← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 197

Sashe 75

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tana ci gaba da rarrashinta tare da nuna mata ba don kai shi asibitin da ta yi bane ko bata kai shi ba idan yau ne wa'adin da Ubangiji ya ɗaukar masa zai mutu, wayar hajiya da ta ajiye a gefe ta fara yin ringing alamar ana kiranta, kallon wayar ta yi ta ga wanda ke kira, sakin Salma ta yi ta ɗauki wayar, saboda shesshekar kukan da Salma ke yi yasa ta nufi hanyar ɗakinta ta ce tana zuwa, bayan tafiyar hajiya kife kai Salma ta yi a saman hannun kujera tana ci gaba da yin shesshekar kuka a hankali, duk abun nan idon Deen na akanta, can ya miƙe yana tafiya a nutse ya nufi wurin da take, ta gefen da ta ɗaura fuskarta ya tsaya yana kallonta wuyan hijab ɗin jikinta ya ɗan zame hakan ya bayyanar da baƙar sumarta, magana ya yi mata calmly saidai da alama bata ji shi ba, ɗan jimm ya yi yana ta kallonta sai kuma ya ɗan rankwafa, "Salmerh..." A karon farko ya kira sunanta, tana cikin kuka ta tsinci sautin daddaɗar muryar da bata iya tantance ko ta waye ba ta kira sunanta, da sauri ta ɗago kanta da alama ma ta tsorata da kiran sunan nata da ta ji an yi, wani bugu gabanta ya yi ganin shi a kusa da ita, bin kyakkyawar fuskarsa ta yi da kallo ƙirjinta na ci gaba da bugawa da ƙarfi, sai yanzu da ta samu kusanci da shi sosai ta ƙara ganin ainihin tsantsar kyawun shi, shima kallon cute fuskarta ya ke wanda yau ne ya ta6a ƙare mata kallo sosai, idanuwanta sun yi ja har lokacin da ɗan kumburi akan su, yayin da dogayen gashin idonta suka mammane ma juna saboda jiƙewar da suka yi da hawaye, bin juna suka ci gaba da yi da kallo shi ya kasa ce mata komai ita kuma tana ta ɗan kikkafta idanu tana sakin ƴar ajiyar zuciya, tun da ta yi arba da fuskarsa a kusa da ita ta nemi kukan da take yi ta rasa, hannunsa ya ɗago ta maido idonta kan abun da ya miƙo mata, kallon shi ta yi ba tare da ta amsa ba ya ɗan lumshe idanunsa with calmness ya ce, "Take it....wipe ur tears." Hannunta na ɗan rawa ta amsa hanky ɗin da ya bata, maimakon ta yi abun da ya ce sai ta bi hanky ɗin da kallo don a wurinta na musamman ne don wani irin taushi ne da shi ga wani sanyi sanyi da jikinsa ke saki kamar yana da lema kuma ba lemar ba ce, a hankali ta ɗaga ido ta kalli Deen ya yi mata alamar ta yi abun da ya ce da kan shi, kai hanky ɗin ta yi fuskarta wani irin ƙamshi mai nutsar da zuciya ya ziyarce ta, slowly ta shiga goge hawayen fuskarta har bata san tana ɗan lumshe ido ba saboda taushin hankyn, bata daɗe tana goge fuskar ba ta cire ta miƙo masa, bai amsa ba calmly ya fara mata magana, "Stop worrying, you didn’t cause his death. Kin yi abu mai kyau da kika taimake shi, it’s just that lokacinsa ya yi shi ya sa ya mutu." Tamkar yana biya mata karatu tana ɗauka yadda ta bisa da ido, ɗage mata gira ya yi alamar ta gane, tamkar yar ƙadangaruwa haka ta gyaɗa masa kai, miƙewa ya yi, ganin yana niyyar tafiya da sauri ta ce masa, "Ga shi.." Ba tare da ya kalli hankyn da take miƙo masa ba ya ce ta ci gaba da using da shi ya san ba gama kukan ta yi ba, da sauri cikin muryar kuka ta ce, "Na daina..." Ya ɗan juyo ya kalle ta da murmushi, ba tare da ya ce mata komai ba ya juya ya nufi hanyar shiga 6angaren da bedrooms suke ta bisa da kallo har ya shige, maido idanunta ta yi tana kallon hankyn tana ɗan yamutsa shi da hannunta, bai daɗe da shigewa ba sai ga hajiya ta dawo, zama ta yi a inda ta tashi kusa da Salma tana kallon ta ta ce, "Yi haƙuri Salma na bar ki zaune wata doguwar waya aka kira ni ne, kin daina kukan ko?" Kai ta ɗaga mata alamar eh ta ce yauwa haka yakamata, tambayoyi ta shiga yi mata game da gidan su Habu Salma tana bata amsa, bayan ta gama tambayar tata ta ce ko a zuba mata abinci Salma ta ce mata a'a yanzu tana gama ci ta taho nan, shiru suka ɗan yi can hajiya ta tambaye ta Deen fita waje ya yi ne Salma ta ce mata a 'a ciki ya shiga ta ce ok, Salma na ta jira ta ga Deen ya fito ta bashi hanky ɗinsa, har bayan wani lokaci bai fito ba gashi dare na ƙara yi, ƙarshe ta yanke tafiya kawai tun da bai fito ba, sallama ta yi ma hajiya ta ce zata tafi, miƙewa hajiya ta yi tana ƙara kwantar mata da hankali ta ce in sha Allahu gobe zata saka Balaraba ta rako ta ta yi gaisuwa gidan su yaron Salma ta amsa da to daga haka ta tafi. Tana tafiya kan hanya tana tunanin abun da ya wakana tsakaninta da Deen, ɗago hanky ɗin ta yi tana kallo, a hankali ta kai shi saitin hancinta, ɗan murmushi wanda bata san daga ina ya fito ba ya su6uce mata. Bayan ta koma gida innarta ke sanar mata aunty Kubra ta kira tana son magana da ita bayan ta ji abun da ya faru, amsar wayar innarsu ta yi ta tafi ɗaki bayan ta zauna a bakin gadonta ta kiran aunty Kubra, saida ta yanke sannan ta kira Salma ta ɗaga, "Hello baby!" Ta faɗa da alamun tashin hankali, murya can ƙasa Salma ta amsa tare da gaishe ta, amsa mata gaisuwar ta yi ta ce, "Na ji abun da ya faru, ai ba laifin ki bane baby ke da kika yi taimako kawai lokacinsa ne ya yi. Pls ki daina damuwa gashi na ji ance har zazzabi ya kama ki." Tana kikkafta idanu ta ce mata ai ta bari, "Yauwa my baby ki kwantar da hankalinki kin ji, Allah Ya jikansa ya sa mai ceton iyayensa ne, kema Allah Ya baki ladan taimako." Ta amsa mata da amin, "Yanzu ya jikin naki, har yanzu akwai fever ɗin?" Girgiza kai ta yi ta ce mata a'a ya sauka, "Kin ci abinci?" Ta ce mata eh, "To kin ci sosai kuwa, ko akwai abun da kike so in saka Sagir ya kawo maki?" Ɗan murmushi Salma ta yi ta ce mata a'a, "Kai babynah, nasan ki da nauyin baki feel free ki faɗa mani komi kike so." Still da murmushi akan fuskarta ta ce mata Allah bata son komai, "Ko kaza?" Wannan karon dariya maganar aunty Kubra ta bata ta ce mata itama bata so, waya suka ci gaba da yi tana ƙara rarrashinta kan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa a ranta, kafin su yi sallama sai da ta ƙara tambayar ko akwai abun da take buƙata ta ce mata ba komai ai ta faɗa mata game da kuɗin da Deen ya bata ta ce ta ƙi ma ta amshi wasu ciki, aunty Kubra ta yi murmushi ta ce mata a'a ta riƙe abunta ta yi abun da ya ce ta yi da su, daga baya suka yi sallama tana ƙara jaddada mata ta cire damuwa a ranta. Bayan sun gama yin wayar zaune ta yi a wurin kamar mai yin tunani, kai idonta ta yi kan hanky ɗin Deen da ta ajiye a gefe, a hankali ta kai hannu ta ɗauko ta ƙura mashi ido tana kallo, a cikin ranta take ƙara yaba irin kirkin Deen tana ɗan murmushi, after some minutes ta miƙe don ta kai ma innar su wayarta, ba da daɗewa ba ta dawo ɗakinta, gado ta nufa ta kwanta, ɗan tsoro ta ji na niyyar kamata saboda tunanin Habu da ya shiga dawo mata, ta yi saurin kauda tunanin ta koma tunano abun da ya faru tsakaninta da Deen, a hankali ta kai hankyn da take riƙe da shi hancinta tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da yake saki tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta, slowly idanunta suka fara lumshewa a haka har bacci ya yi awon gaba da ita....
Chapter 75 · 0% Book details