Sashe 13
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 5
.....Bayan Salma ta gama yin wankin, cikin barandar ta dawo, har lokacin duk suna a zaune itama ta koma gefen babansu ta zauna, hira suka ci gaba da yi don lokacin ya gama cin abincin,
"Auwalu yau bazaka je can wurin aikin bane?" Baban ya tambaya idanunsa akan Auwalu dake lallatsa wayar shi shima tuni ya gama cin abincin, É—an sosa kai ya yi ya ce mashi wllh ya dawo daga makaranta ya gaji ne yau sun sha lectures kuma gashi yana da assignment da zai yi saidai zuwa gobe in Allah ya kaimu, jinjina kai baban ya yi ya amsa da Allah Ya kai mu.
"Kai Sagiru gaba ɗaya ma so kake ka watsar da karatun naka ko? Yanzu kusan fin shekara da ka kammala karatunka na sakandare amman ka tsaya shiririta ka ƙi ka maida hankali ka ci gaba." Ɗan kikkafta idanu Sageer ya shiga yi yana dan murmushi bai ce komai ba.
"Shi wai nan babban ɗan kwallon ƙafa yake son zama." Salma ta faɗa, jinjina maganar baban ya yi tare da maimaita abun da aka ce yana son zama,
"Dama ka tsayar da hankalinka ka yi karatu, ka dai san a ƙasar nan sai mutum yana da hanya, akwai waɗanda suka iya ƙwallo sosai, da in aka taimaka masu ba ƙananun ƴan ƙwallo zasu zama ba, amman saboda basu da hanyar hakan gasu nan sun kare da bugawa a cikin unguwanni suna wahala basu samun komai." Auwalu ne ya faɗa cikin nuna girma.
"Ka ji abun da ɗan uwanka ya faɗa, don haka ka daure ka ci gaba da karatun ka kada a yi biyun babu, idan Allah Ya ƙaddaro zaka zama abun da kake so ko ba yanzu ba zaka zama, amman yanzu ka yi ta zama haka nan bai kyautu ba, ga ɗan uwanka nan ya dage da karatu kuma yana zuwa wurin sana'a, amman kai gaba ɗaya ka ƙi ka maida hankali kan sana'ar sosai. Rayuwa gudu take yi nan da ɗan lokaci kaɗan zaka ga an kai munzalin tara iyali, gara tun kan lokaci ya ƙure ma mutum ya samu madogara, don ajiye iyali bai yuwuwa ba tare da mutum yana da hanyar da yake samu ba, in kuwa ba haka ba mutum ya ce zai tara iyali ba wata ƙwaƙkwarar sana'a tabbas zai jefa kan shi a matsala babba, wahalhalun rayuwa su taru su yi mashi katutu, ina amfanin mutum ya tara iyali madadin ya ji da su dadi sai su ƙare da shan wahala."
A nutse Sagir ya ce, "In sha Allahu zan maida hankali in ci gaba da karatun, dama ina jira a fara sayar da form na Jamb zan siya in yi."
"To Allah Ya bada sa'a. Ku daure ku dage wata rana zaku ci ribar karatun, tun da mu bamu samu muka yi ba shiyasa muke son ku ku yi. Duk da Alhamdulillah, dai dai gwargwado da sana'a Allah Ya rufa mana asiri, amman in mutum ya haɗa da aikin zai fi wadatuwa, ita kanta sana'a in aka haɗa da ilimi tafi faɗaɗuwa, mutum zai ƙara sanin hanyoyi da dubarun da zai inganta sana'ar ta samu karbuwa ba a iya inda yake ba a fadin duniya baki daya." Duk sun natsu suna sauraren shi, ba tun yanzu ba ya saba zama ya yi masu nasiha kan abun da zai amfani rayuwarsu, akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin shi da iyalan nashi,
"Ke mamana ba zaki siya form na Jamb É—in bane.?"
Kai ta É—aga mashi ta ce, "Eh, abun da nike son karanta ba sai an yi ta ba."
"Ita ka san Auntynta Kubra take so ta gado, itama karatun aikin jinyar take son yi, a yadda ma suka tsara can Kaduna zata je ta yi karatun in ta ci jarabawa." Kai mahaifin nasu ya jinjina jin bayanin innarsu Salma yana murmushi,
"To sai ki dage, duk da nasan baki wasa da karatu. Allah Ya yi maku albarka, Ya baku sa'ar duk abun da kuka saka gaba na alkhairi, Allah Ya ƙara shiryar da ku a bisa tafarkin manzo (S.A.W)." Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin amsawa, "Ameen." Kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi, suna matuƙar jin daɗi in mahaifin nasu na yi masu addu'a haka.
"Yau baza ku yi awaran bane?" Auwalu ne ya tambaya yana kallon Salma, kafin ta bashi amsa baban nasu ya ce, "Af, ka ga na shafa'a ma, Sagir jeka waje akwai sauran katakai dana tattaro masu suna nan a bayan mashin." Cike da jin daÉ—i Salma ta ce yauwa dama tafi son yin amfani da sauran katakan akan gawayi.
"Amman mamana ai gawayin kaman ya fi sauki ba hayaki ko?"
Ta ce matsalar gawayin in ya cinye sai mutum ya ta saukewa yana girgijewa ya ƙara, shi kuwa icce ko katako kawai sai dai ta iza. Shigowa Sagir yayi hannuwan shi ruƙe da katakan da aka ɗaure, a gaban kitchen ya ajiye Salma na ganin su da ɗan yawa ta fara washe baki,
"Gasu nan, amman waÉ—annan biya na za a yi gaskiya, sai in ta kawo abu ana yin sana'a amman ba a bani komai, kuma nima ai siyo katakon muke yi." Dariya duk suka yi jin maganar baban.
"Amman ai kana cin awaran ko, kullum sai an ɗibar maka mai yawa, sannan kuma idan babu wasu abubuwan kamar magi da gishiri da sauran abun abinci ba Innarmu take badawa ba a siyo, watarana ma har abincin da za a dafa take bayarwa a siyo." Salma ta faɗa tana dariya, hannu baban nasu ya kai ya ruƙe ha6a ya ce,
"Tohh, abun yau gori za a mani ke nan." Suka saka dariya gaba É—aya,
"Yau mun ji tsakanin ku, gashi nan duk yadda ka ke ji da ita amman ta yi maka gori." Hararar Sagir da ya yi maganar Salma ta yi ta ce, "To an ji, kanwa uwar gami."
"Ba abun da ya shiga tsakaninmu, ai tsakanin uwa da É—anta sai Allah."
Ƴar ƙarar daɗi Salma ta saka ta fara yi ma Sagir gwalo tana fadin an gwasale shi. Hira suka ci gaba da yi cikin nishaɗi gwanin burgewa, sallar la'asar da aka fara kira ya tashe su, baban nasu ya yi masu sallama don komawa wurin aiki daga can in ya yi salla, suma kowa ya miƙe. Malam Bashir ya kasance mutumin arziki ba ga iyalinsa kaɗai ba, hatta mutanen da yake mu'amala da su suna yi mashi shaidar hakan, shi ɗin abun koyi ne ga duk wani magidanci mai iyali, rayuwar shi da iyalan shi ta kasance abun bada misali. Duk da bashi da wadata sosai amman yana da wadatar zuciya sosai, a ganin malam Bashir in har mutum zai tara iyali ya bari rayuwarsu ta tagayyara to miye amfanin tarawa, kullum ƙoƙarin shi ya wadata iyalansa ta bangaren abinci da sutura, gaba ɗaya yaran shi sun fita daban a cikin layin su, tun tasowar su haka zaka gan su tsaf-tsaf cikin sutura ta kirki bai barin su cikin tsumma, ta bangaren karatunsu da lafiyarsu nan ma a tsaye yake yana bakin ƙoƙarin shi, shi yasa sam yaransa basu da damuwar komai, tun tasowar su ba a ta6a kama su da laifin sun ɗauki abun wani ba saboda sun wadata, itama mahaifiyarsu ba zaune take ba tana yin ƴan sana'oin da take tallafa ma mijin nata sun taru sun rufa ma kan su asiri.
ABUJA.
Tun bayan gama sallar magrib su Leemarh suka fara yin shirin tafiya dinner da aka haɗa ma Deen. Tsaye yake gaban dresser idanunsa na kan madubin gaban shi yana gyara zaman waistcoat ɗin jikinsa, wato irin riga mara hannuwa da ake ɗaurawa saman riga ƴar cikin suit mai kaman falmara bayan ya saka ta cikin baƙa mai dogon hannuwa, yayin da Fahad ke can gefe saman kujerar gaban gado ya ɗan zamo jikinsa yana latsa wayarsa, shima da alama ya shirya yana sanye da baƙaƙen suit sai salƙi suke, daga gaban kayan zuwa ƙasan hannunsa farar rigar ciki ta fito don bai saka ma6allan kayan ba, yayin da wuyansa ke sanye da necktie baƙi, damtsen hannun shi ya ɗaura silver din agogo itama sai salki take, haka ƙafafunsa ya saka dress shoes wato rufaffun baƙaken takalma da suka matuƙar ƙara ƙawata shigar tashi, a kallo ɗaya in ka yi masa zaka yanke hukuncin yana daga cikin matasan Abuja da suka taso cikin hutu da jin daɗi saboda yadda shigar ta amshi jikinsa, sumar kansa da ta fuskarsa sun sha gyara sun kwanta luf.
Shigowa ta yi cikin ɗakin ko sallama babu, motsin da Fahad ya ji ya saka shi ɗaga ido ya kallo ta suka haɗa ido, mom ɗin su Deen ce ta shigo, da alama itama ta shirya tana sanye da wata jigunanniyar abaya maroon mai duhuwa, kallo ɗaya in ka yi mata sai ka firgita da kyaun da ta yi a cikin rigar, ta matuƙar amsar jikinta farinta ya fito sosai wani fayau, saman kanta ta naɗa gyallen rigar yayin da fuskarta ta yi makeup har da janbaki kalar rigar wato maroon, ƙafafunta tana sanye da takalma half cover masu dan tsini kalar aikin rigar wato golden, haka hannuwanta ta riƙe purse wadda da gani mahaɗin takalman ce itama golden, ta dai yi kyau sosai ba ƙarya.