← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 197

Sashe 47

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Is everything alright?" Cike da kulawa Fahad ya tambaya, ɗan yamutsa fuska Deen ya yi ya ce, "Mun gama magana da mom ne ta yi faɗa akan na taho ban sanar masu ba, amman ba wani abu." Ya ƙarasa with a smile on his face, shiru Fahad ya ɗan yi yana kallon shi kaman yana nazarin wani abu, sigh ya yi ya furta, "I guess ta yi maka magana akan yarinyan da zaka aura?" Juyowa Deen ya yi ya kalle shi tare da yin dariyarsa mai tsada ya furta, "You guess right. Amman ya akai kasan ta yi mani maganan?" Dan ta6e baki Fahad ya yi yana gyara zaman shi ya ce, "Yakamata ta yi maka maganan ne, ina lura da kai tun a Abuja baka yi waya da ita ba, ɗazun a gidan hajiya ta kira ka lokacin kana bathroom and I thought you will call her back da ka fito sai baka yi hakan ba, nasan dole ta kai ƙarar ka." Dan murmushin gefe Deen ya yi ya kai hannu ya shafi sumar shi. "Na kasa in saba da ita ne a matsayin wadda nike dating, still ina mata kallon sis dina ne." Gyara zama Fahad ya yi tare da cewa yakamata ya saba da hakan, remote Deen ya ɗauko ya sake canza wata sport channel kuma cikin sa'a ɗaya daga cikin wasannin su ne da suka buga a kakar wasanni da ta wuce ake sake nunawa, bayan wani lokaci Deen ya duba agogon hannunsa ya ce ma Fahad bari ya zo ya tafi yana son ya kwanta da wuri don ya huta sosai, kallon shi Fahad ya yi ya ce mashi ya kwana a nan mana, "Ba zaka je aiki gobe ba?" Deen ya tambaya, amsa ya bashi da zai je amman ai gidan ba baƙon shi bane da zai ce sai yana nan zai zauna, murmushi kawai ya yi Fahad ya kai hannu ya ɗauki wayan shi da ya ajiye a gefe ya ce bari ya sanar ma hajiya anan zai kwana kada ta yi ta jira Deen ya furta ok, bayan Fahad ya gama yin wayan ya ce ma Deen ya je ya yi wanka don ya kwanta ya huta, miƙewa ya yi ya nufi bedroom Fahad ya ɗan ɗaga murya yana ce mashi idan ya gama sai ya ɗauki kayan bacci cikin closet ya ɗaga mashi kai. Wayar Fahad ce ta fara yin ringing ya kai duban shi kan screen ɗin ta, mom dinsa ce ya ga tana kira ya ɗauka, tambayar shi ta yi amman anan Deen zai kwana ko ya amsa mata da eh, ta ce ya tambaye shi ko yana buƙatar tea ko coffee ta san turawa da sabo da shan su da dare, murmushi ya yi ya sanar mata ya shiga wanka sai ya fito zai tambaye shi ta amsa da ok. After some minutes Deen ya fito jikinsa sanye da bathrobe, shiryawa ya yi ya saka kayan bacci riga mara hannuwa da wandonta iya gwiwa, yana cikin gyara sumar shi ya ji wayar shi na sanar mashi da ana kira tare da sunan mai kiran wato Basma, sai bayan da ya gama abun da yake yi sannan ya nufi inda wayan take, zama ya yi a bakin gadon ya ɗauki wayan lokacin tuni kiran ma ya tsinke, ya san ko ya kira ta cewa za ta yi su yi vedio call don ta fi son hakan duk za su yi waya, komawa ya yi ɗayan 6angaren gadon ya ɗan kishingiɗa tare da jingina bayansa da kan gadon, vedio call ya shiga kiran ta yana shiga ta ɗauka, lokacin da ya yi arba da ita har sai da ya ɗan kauda idonsa gefe, ita dai tana son saka fingilallun kaya, har magana sai da ya ta6a yi mata can baya kan irin shigan da take yi idan yana a gida, lokacin sai ta nuna wai miye ai shi yayanta ne, ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita duk da haka bai kamata tana saka kowane irin kaya ba saboda shi ba muharraminta bane amman ta ƙi ta bari. Bayan da maganar aure ta shiga tsakanin su sai ma abun da ya ci gaba, bata jin komai ta saka kowani irin kaya, wani lokacin idan ya je gidansu har sai ya nuna mata 6acin ran shi sannan take canza kaya, duk da wasu kayan ko ta canza duk uwar ɗarin ce amman dai wasu da ɗan dama.

Itama a kishingiɗe take tana sanye da wata vest kalar ruwan ƙasa da ko rufe mata mara bata ƙarasa yi ba, da wando casual short, irin ɗan guntun wandon jeans da iyakarsa tsakiyar cinyoyi, a kunnanta ta saka manyan zagayayyun ƴan'kunne dake da stones masu sakin ƙyalli, ɗayan hujen kunnan da take da ta saka ɗan kunne barima. Shiru ta yi tana kallon shi tare da ɗan kikkafta idanunta dake ɗauke da dogon gashin ido masu gazar-gazar,

ÆŠan murmushi ne akan fuskar Deen ganin kallon da take bin shi da shi irin na kana tuhumar mutum da laifi,

"Basma, How are you doing?"

Ɗan kauda ido ta yi, sam bata jin daɗin yadda ya ƙi daina kiranta da sunanta ya rinƙa kiran ta da sunan da ke nuna akwai soyayya a tsakanin su, maido idonta ta yi suka shiga cikin na shi, "Do you even care how I’m doing?" Ta tambaya da ɗan yanayin fushi, yadda ta yi maganar cikin salo da sarrafa labbanta, still murmushin ne akan fuskarsa yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba,

"Now that you are settled after arriving at your destination yesterday, i thought you would want to catch up on how I’m doing. It feels like I’m not a priority." Ta faɗa da London accent,

Shafa sumar kansa ya yi ya ce, "Don't think that way, I'm not fully settled yet. Na daÉ—e ban ziyarci nan ba, and you know my career as a footballer keeps me busy with so many things."

Har ta ji sanyi a ranta hakan da ya faɗa, shiru ta yi tana jefa mashi kallo mai cike da so da ƙauna, "Ya dad da mom?" Amsa mashi ta yi da suna lafiya, ta tambayi suma bai tuntu6e su bane tun da ya bar nan? ya bata amsa da sun yi magana, "Ni ce baka samu lokacin ka yi magana da ni ba?" Ta yi maganar tana mashi kallon tuhuma, da ɗan murmushi kan fuskarsa ya ce mata no ba haka bane ya bari ya samu isasshen lokaci ne da za su yi magana, su dad kawai sun gaisa ne, har ta ji daɗi daga murmushin da ta yi.

"Ya hutun ka? Are u enjoying it?" Kai ya jinjina mata alamar yana jin daɗin hutun, ta ce, "Mom ta faɗa man kana garin su dad, ta ya za ka ji daɗin hutu a nan ƙauyen?" Murmushin gefe ya yi, ya bata amsa da ai sai ya fi jin daɗin hutu a nan tun da bai saba da irin wurin ba sosai, ta6e baki ta yi kafin ta tambayi yaushe zai koma ya faɗa mata,

"Ba don bana son zuwa 9ja ba da zan biyo ka ne, ko da ba a yi hutun skul ba." Ta faÉ—a tana kanne mashi ido, tambayar ta ya yi saboda mi ba ta son zuwa?

"Kawai bana jin daɗin zama a country ɗin." Ɗan jinjina kai ya yi, ya ce "Yakamata kuwa ki koyi jin daɗin zama tun da kaman ƙasar ki ce, parents ɗin ki nan ne asalin su." Ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba. Magana suka ci gaba da yi, yawanci duk ita ce ke yin maganar ya bata amsa, jin alamar an shigo ya sa shi kallon wurin kofar ɗakin, Fahad ne ya shigo ganin waya a hannun shi ya dakata daga bakin ƙofar tare da tambayar shi yana waya ne Deen ya ɗaga mashi kai alamar eh, amsa masa ya yi da ok bari ya gama, "Da wani abu ne?" Har zai juya ya ji Deen ya tambaya, dakatawa ya yi ya ce mashi dama mom ce ta ce a tambaye shi ko yana buƙatan wani abu na ci ko sha, ɗan murmushi ya yi ya bashi amsa da no ai sun ci abinci.

"Ba ka buƙatan tea ko coffee? Ta ce ta san ku turawa kun yi sabo da shan su kafin ku yi bacci." Ɗan faffaɗan murmushi Deen din ya yi ya ce kamar kuwa ta sani ya yi sabo da shan coffee kafin ya kwanta, amma ba sai sun wahalan da kan su ba, Fahad ya ce to miye abun wahala ko Sadeeya sai ta haɗa mashi, "Ba kana kan waya bane?" Fahad ya tambaya, Deen ya ce, "Yea, Basma ce."

"Ka ce kai da amarya ne ake shan luv na zo na katse ku." Wani kallo Deen ya yi mashi wanda nan take Fahad ɗin ya fahimci mi kallon ke nufi, ɗan murmushi Fahad ya yi tare da juyawa ya fice, tambayar shi Basma ta yi waye suke magana bayan ya maida fuskarsa kan screen ɗin wayan ya bata amsa Fahad ne, da yake ta san Fahad ɗin ta ce yana ina su gaisa, wani kallon baki da hankali ya jefa mata ganin da irin shigar da ke jikinta take cewa za ta gaisa da wani, ya san a wurin ta hakan ba wani abu bane, amman koda ba wani jin ta yake a ransa ba nan da ɗan lokaci za ta zama iyalinsa dole ya yi kishin a gan ta haka, amsa ya bata da Fahad ya fita ta amsa da ok, ƴar hira suka ƙara yi kaɗan ya ce mata yana son ya kwanta ya huta sai sun ƙara yin magana, ba don ta so su gama yin wayar ba a lokacin, ta ce sai yaushe za su ƙara yin magana ta san sai bayan wasu kwanakin kuma, gudun jan maganar ya sa shi ce mata da ya samu lokaci zai kira ta, ta amsa da tana jira idan kuma ta ji shiru ita za ta neme shi dama ta fi damuwa da shi, murmushi kawai ya yi ya ce mata good night,
Chapter 47 · 0% Book details