Alhaji Nuraddeen ya koma wurin aikin shi, ita hajiya ta ce zata ɗan zauna saboda su Ibrahim ɗin, Jameela na a cikin halin laulayin take ma Ibrahim maganar wai yaushe za su bar ƙasar ai ya ce mata ba su cika zama anan ba, ya ce mata yana jira sai hajiya ta yi maganar lokacin da za su tafi, ganin har cikin ya kai kusan wata biyar ba ai zancen tafiyar na su ba ya sa ta matsa mashi lamba wai ita tafi son ta ci gaba da rainon cikin a ƙasar waje kuma ta haihu hannun ƙwararrun likitoci, ganin ta matsa ya sa shi samun hajiya ya yi mata zancen tafiyar su, a lokacin ta ce mashi tun da juna biyun matar shi ya fara girma bari ta yi ta sauka, jin haka ya sa shi ce mata wai da ya fi son su koma saboda tafi samun kulawa kuma ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci, duk da bai fito fili ya bayyana hakan ra'ayin Jameela bane hajiyar ta so ta fahimci hakan, cikin ɗan murmushi ta ce mashi duk nan ƙasar ba ƙwararrun da za su duba mashi matar tashi ne, ko yayan shi ba a nan aka haifa mashi yaron shi ba, bai dai ce mata komai ba a lokacin itama bata bashi tsayayyar magana kan komawar ta su ba, koda Jameela ta ƙara mashi magana kan hakan ya faɗa mata Hajiya ta ce anan zata haihu, aikuwa ta shiga yin tijara iri-iri, gaba ɗaya ta hana mashi zaman lafiya har tana cewa ita ta yi zaton ma suna yin auren za su tafi honeymoon ƙasashe amman an zo an jibge ta a ƙauye, ga yayan shi can da iyalinshi suna ƙasar waje sai ita don tana bare shine za a ƙi yi mata abun da take so, duk ƙoƙarin shi na ya fahimtar da ita shi Sa'ad aikin shi yake a can ta ƙi sauraren shi. Lokacin da cikin ya isa fara zuwa awo hajiya ta yi mashi magana, ya yi ma Jameela maganar amman fir ta ƙi fara zuwa wai ai ba a damu da lafiyar abun cikin nata ba shiyasa za a barta ma'aikatan asibitin ƙauye su duba ta, da abun ya ishe shi kawai sai ya kira dad ɗin shi ya roƙe shi kan yana son ya taho da Jameela don bata jin daɗi, ya ce cikin na wahalar da ita sosai yasan zata fi samun kulawa anan, hajiya ta yi mamaki lokacin da dad ɗin ya yi mata maganar, dama tun lokacin da ya fara neman auren Jameela ya fara ja da maganarta, bayani ta yi ma dad ɗinsu ta ce mashi ba wata wahalar da take sha kawai dai shine ya fi son hakan kuma ta bari cikin ya yi ƙwari sosai sai su taho, ya ce mata to in tana ganin ba matsala kawai su taho da itan dama itama yakamata ta dawo hakanan.

Farin ciki a wurin Jameela ba ya misaltuwa lokacin da ta ji zancen tafiyar su ƙasar Australia da a lokacin nan dad ɗin yake aiki, Ammin su na jin zancen tafiyar tasu bayan ta sanar mata sai cewa ta yi wai ta tafi da Naila, haka ta sanar ma Ibrahim din cewa tana son tafiya da ƙanwarta don ta rinƙa taimaka mata, lokacin da ya yi ma hajiya maganar ranta ya 6aci ganin yadda Jameelar ke son mayar da su shashashu, cikin yanayi na 6acin rai ta ce mashi ba za a je da wata ƙanwarta ba ko ta ɗauka tafiyan kaman zuwa Kano ne, duk wata kulawa ai zata samu a can tun da anan ma bata rasa hakan ba, a karon farko da ta fara magana akan tsakanin shi da iyalinshi cikin ƙoƙarin ankarar da shi ta ce,

"Ibrahim, yakamata ka isa da gidanka ka zama namiji, ba baki zan maka ba amman muddin ka ci gaba da sake ma iyalinka, ka ce duk abun da take so sai ka yi mata koda kai zaka takura da hakan to kuwa watarana zaka yi kuka da hakan, saboda mata ba a sake masu gaba ɗaya don abun zai ta ƙara gaba ne har ya kai girman da lokacin da zaka so ɗaukar matakin gyara hakan ya fi karfin ka..." Cikin kwantar da murya ta ci gaba da nusar da shi illar dake tattare da hakan, cike da nuna gamsuwa da maganar ta ya yi mata godiya. Jameela ta ji haushin jin ba za a tafi da Naila ba, haka tai ta faman fushi ya bata haƙuri tare da nuna mata tafiyar da itan ne ba zai yuwuwa ba tun da ba a shirya hakan ba. Ba tare da wani ɗaukar lokaci ba aka gama yi ma Jameela duk wani shiri na tafiya, lokacin da ya rage saura sati ɗaya su tafi suka shirya zuwa Kano don ta yi bankwana, kuɗi masu yawa ta buƙata a wurin shi wai zata ba iyayenta tun da tafiya zata yi, ya nuna mata bashi da su tun da bai riga ya fara aiki ba dama yawanci ɗawainiyar su iyayen shi ke yi masu, rufe ido ta yi ta kama yi mashi masifa har tana faɗin ita da ta san irin rayuwar da zata fuskanta ke nan a gidan wllh da bata aure shi ba, a tunaninta zai yi mata duk abun da take so ta yi rayuwar aure mai daɗi, har da ce mashi tana da masu son aurenta da in ta auri wani cikin su ta san zata yi rayuwa mai dadi fiye da ta gidan shi, hankalin Ibrahim ya yi matuƙar ƙololuwar tashi jin kalamanta a lokacin, ba irin lallashinta da bai yi ba yana nuna mata in dai zata yi mashi adalci shima mai ta nema a gidan shi ta rasa, duk wani abu da take son ci shi ko sha tana samu, haka bata yin komai musammaman aka samo mata mai aiki, sannan duk ta buƙaci kuɗi yana bata, kawai wannan da ta buƙata ne sun yi yawa bashi da su a lokacin, amman ta yi haƙuri da ya fara aiki duk wata buƙatar ta ta kuɗi zai rinƙa yi mata, ya ce shi siyasa ma yake shirin fara yi don haka ma ya yanke yin master's degree ɗin shi akan political science.

"Amman ai kuna da kadarori, ba ka faɗa mani har gonaki kana da su naka ba da ake maku noma, a sanina noma ana samun kuɗaɗe sosai to su ina suke da bazaka rinƙa yi mana amfani da su ba?" Ta tambaya fuska a ɗaure ta wani ƙanƙance idanu kanta ko kallabi babu sai baƙar sumarta tum, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ba ƙarya na faɗa maki ba, sai dai su waɗannan kuɗaɗen dama ba su shigowa hannuna suna wurin dad da su ne yake mana hidindimun da suka shafe ni..." Tun kan ya ƙarasa ta katse shi.
Chapter 36 · 0% Book details