Sashe 107
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kusan sau ukku ta tura kofar a hankali, nan ma wayam ta gani babu kowa a ciki, jawo kofar ta yi ta dawo cikin ɗakin ta nufi gaban dressing mirror, kayan shafan da Leemarh ta yi amfani da su mai da turare da roll on ta bi da kallo waɗanda da gani ba a daɗe da yin amfani da su ba, jim ta yi tare da ɗan ƙanƙance idanunta alamar tana tunanin wani abu a ranta, juyawa ta yi ta nufi ƙofa ta fita daga cikin ɗakin, fitowa ta yi cikin falon daidai lokacin chef Alima ta taho hannuwanta riƙe da tray mai ɗauke da warmers a sama da ta ɗauko daga dining area bayan basu umarnin su kwashe abincin da suka kai ƴan gidan ba za su ci ba, tana zuwa kusa da mom ta dakata cike da ladabi ta gaishe da ita, "Have u seen Leemarh?" Mom ta jefa mata tambaya ba tare da ta amsa mata gaisuwarta ba, da sauri ta ce mata eh ɗan ɗazu bada jimawa ba ta zo kitchen ta haɗa kofin coffee biyu, ɗan yamutsa fuska mom ta yi jin zargin da ya zo mata a rai ya tabbata, da hannu ta ba Alima umarnin tafiya ita kuma ta juya ta nufi bene, tuni Fahad ya gama shan coffee ɗin suna yin hira da Leemarh, har lokacin su biyu ne a cikin falon da alama Deen ya basu space ne shiya sa bai dawo ba, idan ka gan su yadda suke zaune zaka ce masoya ne a zahiri don sun yi matuƙar dacewa da juna, turo kofar da suka ji an yi ya sa a tare suka kai idanunsu wurin, Leemarh na ganin wadda ta shigo har sai da gabanta ya ɗan faɗi ta yi saurin gyara zamanta daga ɗan kishingiɗar da ta yi a saman doguwar kujerar da suke zaune tare da Fahad, shigowa ta ƙarasa yi cikin falon tana jefa masu wani irin kallo fuskarta babu yabo babu fallasa, daga ɗan nesa da su ta tsaya idonta akan su, cikin kama kai Leemarh da ke kallonta ta furta, "Mom..." Shiru bata amsa ba, Fahad ya ɗaga ido a hankali ya gaishe da ita, kaman baza ta amsa ba can ƙasan maƙoshi ta furta lafiya, "What are you doing here?" Ta jefa ma Leemarh tambayar tare da ƙara ɗaure fuska, da ɗan murmushi ta ce, "Ba komai, na kawo ma su yaya Deen coffee ne." Tana ɗan harararta ta ce, "Ina Deen ɗin a nan?" Leemarh ta ce, "Ya tafi bedroom amsa call." Wani kallo ta yi mata har zata juya sai kuma ta dakata ta sake cewa, "Ke baki da abun yi da kika zo ki ka yi zaune a nan?" Bin ta da kallo Leemarh ta yi sai kuma ta ɗan kalli Fahad da kansa ke a ƙasa yana latsa wayansa da ya ɗauka, ɗan ɗaure fuska Leemarh ta yi ta amsa mata da eh hira suke da yaya Fahad, ba tare da ta ce wani abu ba ta juya ta nufi bedroom ɗin Deen, shiru Leemarh ta yi tana kallon Fahad da har lokacin kansa ke a ƙasa, slowly ta kira sunan shi, "Yaya Fahad..." Ya ɗago idanunsa ya kalle ta ya ɗan sakar mata murmushi, ba da jimawa ba mom ta dawo ta nufi hanyar fita Leemarh ta bita da kallo, bayan ta kama handle ta juya da ɗan ɗaga murya ta ce, "To zaki kwana anan ne?" Ɗan tura baki Leemarh ta yi ta ce, "Bana jin bacci, zan taho idan muka gama hiran." Wani mugun kallo ta sakar mata kafin ta ce mata ta taso su tafi, yamutsa fuska Leemarh ta shiga yi alamar bata son tafiya, ɗan ɗago kai Fahad ya yi suka haɗa ido ya yi mata alamar ta je da kai, ba don ta so ba ta miƙe tana tura baki ta ce mashi sai da safe ya ɗaga mata kai, wani murmushi mom ta yi tare da ɗan jinjina kai alamun mamakin wato sai da Fahad ya ce ta tafi sannan, tana gaba mom ɗin na a baya tana yi tana waiwayenta, kana ganin fuskarta ka san bata ji daɗin tahowa ba, har abu ta sako a cikin aljihun rigar baccinta da ta siya ɗazun a mall take son bama Fahad ɗin, tana niyyar idan sun gama hira zata taho sai ta bashi gashi mom ta 6ata mata shirinta, har ɗaki mom ta bita, ta na shiga da sauri ta kai hannu zata rufe ƙofar ɗakinta mom ta bangaje kofar don ta fahimci mi take ƙoƙarin yi, shiga ta yi cikin ɗakin fuska a ɗaure Leemarh dake tsaye tana bin ta da kallo, "Wato Leemarh kin raina ni ko!" Mom ta faɗa a fusace, ɗan yarfa hannu ta yi fuska a yamutse ta ce, "To mi kuma na yi mom?" "Ban sani ba! Duk maganar da na yi maki akan Fahad baki ji ba ko?" Wani kallo mai tattare da mamaki Leemarh ta yi mata ta ce, "Yanzu mi na yi mom? Kawai fa coffee na kai masu har da yaya Deen, sannan na zauna muna hira, mi ye ne laifi a ciki?" Shiru mom ta ɗan yi tana ci gaba da kallonta cikin fushi, "Na gargaɗe ki akan idan ma soyayya kuke tun wuri ki datse ta baki ji ba ko?" Yarfa hannu ta yi ta ce, "Amman mom I have already told cewa ni ba soyayya nike da shi ba..." Ta katse ta, "To shisshige masa na miye?" Leemarh ta ce, "To shi ba ɗan uwana bane? Yadda yaya Deen yake a wuri na haka shima na ɗauke shi, miye laifi to don na shisshige masa." A harzuƙe mom ta ce, "Ke kaɗai ce yar'uwarsa? Ko su Omar suna masa haka ne." Leemarh ta ɗan ta6e baki ta ce, "Kowa da yadda ya ɗauke sa, ni na faɗa maki tamkar yaya Deen na haka na ɗauke sa, duk abun da zan yi ma yaya Deen shima zan masa." Ta ƙare tare da watsa hannuwa alamar gaskiyarta take faɗa, "To bana son wannan shisshige masan da kike, kuma as I warned u, idan ma kin san da wani abu na soyayya tsakanin ku ki yanke shi." Tana ƙarasawa ta juya ta nufi ƙofa Leemarh ta bita da kallo mai kaman na takaici har ta fice, jiki a sanyaye ta nufi bakin gadonta ta zauna, ji ta yi ranta duk ya jagule don ita dai ta san tana son yaya Fahad kuma burinta aure ya shiga tsakaninsu, zuciyarta ta shiga tunzurata kan ta faɗa masa tana son sa kawai, idan ya so maganar ta fasu kowa ya sani a family duk abun da zai faru ma ya faru, sai dai kuma wani 6angare na zuciyarta baya bata ƙwarin gwiwar yin hakan musamman tunanin kada Fahad ɗin ya ƙi kar6ar soyayyar tata, a hankali ta kai hannu cikin aljihun rigar ta, bin haɗaɗɗun chocolates ɗin da ta ɗauko a mall don ta bashi ta yi da kallo, a tunaninta idan ta bashi zai fahimci wani abu game da son shi da take yi saboda chocolates ɗin na ɗauke da kalmar love da hoton heart a jiki, kokonton ko ta bashi ta shiga yi, bayan wani lokaci ta ajiye su daga can bakin gado ta ƙarasa hayewa ta kwanta, zuba ma wuri guda ido ta yi a cikin ranta maganganun mom ɗinsu na dawo mata, mi ya sa mom ta tsani yaya Fahad sosai? ta san ba shi kaɗai take ma haka ba a familyn dad ɗinsu amman dai na shi ya fi yawa, mi ye aibun sa da zata ce bazata bari ta aure shi ba, ita dai a ganinta yaya Fahad bai da wani aibu, yana da duk qualities da za su saka mace ta so shi, gaskiya ita dai tana son shi sai dai komai zai faru ya faru...., haka ta yi ta tunane-tunane da yin tufka da warwara har bacci ya yi awon gaba da ita....