← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 197

Sashe 57

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ahh..wllh sam ban É—auki murya ba, da yake itama ba wata babban murya ne da ita ba, ashe babynah ce.." Tana murmushi ta amsa mata da eh,
"Babynah ya kike? fatan kina lafiya."
"Lafiya lau Autynah, ina wuni ya aiki."
"Alhamdulillah, gani nan ban daÉ—e da dawowa ba ma, da yake evening na yi, gaba É—aya na gaji yanzu nan na watsa ruwa gani nan na baje." Salma tana Æ´ar dariya ta ce, "Sannu Autynah.." Ta amsa mata da yauwa,
"Bari in kai ma innar wayar..." Katse ta ta yi, "No ba sai kin kai mata ba, dama kiran naki ne ina son in ji muryan Æ´ar babynah ne.." Still da dariya akan fuskarta ta ce, "To na gode Autynah mai kaunata, ina missing en ki sosai.."

"Allah Sarki my baby, in sha Allahu ai mun kusa mu kasanci a kusa da juna da zaran kin fara karatu a nan, yanayin aikin namu ne da mutum bashi da lokacin kansa sosai ina ta son nima in zo in gan ku...." Hira suka ci gaba da yi mai nuni da yadda suka damu da juna, daga baya ta tambayeta ko tana da wata matsala ta ce mata a'a,

"Babynah na san halin ki sarai da nauyin baki, in baki sanar da ni buƙatunki ba to wa zaki sanar wa?" With a broad smile Salma ta ce, "Allah Aunty Kubra bani da wata buƙata, ko kuɗin da kika turo mani last time suna nan ban siya komai ba." Da alamun mamaki a muryar aunty Kubra ta ce, "Lahh..ke da na turo ma su don ki siya abun da kike so shine kike ta ajiyar su?" ta ce, "To ai Aunty Kubra ba wani abu da nike so yanzu."

"Kina budurwa za ki ce ba abun da kike so, ina kika bar cosmetics? Su perfumes, roll on..." Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce, "To ai Aunty Kubra duk ina da su fa cikin waÉ—anda kika aiko mani duk akwai saura." Salati Aunty Kubra ta saka, "Yau na bani..Salma ba dai jere kika yi da su ba baki using da su?" Da sauri ta ce mata wllh tana amfani da su,

"To amman yakamata a ce by now sun ƙare ai, kuma dama abubuwa irin wannan wa ya ce maki bari ake har sai sun ƙare sannan a siyo wasu? Tun da products din ko da yaushe cikin yin su ake kala kala, yakamata mutum na bincikawa idan ya ji wani mai kyau da inganci sai ya yi trying nasu ya ga ko za su fi wanda yake using da kyau. Sannan su gyaran kai da jiki....wai ma Salma kina zuwa saloon kuwa?" Kame-kame ta shiga yi tana ɗan sosa ƙasan gashinta ta ce, "To ai ni Aunty Kubra kin san bani yin saloon."

"Ina nufin kina zuwa wankin kai da su gyaran jiki, su lalle?" Ɗan zaro ido Salma ta yi ita yaushe rabon ta da yin wani lalle, kawai dai bata barin ƙumbunanta su yi fari fat, wankin kai kuwa dama sai idan ta je hutu Kaduna wurinta take kai ta amman a nan innarsu ke taya ta ta wanke "Kika yi shiru?" Amsa ta bata da a'a amman tana yin lalle sai dai ba akai akai ba,

"To fisabilillahi baby kuma sai ki buɗe baki kina cewa ba abun da zaki da kuɗi? bacin duk ga abubuwan da ya kamata ace kina yi amman ba kya yi, ai an ce ko kana da kyau to ka ƙara da wanka, idan baki gyara kan ki sosai ta ya zaki samo mana surukin kirki? Ko so kike ki kwaso mana kwashikwaraf?" Tana ƴar dariya ta ce mata a'a.

"To kuwa mace yanayin gyaranta yanayin mazan da za su rinƙa tunkararta. Daga yanzu karki ƙara wanke kanki a gida in ba so kike sumarki ta lalace ba, kina da gashi mai kyau tubarkallah, idan kina son ya ci gaba da bunƙasa to ba kowanne abu zaki na danƙara ma kanki ba wurin wanke shi, duk ƙarshen wata kije a yi maki wash and set da kuma ƙunshi, sai gyaran jiki ma duk bayan lokaci shima a rinƙa yi maki, zuwa da safe zan ƙaro maki kuɗi sai ki haɗa da wanda kika ce suna nan ki je a yi maki duk abun da na ce, har su kayan shafan ki je ki siyo ki daina jira sai sun ƙare, bari ma zan bincika maki skin care products masu kyau sai ki samo." Cike da jin daɗi Salma ta amsa mata da to tare da yi mata godiya,

"Ba godiya zaki mani ba, ki tabbatar kin yi duk abun da na ce kin ji ni?" Kai ta daga, "Eh, in sha Allahu I will do as you instructed auntynah." Murmushi Aunty Kubra ta yi tare da faɗin, "That's my baby girl. Allah Ya ci gaba da raya mana ke ya ƙara yi ma rayuwarki albarka."

"Amin Autynah, may Allah bless ur life too." Cike da jin daɗi aunty Kubra ta amsa mata, bayan sun ɗan ƙara yin hira daga baya suka yi sallama, Salma ta ajiye wayar gefe tana murmushin hirar tasu, don ma bata san cewa har yanzu tana yin awara ba ta san da sai ta yi mata faɗa, don tuni ta hana ta ta ce ta bar ma su Imrana suna yi to amman ita tana son yi, a ranta take raya Aunty Kubra tana matuƙar ƙaunarta ta san kuma don Allah bai ta6a bata haihuwa bane.....

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_

ZAINAB BATURE

21

Washe gari da safe Salma ta fito bayan ta gama yin shirin tafiya islamiyya, a bakin baranda ta tsaya tana yi ma innarsu sai ta dawo, fitowa innar ta yi tana murmushi ta ce, "Za a tafi?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, da yake lokacin da suna yin karin kumallo Salma ta ba innarsu labarin wayar su da aunty Kubra jiya da daddare hakan ya sa innarsu ta ce, "Idan kika dawo sai in taya ki ki kwance kan ki je a wanke makin ko?" Ƴar dariya Salma ta yi ta ce to, sai kuma ta ce, "Ya maganar zuwa kasuwar? Ko ki bani kawai da an tashi sai in wuce ba sai na yi wahalar dawowa ba." ɗan jimm innarsu ta yi ta ce, "Ko dai a bari sai bayan kwana biyu sai a yi awaran?" Da sauri Salma ta ce, "A'a innar mu kawai ki kawo a siyo waken, shike nan don an bamu kuɗi sai mu daina yin sana'a? Ai kuɗin za su ƙare ko." Kai ta gyaɗa ta ce to bari ta bata, ɗaki ta koma bada daɗewa ba ta fito tana riƙe da kuɗi ta bata, bayan ta faɗi mata abubuwan da zata siyo ta ce mata sauran kuɗin ta yi amfani da su ta siya abun da take so, da sauri Salma ta ce, "A'a innarmu ki bar su, ai aunty Kubra ta ce zata turo mani kuɗi, ki yi amfani da waɗannan, na san ma duk a hidiman gida za su ƙare." Yar hararar wasa ta yi mata, "Ke ni ki amsa, na Kubra daban nawa daban, kuma bake kika samo mana su ba." Ƙin amsa ta yi tana noƙe kai tana ce mata ta bassu don Allah, Sagir ne ya shigo har zai nufi hanyar banɗaki ganin su ya fasa ya nufo su,

"Wai Salma wasan da nike yi dake ne ya sa kika fara raina ni? Ya ina baki abu zaki ƙi amsa, kuma dama ba kin ce zaki siyo fara ba ki soya, to ba sai duk ki haɗa ki siyo ba." Innarsu ta faɗa da ɗan daure fuska, yamutsa fuska ta shiga yi tana marairaice mata tana faɗin ai tana da kuɗin da za ta siyo farar,

"Ah lalle yarinyar nan gatan da kike samu ya yi yawa wllh, wato kuɗi ma ake baki kina ƙin amsa. Ni innarmu don Allah ki bani ina so..." Janye kuɗin ta yi ganin ya miƙo hannu ta ɗan ɗaure masa fuska, ya sake cewa, "pls innarmu wllh ina cikin buƙatan kuɗi, kuma dama baki bamu salalarmu ba a cikin kuɗin da Nuree jr ya bada." Wani kallo ta masa ta ce, "Ku da kuka ci gasan kana nufin baku samu komai ba a wurinsa?"
Chapter 57 · 0% Book details