Sashe 184
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tuyan awara ba, da alama babu mai hoton ne da tabbas har shi sai an yaɗa, wataƙil har da don da daddare take yin awaran ya sa ba a samun hoton ba...Fahad na zaune idonsa akan wayarsa, mamaki ne sosai bayyane akan fuskarsa yayin da yake kallon abun da ake yaɗawa a social media na soyayyar Deen da Salma, kasa jurewa ya yi ya danna ma Deen kira don ya tabbatar, lokacin Deen bai daɗe da komawa bedroom ɗinsa ba ya fito daga toilet ya ji wayan sa na ringing, bakin gado ya nufa ya ɗauka a inda ya ajiye ta, ɗan murmushi ya yi ganin mai kiran, yanke kiran ya yi shi ya kira tare da hayewa saman gadon, bayan Fahad ya ɗauka suka gaisa Deen ya yi masa ya karatu, Fahad ya amsa mashi tare da tambayar yadda kowa yake a nan, duk da kwanan sa biyu da komawa India, ƴar magana suka yi kafin ya ji Fahad ya ce, "I want to ask about something." Deen ya gyara zama tare da furta ok he should go ahead, Fahad Ya ce, "Abun da na gani yana yawo social media is it true?" Ɗan murmushi Deen ya yi ya ce, "Yea." Shiru Fahad ya yi irin na mamaki ya kashe mutum, after few seconds ya ce, "Amman ya aka yi hakan ya kasance tsakanin ka da ita?" Deen ya ce masa kawai ya ji ya fara son ta kuma auren ta yake son yi, ɗan shiru Fahad ya yi kafin ya ce, "Ita kuma wadda maganar aure ke tsakanin ku fa?" Deen na murmushi ya ce zai aure su ne su duka, "Do you think it is as easy as you think?" Deen ya bashi amsa da in sha Allah zai iya handle na su, Fahad ya ɗan yi shiru can ya furta, "Allah Ya tabbatar da alkhairi." Deen ya amsa da Ameen, ƴar hira kaɗan suka yi Fahad ya yi masa sallama, ba ƙaramin mamaki Fahad ya yi ba jin da gaske ne, a ganin shi mi Deen zai yi da wannan yarinyar wadda har yanzu shi ɗaukar mara kunya yake mata, a ganin shi tausayi da taimakon da ta nuna akan Habu bai isa ya goge wanccan halin nata da ya bayyana ba. Mom Jameela ta ji kamar zuciyarta zata yi bindiga sakamakon ganin bayyana Salma da aka yi a mai tuyar awara, ji take Deen ya gama zubar masu da mutunci a idon duniya ya ƙasƙantar da su, sam ta kasa zama sai pacing up and down take a cikin ɗaki, Leemarh ce ta shigo cikin ɗakin jikinta sanye da kayan bacci tana riƙe da wayarta, mom Jameela ta juyo tana kallonta da fuskarta da ke a murtuƙe, ganin yanayin ta ya sa Leemarh shan jinin jikinta ta kasa furta abun da ya kawo ta, cikin ƙuncin rai mom ta ce ya aka yi ta zo ta kafe ta da ido, da ƙyar ta furta, "Dama zuwa na yi in nuna maki abun da ke ta trending...wai yaya Deen yana soyayya da wata mai awara kuma wai auren.." Wata uwar tsawa mom ta kwatsa mata ta ce, "Fita ki bani wuri Leemarh!" Leemarh ta yi saurin juyawa ta fita daga ɗakin, daga yanayin mom ɗin ta gane ta san da abun da ta je nuna mata...Dad ya shigo cikin ɗakin mom da sallama, nufo ciki ya yi idanunsa akanta kamar yadda itama ta juyo tana kallon shi, a bakin gado ya zauna ya ce, "Mi yake faruwa ne, kin kira ni kina son gani na kuma kamar hankalin ki a tashe..." Katse shi ta yi a fusace ta ce, "Ya hankalina ba zai tashi ba, ba ka ga abun da yake yawo akan Deen ba a social media?" Dad ya ɗan yi shiru yana kallon ta, shima ya gani kuma hajiyarsa ta kira sa sun yi magana kan neman auren yarinyar da yake, sauke numfashi dad ya yi cikin kwantar da murya ya ce, "Na gani, amman ni ina ganin wannan ba wani abun tashin hankali bane ai, tun da ya ji ya gani yana son yarinyar, sai mu yi masa fatan alkhairi." Wani matsiyacin kallo mom take wurga masa ta yamutsa baki, cikin ƙulewa ta ce, "Ke nan kai a wurin ka wannan ɗin ba abun tashin hankali bane? Ana yaɗa ɗan ka na soyayya da ƴar matsiyata mai tuyan awara hakan ne ba wani abu ba?" Dad ya yi ɗan murmushi ya ce, "To Jameela in dai an tabbatar yarinyar bata da wata illa da zata hana a aure ta ai hakan ba wani abu bane, kuma tuyan awara wannan ai sana'a ce ba bara aka ce tana yi ba, neman halak ne." Wani kallon mamakin baka za ci mutum zai faɗi abu ba ta shiga bin dad da shi, cike da 6acin rai fuskarta ta yi wani jajir ta ce, "Maganar in an tabbatar bata da illa kake yi, bacin illa a tattare da ita a bayyane take, yarinyar da ke tuyan wara a titi tana caccafkewa da kowani gardi ita ce zamu amince ɗan mu ya aura? Kuma da kake maganar sana'a, ai ni ban ga sana'a ba a yin wara face tambarin faƙiranci, kuma wllh ba zan ta6a amincewa ba Deen ya auri ɗiyar matsiyata, bama ita ba a duk Funtua ba sa'ar auren shi!" Still dad ya yi yana ta kallonta fuskarsa ta nuna alamun irin mamakin mutum, wai Jameela ce ke faɗin ɗanta ba zai auri ɗiyar matsiyata ba, ko ta manta ita yadda aka auro ta, gara ma ita wadda Deen ke so suna ƙoƙarin neman na kan su, ba kamar ita ba da babu abun da suka saka a gaba lokacin ban da garari, gani dad ya yi idan ya biye ta ransa ne zai 6aci hakan ya sa shi miƙewa yana faɗin, "To ni dai a wurina sana'a komi ƙanƙantar ta sana'a ce, kuma bata daga cikin abun da zai saka a ƙi auren mutum, don haka in dai an yi bincike akan yarinyar an tabbatar babu wata matsala a tare da su da zata sa a ƙi auren ta to ni ba zan ƙi amince masa auren ta ba." Yana kai wa nan ya nufi hanyar barin ɗakin, a masiface mom ke faɗin ai dama ta san tun da ƴar Funtua ce ba zai taba ganin illar ta ba, to wllh sai dai idan ba ranta zai auri yarinyan nan, dad dai bai bi ta kanta ba ya yi tafiyarsa, hakan kuma da ya yi ba ƙaramin ƙara ƙular da ita ya yi ba, ta kai zaune bakin gadon fuska a hautsine, wata irin tsanar Salma take ji a ranta irin tsanar da bata tunanin ta ta6a yi ma wani ita, mai wara Deen zai aura? Kai ina...wllh over her dead body! Ke nan ma so ake duk burinta akan auren shi da Basma ya tashi a banza, kuma ta san muddin ya auri wannan ɗiyar matsiyatan to sai sun handame komai na shi, ƙarshe ta zo ta haifa yara rankacabai don irin su ba control ɗin haihuwa gare su ba, wannan tunanin ya ƙara dugunzuma hankalin mom, ita mamakinta yadda aka yi ma Deen har ya faɗa soyayya da yarinyar, abun da ta ga an wallafa kan sanadiyar alaƙar su ne ya shiga dawo mata, tunanin tabbas da walakin goro a miya ne ya zo mata, lokaci guda ta gasgata zuciyarta kan ba haka nan suka bar Deen ba asiri suka yi masa, ta hanyar yin amfani da kusancin da yarinyar ta samu da shi, dama idan mutum na yin abu sai ya ga kowa ma na aikata abun, nan take mom ta yarda da zarginta, a ranta take raya aikuwa ba zata tsaya kallon ruwa ba kwaɗo ya yi mata ƙafa, zata nuna masu iyakar su...hannunta har ɗan rawa yake ta ɗauki wayarta ta fara kiran Amminsu....