← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 197

Sashe 65

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Ajiyar zuciya innarsu Salma ta sauke bayan ita da Salma sun gama kallon vedion ziyarar da Deen ya kai da irin tallafin da ya bada, miƙa ma Sagir wayar shi da suka yi kallon a ciki ta yi ta ce, "Wai haka yake da kuɗi? Na ga ba ƙaramin tallafi ya ba mutane ba!" Ta faɗa da mamaki, wata dariya Sagir ya yi yana jinjina kai ya ce,"Yo innarmu wannan har wani abu ne a cikin irin kuɗin da yake da su a matsayinsa na ɗan ƙwallon kafan Turai, mutumin da a duk sati ake biyan su miliyoyin kuɗi, ai duk yadda zan faɗa maku irin kuɗin da ake samu a harkar ƙwallo ba zaku gane ba wllh, ku dai ku taya ni addu'a in samu irin damar shi, wllh da gaba ɗaya danginmu sun warke daga talauci." Salma da ke a gefen innarsu saman tabarma ta yi dariya ta ce, "Kamar gaske, kai idan Allah Ya sa ka samu dama har ka tafi ƙasar waje ai na tabbata can zaka samu matan turawa ka aura mu kuma sai mun gan ka kawai." Wani mugun kallo ya jefa mata ya ce, "Ke dai wallahi sakarya ce, maimakon mutum ya faɗi niyyarsa mai kyau ki yi masa fatan alkhairi sai zancen banza." Dariya ta shiga ƙyalƙyata masa ya yi ƙwafa tare da miƙewa da alama ya ji haushin maganar tata, "Sorry my brother, Allah Ya tabbatar maka da niyyar ka, ka ga ma sai kawai in koma wajen ka can ƙasar wajen in ci gaba da karatuna." Tsoki ya yi mata daga haka ya fice daga gidan innarsu dai bin su ta yi da kallo tana dariya don abun su ba shi da ranar ƙarewa. Bayan sallar magrib su Imrana suka fitar da kaya don fara tuyar awara, bayan Salma ta gama shiryawa don zuwa wurin awaran, ɗakin innarsu ta shiga ta iske ta zaune a bakin gado tana ninkin kaya, tana ganin Salma ta fara yi mata murmushi itama shine akan fuskarta, a saman kujera ta zauna ta yi mata sannu ta amsa, ta ce ma innar zata tafi wurin tuyar awaran, tana kallonta still da murmushi a kan fuskarta ta ce, "Ki yi zaman ki ki huta tun da ga su Imrana can suna yi." Ta ce mata a'a zata je, gyaɗa mata kai innarsu ta yi ta ci gaba da ninkin kayan, ganin Salmar ta yi shiru kuma bata tashi ta tafi wurin awaran ba kamar yadda ta ce ya sa ta dakata tana kallonta ta ce, "Ko da wani abu ne Salma? Na ga kamar da magana a bakin ki." Kallonta ta yi tana faffaɗan murmushi ba tare da ta ce komai ba, "Yaushe muka fara haka da ke? Minene kike son faɗa mini har kike jin nauyi haka?" ƴar dariya Salma ta yi ta ce, "Innarmu ba fa wani abu ba ne." ta ce, "To faɗa mini ina jin ki auta ta." Ta tattara duka attention ɗinta akan ta, ci gaba da murmushi Salma ta yi haka nan sai take jin nauyin abun da take son faɗa mata, zuba mata ido innarsu ta yi tana jiran ta ji mi zata faɗa ta ce, "Ko dai saurayi kika yi ne shi ne kike jin nauyin sanar mini?" Cike da zolaya innarsu ta faɗa, dariya sosai Salma take yi ta ce, "Kai innarmu wani saurayi kuma, ai in wannan ne ba zan ji nauyin sanar maki ba, kamar yadda kike ce mini idan har na yi saurayin da na ji ina son sa in sanar maki kar in 6oye maki." Kai ta jinjina mata alamar haka ne, ta ce, "To yanzu ma koma minene kar ki ji komai ki faɗa man zan fahimce ki." Salma na dariya ta ce, "Ba fa wani abu bane, dama cewa zan yi ko yau ma a yi ma yaya Deen irin awaran jiya na ga ya ci sosai ba har na faɗa maki yadda suka yi da hajiya ba da bai bata ba." Faffaɗan murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce, "To dama wannan ne kika kasa sanar mani Salma, ai ba wani abu bane ni jin daɗina ne a ce ina da abun da zan bashi kuma ya amsa, mutum irin wannan komai ka yi masa baka faɗi ba saboda irin alkhairinsa, ko da ace alkhairin nasa bai je ma mutum ba zai je ma wani nasa ko wanda ya sani, kin san a cikin waɗanda ya biya ma kuɗin aiki a asibiti har da malam Rabi'u?" Shiru Salma ta ɗan yi alamar tunani ta yi saurin cewa, "Baban su Habiba?" Kai innarsu ta ɗaga, "Eh wllh..baki ji yadda na ji daɗi ba ɗazun da muna waya hajiyarmu ta sanar mani, dama bayin Allah sun shiga damuwa ana ta faman cuku cukun yadda za a haɗa kuɗin aikin sai gashi Allah Ya kawo mafita." Murmushi ne akan fuskar Salma a cikin zuciyarta fuskar Deen na mata yawo, "Daga can ƙasan mu ma na ji akwai wani mutumi mai fama da lalurar ƙoda shima yana cikin waɗanda suka samu tallafin aiki, ko baka haɗa komai da mutum ba ka ji ya samu mafita akan mayuwacin halin da yake ciki dole ka ji masa daɗi wllh. Allah dai Ya saka masa da alkhairi Ya ƙara masa ɗaukaka." Salma ta amsa da ameen with a smile on her face, innar ta ce mata ta je ta ɗebo awaran sai a haɗa dare na ƙara yi ta amsa da to ta miƙe, bayan ta dawo suka fara yin aikin tare kamar jiya, innarsu ta bada shawarar su canza yau a yi masa egg sauce. Deen yana kishingiɗe a saman gado hannunsa riƙe da wayarsa yana duba tarin saƙonnin da aka masa, wasu ya yi reply wasu ya yi liking, daga cikin waɗanda suka ɗaura ziyarar tallafin nasa a shafukan su har da mai girma gwamnan katsina ya yi masa kalaman yabo da godiya da kuma fatan alkhairi, shima Deen ya yi masa godiya tare da ɗaurawa a page ɗin sa, ɗayar wayarsa dake ajiye a gefensa ce ta fara yin ruri ya kai idanunsa kanta kafin ya ɗauka, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ya yi picking call din a nutse ya furta, "Good evening dad.."
Daga É—aya 6angaren dad É—in ya ce, "How are you my son?" Ya amsa masa da Alhamdulillah, dad ya ce, "Ma sha Allah, gani nan cikin farin ciki sosai ganin yadda al'umma suke ta jin daÉ—i da yabon abun da ka yi Deen, ba zan 6oye maka ba na ji daÉ—i sosai har bansan yadda zan bayyana maka ba, I am always proud of u my boy." Murmushi ne akan fuskar Deen ya ce, "Thank you dad."
"Yaushe zaka dawo ne, ko Funtua ta yi maka daɗi nan zaka ƙare hutun naka?" Ya faɗa yana ƴar dariya, amsa Deen ya bashi da zai dawo akwai abubuwan da yake so ya ƙarasa kammalawa, hira suka ci gaba da yi dad na bayyana masa yadda shima mutane suka yi ta kiransa suna nuna jin daɗi da yabon abun da ya yi kafin daga baya suka yi sallama, ko minti biyar ba a yi ba sai ga kiran mom ɗin sa ya shigo, bin wayar ya yi da kallo kamar mai shakkar ɗaga kiran, sallama ya yi bayan ya ɗaga, ko amsa sallamar bata yi ba ta fara cewa, "Wai Deen mi yake damun ka ne? Yaushe ne zaka fara yin tunani yadda ya kamata? Ka je ka samu wuri ana ta tunzura ka kana 6annar kuɗi sai ka ce wanda bai son ciwon kansa ba. Kai baka da buƙatun kanka ne da zaka tare a biya ma wasu nasu? Idan taimako ne ai daidai gwargwado kana yi, ko ba dama kana yin taimakon a foundation ɗin naka da ita kakar taka take running maka ba? Wannan duk bai isa ba da sai an saka ka je kana ma wasu 6arin kuɗi, mutane da rashin godiyar Allah da mugun hali hakan kuma ba zai hana su bika da sharri ba ba kamar ganin Allah Ya ɗaukaka ka. Ai kana da family, idan kuɗin sun yi maka yawa ka biya ma ƴan'uwanka buƙatun su ba ka tare a hidimta ma wasu bare ba da yabawar da za su yi ba lalle har zuciya ba...." Shiru ya yi yana saurarenta fuskarsa ta bayyana yanayin 6acin rai, "Deen are you there?" Ta faɗa jin har ta ƙare maganganunta bai ce mata uffan ba, slowly ya furta, "Yea.." A ɗan fusace ta ce, "Ok, shine ka yi banza da ni in ƙaraci haushina?" Ɗan murmushi ya yi wanda ya fi kama da a kira na takaici, lumshe ido ya ɗan yi trying to calm himself kada ya fadi wani abu ba daidai ba, calmly ya ce, "Ki yi haƙuri mom, amman ni abun da na yi ra'ayin kai na ne ba wanda ya sani, kuma na yi ne saboda Allah not to seek people's praise, ban yi realizing hakan abu ne mara kyau ba ganin yadda kowa ke yabawa sai yanzu da ke kika nuna mani hakan." Shiru ta yi na ɗan lokaci da alama ya kashe mata baki, cike da kama kai ta furta, "Nima ai ba ina nufin hakan da ka yi abu ne mara kyau ba, kawai dai yakamata a ce kana yin tunani a duk abun da zaka yi, bai kamata ka tare a taimakon wasu bare ba kawai." Ɗan ta6e baki ya yi ya ɗan sauke ajiyan zuciya ya ce, "I thought yin taimako koda a wuri guda ne in dai ana buƙatan hakan ba laifi bane, kuma nan ne asali na, miye laifi don ina taimaka ma mutane?" A ɗan harzuƙe ta ce, "Ta ina nan ɗin ya zama asalin ka? A nan aka haife ka?" Shiru ya yi don ya san ko mi zai faɗa sai ta yi jayayya da hakan, ta ci gaba da faɗin, "Ka kama ka tare a nan, sai ka ce nan kaɗai kake da dangi, ga su Ammi can duk sun ƙagara su ganka sai tambayar yaushe zaka je suke yi, amman da yake su baka basu mahimmanci ba shi ya sa ba ta tasu ka ke ba, balle ka yi tunanin zuwa suma ka ji buƙatun su." Ɗan murmushi ne akan fuskarsa jin ƙarashen zancen nata, dama ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ita bata ƙaunar ta ga an hidimta ma wani in ba danginta ba, sigh ya yi ya ce mata zai je can ɗin da ya kammala abubuwan da yake yi a nan, ta ce, "Allah Ya sa. Amman yakamata kafin ka je ka fara tura masu wasu kuɗi, za su ji daɗi su san ka damu da su kuma kana sane da su, tun da duk suna ganin irin 6arin kuɗin da kake yi akan wasu bare." A taƙaice ya ce mata zai yi hakan da tunanin faɗin hakan zai kawo ƙarshen korafin nata, sai kuma ya ji ta sake cewa, "Ita Basma kuna yin wayar ko itama ka shiga dangi masu muhimmanci ka manta da ita?" Runtse ido ya yi tare da yamutsa baki kafin ya bata amsa da ko jiya sun yi chat. Ajiye wayar ya yi bayan sun gama ya zuba ma wuri guda ido, duk da ya san halinta amma sosai bai ji daɗin maganganunta ba, ganin yadda kowa yake yaba masa kan abun da ya yi amman a ce sai mahaifiyarsa ce zata kushe, hannu ya kai ya dafe forehead ɗinsa tare da ɗan lumshe ido, bayan ɗan lokaci ya kai hannu ya ɗauki wayoyinsa, zuro kafafunsa ya yi ƙasa ya miƙe tare da nufar ƙofa ya fita. Bayan sun gama haɗa awaran, a cikin wata warmer mai kyau aka zuba awaran sai egg sauce ɗin a cikin ƙaramar warmer ɗin ta awaran, shiryawa Salma ta yi cikin doguwar rigar atamfa ta yi ɗaurin kallabi mai kyau gashinta dake a fake ya leƙo ta ƙasan ƙeyarta, fuskarta ta yi fresh duk da bata shafa hoda ba dama haka face ɗinta take zaka ga kamar ta shafa hoda saboda yadda fatar ta take sumul, iya ɗan lip gloss ta shafa ta yafa gyale, ita kanta ta ga ta yi kyau bayan ta duba madubi da yake akwai wuta, sai kuma ta kasa fita saboda kunya a cikin zuciyarta tana raya to ma wai duk miye na yin shirin, duk da jiya ma sai da ta canza kaya amman ita kanta ta ga ta fi fitowa tsaf tsaf yau, da ƙyar dai ta fita daga cikin ɗaki a zuciyarta tana zullumin kada innarsu ta zargi wani abu, dama ɗazun saida ta ji kunyar cewa a yi masa awaran da ta yi.....
Chapter 65 · 0% Book details