Sashe 133
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
masa, Fahad na ganinsa ya miƙe yana masa sannu da zuwa da murmushi ya amsa masa, ya ƙarasa daga gaban kujeran da hajiya take ya tsugunna, a nutse cikin ladabi ya gaishe da ita, tana murmushi ta amsa masa tare da yi mashi an zo lafiya, ta ce "Ya aka baro iyali?" Yana murmushi ya ce, "Duk suna nan lafiya lau suna gaishe da ku, suma suna nan zuwa in sha Allah." Hajiya ta ce Allah Ya yarda, miƙewa ya yi bayan sun gama gaisawa idanunsa akan Fahad ya nufe sa tare da miƙa masa hannu suka gaisa, bayan ya zauna akan kujera ya ce ma Fahad ya zauna, "Fahad ya aiki?" dad ya tambaya, ya ce, "Alhamdulillah, daga can ma nike yanzu." dad ya jinjina kai ya ce, "Allah Ya ƙara taimakawa." Fahad ya amsa da Amin, Hajiya na kallon dad ta ce, "Sai ga ƴar hutuna, saboda murna yanzu na gama bata abun sha a baki." Dad ya yi ƴar dariya tare da kallon Leemarh da itama dariyar ta ke, ya ce, "Ai da bata zo Funtua ba da hankalin kowa ba zai kwanta ba." Hajiya ta yi dariya ta ce, "Ta kwana biyu bata zo bane." Dad ya ce, "Hakane, na so ma su zo gaba ɗaya, to sai mom ɗinsu ta ce za su fara zuwa Kano da yake can ma sun ɗan kwana biyu ba su je ba." Hajiya ta ce ba komai za su zo ne wani lokaci, Leemarh ta kai hannu ta ce ma dad bari ta zuba mashi kunun aya ya yi daɗi sosai, hajiya ta ce ta bari a kawo masa wani, dad ya ce lafiya lau a zuba masa wannan ɗin, bayan ta zuba masa a cup ta miƙa masa, Leemarh ta kalli Fahad da fuskarsa ke kallon direction daban, zuba wani kunun ayan ta yi tare da miƙewa ta nufe shi ya juyo ya kalle ta, daga gefen sa ta tsaya ta ce gashi shima ya sha, ya yi mata murmushi ya amsa, bayan ya sha ya cire cup ɗin daga bakinsa, ta ɗan rankwafa ta yi ƙasa da murya ta ce, "Yaushe zaka je gida?" idonsa a cikin nata ya tambayi tana son zuwa ne ta ɗaga masa kai, ya ce ok ko yanzu idan ta shirya sai su tafi, miƙewa ta yi ta ce to bari ta ɗauko abu, hajiya dake kallon su ta ce ya aka yi ne Fahad ya ce tana son zuwa can gidansu ne, bada jimawa ba Leemarh ta dawo cikin falon tana riƙe da wata babbar farar shopping bag, hajiya na kallonta ta ce, "Baki bari ki ƙara hutawa, gashi ko abinci ma baki ci ba." Tana murmushi ta ce mata idan ta je can sai ta ci, dad dake kallonta da murmushi ya ce, "Kin ƙosa ki ga yan'uwan naki ne?" Ta ɗaga masa kai, hajiya ta yi mata sai ta dawo daga haka suka nufi ƙofa sun jera da Fahad, suna kusa isa ƙofa ya kai hannu zai amshi ledan hannunta, ta juyo ta kalle shi ya ɗan yi mata murmushi, hannu guda na ledar ta sakar masa suka kama tare daga haka suka fita daga cikin falon.....