Sashe 140
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun iso asibitin, aunty Kubra ta faka motar a wurin da aka tanada don haka, a tare suka fito daga cikin motan Salma ta buɗe back door ta ɗauko food carrier ɗin, cikin maternity ward din da aunty Kubra take suka nufa, suna shiga staff suka shiga gaisawa da aunty Kubra daga gani suna girmama ta, wani matashin mutum ne ya fito ta wata ƙofa jikinsa sanye da baƙin wando da maroon riga mai ma6allai ya yi tucking rigar cikin wandon, wuyansa rataye da stethoscope, tsaf tsaf da shi sai sakin ƙamshi yake, a yanayin shekaru zai kai talatin da wani abu, wankan tarwaɗa ne kyakkyawa da shi da ganin fatarsa ka san hutu ya zauna masa, kana ganinsa ba sai an faɗa ba zaka gane likita ne, dakatawa ya yi gaban aunty Kubra da murmushi ya gaishe da ita, ta ce, "Dr Hisham barka da dare, kana on call ne?" Amsa ya bata da eh, "Tare zamu kasance ke nan." Ta faɗa tana murmushi, kallon Salma da ke gaishe da shi ya yi ya amsa mata da murmushi, maida idonsa ya yi kan aunty Kubra ya ce, "Aunty Kubra baƙuwa muka yi ne?" Ta ce masa eh tare suka zo, kai ya jinjina ya ƙara kallon Salma suka haɗa ido, "Aunty Kubra wacece ita don ban ta6a ganin ta kin zo da ita ba." Aunty ta yi ɗan faffaɗan murmushi ta ce, "She's my daughter." Sake kallon Salma da ke ɗan murmushi ya yi ya maida idonsa kan aunty ya ce ɗiyar ƴar'uwarta ko ɗan'uwanta? Aunty ta ce, "I mean my biological daughter" Ɗan kai idonsa ya yi kan Salma kafin ya kalli aunty da yanayin shakku, tana ƴar dariya ta ce, "Baka ga muna kama ba." Still sai da ya ƙara kallon Salma kafin ya ce gaskiya basu kama, "Na fi ta kyau ko?" Aunty ta tambaya, Dr Hisham yana ɗan murmushi ya ce in dai gaskiya za a faɗa Salma ta fita kyau, Aunty ta saka dariya ta ce, "Ka dai duba da kyau Dr, ni da nike fara ka kuma san fari kyau ne." Dr Hisham ya ce, "Aunty ai yanzu fari ba ya a cikin kyau tun da har na kanti ana siyarwa, kuma ita kalanta ma mai tsada ne ba a cika samun shi ma a cikin mutane ba sosai balle a kanti." Salma dai murmushi kawai take tana ɗan sauke idonta ganin yadda Dr ɗin ke yawan kallon ta, sake tambayar aunty ya yi game da Salma ta sanar da shi ɗiyar cousin sister ɗinta ce ta zo mata hutu ne, kuma itama tana son zama nurse kamar ita, Dr ya jinjina kai tare da kallon Salma ya ce, "You are welcome baƙuwar mu." A hankali ta yi masa godiya, aunty ta ce bari su kai kayan hannun su ciki sai sun haɗe a ward round ya ce ok ya wuce suma suka nufi ciki, bakin wata ƙofa suka zo aunty ta buɗe suka shiga, ɗan madaidaicin ɗaki ne akwai gado da yar side locker kalan na asibiti sai kujerar zama ta roba da ɗan madaidaicin fridge, a jikin window ɗin ɗakin an saka labule yayin da ƙasan ɗakin gaba ɗaya tiles ne, a saman drawer ɗin gefen gadon aunty ta ɗaura jakar hannunta, kallon Salma ta yi ta ce ta ajiye food carrier din ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, wata ƙofa dake a cikin ɗakin aka buɗe suka kai idanun su wurin, wata ƴar dattijuwar mata ce ta fito hannunta riƙe da bucket da ƴar jarkar liquid soap a ciki, tana ganin aunty ta yi murmushi tare da gaishe da ita, aunty ta amsa tare da tambayar ta wanke toilet ɗin aka yi ta ce mata eh, sannu aunty ta yi mata matar ta amsa daga haka ta nufi ƙofa ta fita, jakar da ta ajiye ta kai hannu ta buɗe tare da fiddo wani ɗan madaidaicin zanen gado, farin yadin dake a saman gadon ta kai hannu ta cire bayan ta kakkabe gadon ta fara shimfiɗa wanda ta fiddo, Salma ta miƙe ta ce bari ta shimfiɗa ta bata ita kuma ta juya ta shiga toilet bayan ta cire rigar saman uniform ɗinta, bayan ta fito ta ce ma Salma za su je ward round sai ta dawo ta ɗaga mata kai, bayan ta kai ƙofa ta juyo ta ce, "Ga ruwan zafi nan a flask idan zaki haɗa tea, idan kina jin bacci ki kwanta a gadon." Salma ta amsa da to tare da yi mata sai ta dawo, bayan tafiyar aunty komawa ta yi saman gadon ta ɗan kishingiɗa tana latsa wayarta don bata jin yunwa ta riga ta ci abinci kafin su taho, after some few minutes da tafiyar aunty ta ji an yi knocking kofar ɗakin, ɗagowa ta yi tana kallon ƙofar jin an ƙara yin knocking ta ɗan ɗaga murya ta ce ƙofar a buɗe take, turo ƙofar aka yi tana ganin wanda ya shigo ta tashi zaune sosai tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake, ɗan murmushi ya yi mata ya ce, "Baƙuwarmu ke kaɗai?" Kai ta ɗaga masa, ya tambayi aunty ta ce masa ta fita ta ce za su je ward round, kai ya ɗaga mata daga haka ya juya, sai kuma ta ga ya dakata tare da juyowa ya kalle ta ya ce, "Amman zaman ke kaɗai ba za ki ji kaɗaici ba?" Ta yi ɗan murmushi ta ce masa a'a, ya ce, "Ko da yake ai ga phone nan zata ɗebe maki kewa kafin ta dawo." Ita dai murmushi kawai ta yi, ya sake cewa, "Amman tun da fannin mu kike son karanta ai kamata ya yi aunty ta tafi da ke ward round ɗin ki fara samun experiance." Shiru ta yi tana kallon shi bata ce komai ba, "Idan kina so mu je sai ki fara ganin yadda abubuwan suke ko." Ya faɗa idonsa akanta yana ɗan murmushi, shiru ta ɗan yi sai kuma ta ji tana son ta je ɗin, saukowa ta yi daga saman gadon ta saka takalmanta ya yi mata alamar su je suka nufi ƙofa, bayan sun fito ya cire stethoscope ɗin wuyansa ya miƙa mata ya ce ta riƙe masa ta amsa sannan suka tafi, yana gaba tana biye da shi bayan sun fito nan suka haɗe da aunty Kubra ta taho wuyanta rataye da stethoscope, hannunta ɗaya wasu files ne ɗayan kuma na'urar auna BP, tsayawa suka yi aunty ta kalli Salma sai kuma ta kalli Dr ta ce, "Ko nema na take ne?" Yana murmushi ya ce mata a'a ya je wurinta ne ya iske bata nan sai ita kaɗai shine ya ce ta zo su je a yi ward round ɗin da ita don ta fara samun experience, aunty ta yi ƴar dariya ta ce kuma haka yakamata daga haka wuce, wani babban ɗaki suka shigo wanda gaba ɗaya majinyatan mata ne masu fama da lalurori daban-daban da suka shafi ciki da haihuwa, su ukku suka fara duba marasa lafiyan ita dai Salma tana biye da su, lokaci guda kuma jikinta ya yi mugun sanyi laƙwas saboda tausayin halin da marasa lafiyan ke ciki, lokaci bayan lokaci Dr Hisham ke ɗan kallo ta da murmushi yayin da yake bincikar majinyantan ya ce mata tana ganin yadda suke aikin ta ɗaga masa kai, sai dai a yadda take ji ma gaba ɗaya ta sare kamar ba zata iya jure ganin yadda suke duba marasa lafiyan ba, bayan sun gama da 6angare guda za su nufi ɗayan bangaren, aunty ta kalli Salma ganin ta ja ta tsaya, tana murmushi ta ce mata ya aka yi ne, cikin rawar murya ta ce, "Ɗakin zan koma." Dafa shoulder ɗinta aunty ta yi tana tambayar mi ya sa zata koma ko ta gaji ne, kawai sai gani ta yi ta fashe da kuka ta rufe fuskarta a jikinta, Dr Hisham da har ya fara duba wata ya ɗago yana kallon su, dawowa wurin su ya yi yana tambayar aunty lafiya mi aka yi mata, ɗago fuskarta aunty ta yi ta ce, "Mi ya faru ne baby?" cikin muryar kuka ta ce bazata iya ci gaba da bin su ba ɗaki zata koma, ƴar dariya aunty ta yi ta kalli Dr ta ce, "To Dr baƙuwar mu mai koyon sanin makamar aiki tausayi ba zai bari ta ci gaba da koyon aikin ba." Ɗan buɗa ido ya yi sai kuma ya yi yar dariya ya ce, "To baƙuwar mu a haka zaki yi irin aikin namu, dole aikin mu sai an cire tausayi sannan za a iya shi." Shiru Salma ta yi ta sauke idanunta ƙasa, aunty ta tambaye ta zata iya ci gaba da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta kalli Dr ta ce pls bari ta maida ta ɗaki she will be back now, ya jinjina mata kai still da ɗan murmushi akan fuskarsa ya yi ma Salma sai da safe, ba tare da ta kalle shi ba ta ɗaga masa kai suka tafi, aunty bata daɗe ba bayan ta kai Salma ɗaki ta dawo, Dr na murmushi ya tambaye ta ya Salma ta ce tana can ta kai ta ɗaki, ya ce amman dai tana da tausayi sosai, aunty na ƴar dariya ta bashi amsa da haka take tausayi ne da ita sosai, Dr Hisham ya ce to wannan ma zata iya aikin asibiti, aunty ta ce da ta fara karatun dole zata bar tausayin. Salma ta ɗaga ido ta kallo ƙofa jin an turo, aunty ta gani ta shigo da alama sun gama ward round ɗin, nufo ciki ta yi tana kallon Salma da ta tashi zaune daga kwancen da ta ke tana kallon ta, daga gefenta saman gado ta zauna da ɗan alamun mamaki ta ce, "Wai baki bacci ba har yanzu?" Salma ta ɗaga mata kai duk ta yi sukuku da ita, aunty da ta lura da har lokacin a sanyaye jikinta yake ta kai hannu ta dafa nata hannun da ɗan murmushi ta ce, "Kin ga abubuwan da suka tada maki hankali ko, irin abubuwan da mata ke going through ke nan yawanci duk sanadiyar haihuwa....amman a haka wasu mazan basu da abun wulaƙantawa irin mace, wata ma don bata haihun ba