Sashe 171
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Wannan kyau sai ka ce dai yau ne auren, ko da yake na san shigar yau nafila ce a kan ta ranar....amman kada fa yana ganin ki ya buƙaci a ɗaura auren yau ko gobe, sai dai baban Sageer ya ji an doka masa kira cewa ana son a ɗaura auren ki." Dariya sosai Salma ta saka, lokaci guda kuma zullumin da take ya zo mata a rai, a sanyaye ta kalli aunty ta ce, "Aunty ni sai in ta jin kaman idan ya zo zai ce....kaman zai yi mani maganar wanccan ne." Aunty da ta fahimci abun da take nufi ta ce, "Wai kina ganin zai ce ya fasa son ki, ai baby ba wani lafiyayyen namiji da zai iya rejecting naki, koda ma a ce ya zo da wannan niyyan ina tabbatar maki zai fasa ne, balle ma na san bada hakan zai zo ba, wataƙila dai ya yi maki bayanin wanccan ɗin ba wai ya ce ya fasa son ki ko auren ki ba, in sha Allah alkhairi zamu ji." Salma ta sauke idonta ba tare da ta ce komai ba, gyale da takalma duk sababbi aunty ta fiddo mata, tana ɗan ƙara gyaggyara ta suka ji wayar Salma ta fara ringing, aunty ta ce ta je ta duba ƙilan shine, gado Salma ta nufa sai ka ce wata amarya ta ɗauki wayan ta ga shi ɗin ne, aunty da ke kallonta ta tambayi shine ta ɗaga mata kai ta ce ta ɗauka, bayan ta yi picking kiran ta kai kunne tare da yin sallama, ɗan saurarawa ta yi kafin ta furta ok daga haka ta cire wayar, kallon aunty ta yi ta ce, "Wai ya ce ya zo address da aka tura mashi." Da sauri aunty ta kai hannu ta ɗauki wayarta tana faɗin bari ta kira Isyaku, dama ɗazun bayan ya gama yin shara ta sanar da shi cewa za ta yi baƙo ya kasance available watakil zai yo masa jagora zuwa gidan, bayan Isyakun ya ɗaga ta sanar da shi cewa baƙon nata ya iso, ya tambayi a mota suke aunty ta ce eh, kalan motan ya tambaya ta ce ba ta sani ba bari ta tambaya, sai kuma da sauri ta ji ya ce, "Aunty ga wata mota nan na ga ta shigo layin nan yanzu." Tambayar shi ta yi wace irin mota ce, ya ce, "Wllh aunty ban sani ba, haɗaɗdar farar mota ce ni dai bamma taba ganin kalan ta ba balle in san wace iri ce." Ya na maganar idon shi akan motan dake ta ɗaukar ido gashi ba zaka ce ga wanda yake ciki ba don glass din ta tinted ne kuma hatta lambar motar an rufe, aunty na jin haka ta yi tunanin Deen ɗin ne, aunty ta ce mashi motan ta tsaya ne ko tafiya take, Isyaku ya ce mata tafiya take amman a hankali da alama baƙon ne yake neman gidan bari ya je ya gani idan shine, nufar motar ya yi da yar sassarfa, daga wurin ƙofar gaba ya tsaya ya yi sallama duk da bai ganin wanda ke ciki, slowly glass ɗin front seat ya sauka, har saida gaban Isyaku ya faɗi lokacin da ya yi arba da mutumin da ke zaune a gaban, ganin shi wani jibgege mai ƙirar ƙarfi, ga shi gaba ɗaya jikinsa baƙaƙen kaya ne kansa ya saka baƙar hula face cap ya kuma rufe fuskarsa da baƙin takunkumi, a cikin rai Isyaku ya shiga kokonton anya kuwa baƙon auntyn ne, Isyaku bai san lokacin da ya ɗan rankwafa ba ya gaishe da mutumin ganin yana kallon shi, kai kawai mutumin ya ɗaga, cikin ɗan dabarbarcewa Isyaku ya ce, "Da...dama zan tambaya ne ko kai ne za a yi ma jagora zuwa gidan aunty Kubra?" Mutumin bai ce masa komai ba ya juya ya kalli baya kana gani magana ya yi da wani, juyowa ya yi ya jinjina ma Isyaku kai alamar eh, da sauri ya ce to ga gidan can ya yi gaba yana tafiya da sassarfa motan na bin shi a baya, yar tafiya kaɗan suka yi suka iso gidan, Isyaku ya kama gate ɗin gidan ya zuge tare da ja baya motan ta kutsa cikin gidan, rufe gate ɗin ya yi ya ƙarasa gaban motan yana ce ma mutumin bari ya sanar da ita gashi ya zo, nan ma mutumin kai kawai ya ɗaga masa, Isyaku ya nufi cikin gidan da sauri a ransa yana tunanin ko wane baƙo ne wannan aunty ta yi, amman kuma ya gane ba mutumin bane kaɗai a motan, ban da shi da wanda yake tuƙa motan akwai wani a baya....bayan Isyaku ya sanar ma aunty ya dawo wurin su ya sanar da su ya faɗa mata, nan ma dai mutumin kai ya ɗaga masa, har ya nufi gate zai fita ya ji an ce masa, "Hey..." Hakan ya sa shi juyowa, wanda ke a mazaunin driver ne ya yi masa magana, shima dai irin suffa da shigar ɗayan na gaban ke gare shi, Isyaku ya ƙarasa wurin shi tare da ɗan rankwafawa kamar mai neman gafara, bayan motan ya ga mutumin ya juya kafin ya juyo ya miƙo masa abu a hannunsa, hannu na rawa Isyaku ya karba ya ga kudi ne masu ɗan yawa, godiya ya shiga yi ma mutumin yana ɗan zaka kai a kokarin sa na ya hango wanda ke a bayan amman bai iya hango kowa ba, ya nufi gate yana ta mamakin kuɗin da aka basa da kuma wanda ke a bayan, wanda idan da Isyaku ya ga Deen wataƙil har kusan suma sai ya yi don daɗi saboda big fan ɗinsa ne....aunty ta shigo cikin ɗakin Salma bayan Isyaku ya sanar da ita isowar baƙon, tana murmushi ta ce, "Zakanya to ga Zakin naki ya iso." Salma ta ji gabanta ya faɗi, dama tun da ta ji an buɗe gate kirjinta ya shiga bugu da ƙarfi, aunty ta ɗauki gyalenta da ke ajiye gefe ta miƙa mata, Salma ta amsa tare da miƙewa ta yafa gyalen, aunty ta ɗan ƙara gyaggyara ta kafin tana murmushi ta ce mata ta je kada ya yi ta jira, Salma ta ɗan marairaice ta ce to ta raka ta, dariya aunty ta yi ta ce ya za ai ta raka ta gun saurayi, tare suka fito falo aunty na kallon ta da murmushi ta ce mata ta je ta kuma kula, Salma ta nufi kofar fita daga falon gabanta na faɗuwa......
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
55
*✨A CIKIN RAYUWA✨*
ZAINAB BATURE
55