Sashe 30
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Suna wuce wata kwana dake a 6angaren hagun su, a daidai bakin gida na farko dake a bakin hanyar ya fara ƙoƙarin karya kan motar, cikin wasa ya ce Allah Ya sa nan ne gidan hajjan bai manta ba, yanayin fuskar Fahad ne ya ɗan canza kaman zai yi murmushi ba tare da ya ce komai ba sanin da wasa ya yi maganar, kana gani kasan ba ƙaramin babban gida bane yadda katanganar shi ke da tsawo a bakin hanyar, jami'ai biyu ne zaune a bakin tangamemen baƙin gate ɗin shiga gidan, daga yanayin yadda aka tsara ginin katangar gidan ma zaka san cikin gidan ma ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, akwai shuke-shuken fulawoyi masu kyau da tsari da fitulu a wajen, daga waje kana hango wasu shuke-shuken dogayen fulawoyi dake a cikin gidan. Jami'an na ganin motar ɗaya ya miƙe daga saman bencin da suke zaune don ya je ya buɗe masu gate sanin motar ko ta wacece, yana gama buɗewa motar ta kutsa kai jami'an na ɗaga ma motar hannu don duk a zaton su Fahad ne kawai a ciki.
"Ko dai shine ya iso?" Wani matashin mutumi ne ya faÉ—i hakan daga bangaren daman dake kallon gidan suna zaune su ukku a bakin wani shago,
"Anya kuwa, idan shine ai ba zaka ganshi ya zo a mota É—aya ba kuma ba tare da jami'ai ba, sannan bana ma tunanin zai hawo waccan motar sai dai wadda ta fita." Guda ne a cikin su ya furta.
"Ai bama shi bane, waccan motar ta wannan jikan gidan likita ce, ya ma sunan shi...yauwa, Fahad ɗin nan." Wanda shine mai shagon ya faɗa. Su nan duk ƴan ƙwallo ne zaman dakon zuwan Deen suke tun da suka gani a facebook cewa yana a Zaria, shine suke tunanin daga can ƙilan nan Funtua zai wuto.
"Amman bakwa gani ko tare suke? Ai dama hoton da muka ga ni ɗazun an yaɗa a Zaria ne suka yi shi kuma tare da likitoci suka yi shi." Wanda ya fara yin magana tun farko ne ya sake fadin hakan, cike da kokonto na biyun ya ce gaskiya dai ƙilan shi likitan bada motar ya je wurin aiki ba don ba yadda za ai Nuree Jr ya yo irin wannan shigowar, haka dai suka yi ta faɗin hasashen su.
Kai tsaye babban parking space ɗin gidan suka nufa wanda zai iya ɗaukar motoci shidda, bayan sun faka a kusan tare suka fito Deen na riƙe da hular shi a hannu, ƴar miƙa ya yi tare da faɗin Alhamdulillah, Fahad dake kallon shi daga ɗayan bangaren da ɗan murmushi ya ce halan ya gaji,
"Sosai, it has been a long time ban yi driving haka ba, and tuƙi a Nigeria sai mutum ya saka kula sosai saboda yanayin hanyan ba kyau." Murmushi kawai Fahad ɗin ya yi, officern da ya buɗe masu gate yana gab da rufewa ya ga sun fito, dakatawa ya yi yana kallon Deen cike da mamaki, sam bai kawo ma ransa zai ganshi ya fito daga cikin motar ba, duk da suma sun ga hotunan shi da aka wallafa cewa yana Zaria, da sauri ya juya kan abokin aikin shi ya sanar da shi ga Nuree nan sun zo tare da Fahad, yana jin haka ya yi saurin miƙewa yana tambayar shi da gaske, tare suka shigo cikin gidan suka nufo su, da ɗan ɗaga murya guda ya fara faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...." Ya yi hakan ne don ya dakatar da su ganin suna ƙoƙarin shiga cikin gidan, cikin washe baki suka shiga gaisawa da shi suna mashi an zo lafiya, yana amsa masu cikin sakin fuska Fahad na daga gefe shima suka yi mashi sannu da zuwa, bayan sun gama gaisawa har za su wuce, ɗaya daga cikin officers ɗin ya ce mashi pls bari su ɗan yi hoto yana fiddo waya, Deen ya basu damar hakan, bayan sun yi hoton suka wuce suma su officer ɗin suka nufi komawa gate cike da zumuɗin zuwa su yaɗa labarin zuwan shi da hoton da suka yi. Harabar gidan na da girma sosai, bangare biyu ne a cikin gidan, akwai bangaren iyayen Deen wanda ƙaton ginin bene ne yana daga can ciki amman tun a bakin gate kana shigowa zaka hango ginin saman benen, 6angaren hajiya shine a farko wanda shima babban flat ne mai kyawun gaske, daga gefen ginin hajiyan ana hango wani 6angare na jikin ginin su Deen kuma ta nan ake bi zuwa can bangaren.
Page 11&12
WAIWAYE
Lokacin da Hajiya Binta ta auri mijinta marigayi Amb. Nuraddeen, duka bata wuce shekaru goma sha huɗu ba, lokacin iya karatun ƙaramar sakandire ta yi, sai bayan shekaru da yin auren su lokacin suna zaune ƙasar waje ta samu ci gaba da karatun ta in da har ta kai matakin digiri na biyu a fannin kasuwanci, hakan yasa ta kasance babbar ƴar kasuwa ce dake yin kasuwancinta tsakanin ƙasashe daban-daban, ta kasance tana siyar da furniture na ƙasashe daban- daban da kayan sakawa da su akwatuna, jakunkuna, takalma, tana da plaza fin ɗaya dake da manyan shaguna na kaya da ake kula mata da su anan Funtua da kuma Zaria, haka kuma tana da motoci da ake haya manya da ƙananu da kuma keke napep da mashina, sannan kuma itama tana gonaki da ake mata noma sosai. Koda yanzu Hajiyar Ambasada ta tsufa har yanzu kasuwancinta na saro kaya daga ƙasar waje na tafiya lafiya lau don ta kafu sosai, tana da connection mai ƙarfi da kamfunan da take sarar kaya na ƙasashen waje, kuma tana da amintattun mutane dake mata hidimar komai. Mahaifin su Fahad ne ɗanta na farko da ta haifa bayan shekaru ukku da yin aurenta, a yanzu yana cikin shekara ta hamsin da bakwai, sakamakon ya fara yin aiki da wuri hakan yasa ya yi retire kafin ya kai shekaru sittin. Lokacin da ya kammala karatun shi na degree mahaifin su babban ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje ne hakan ya sa aiki bai mashi wuyar samu ba. Sai mahaifin su Deen wanda a cikin shekarar da ake yake cika shekaru hamsin da biyu, gaba ɗaya karatun su ba anan ƙasar suka yi shi ba hakan yasa suke kammalawa da wuri.
Bayan mahaifin su Fahad ya fara aiki bada jimawa ba yana da shekaru 27 aka yi auren shi da Hajiya Amina, auren zumunci ne aka yi masu don ƴar'uwar su ce matsayin cousin ɗinsa take, tun kafin ya kammala karatun shi soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su a zuwan da suke yi, anan Funtua mahaifin shi ya gina mashi gida wanda shine har yanzu suke a ciki, bayan shekara ɗaya daidai da yin auren aka haifi Fahad.
Daga baya lokacin da Alhaji Sa'ad ya yi kuɗi sosai ta hanyar aiki da sana'ar noman da suke yi ne ya ƙara faɗaɗa gidan da suke tare da ƙawata ginin daga flat ya koma babban ginin bene. Da yake irin aikin mahaifin shi ne ya yi hakan yasa suma sun ɗan zauna a wasu ƙasashen sai dai basu kai yawan ƙasashen da mahaifinsu ya yi aiki ba, kuma shi bai samu kaiwa matsayin Ambassador ba ya ajiye aiki amman ya kai daga cikin manyan matsayi a aikin.
A bangaren Jameela mahaifiyar su Deen, ta kasance ita ce babba a gidan su, sai mai bi mata wato Sapna, Bashir shine na ukku sai mai bi mashi Naila, akwai ƙanwar su ta biyar Aseeya sai ɗan autan su namiji Adam dama su shidda ne a gidan su.