← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 197

Sashe 161

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Maleek ya baro gidan su Huda, driving yake amman gaba ɗaya hankalinsa baya a tare da shi, damuwa ta yi masa yawa sai faman girgiza kai yake yi, wayarsa da ta fara ringing ce ta maido sa hankalinsa, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, daga ɗayan 6angaren mummyn Huda ta yi magana yadda take kiran sa, saida ya yi ƙoƙarin saita natsuwarsa kafin ya amsa mata, ta ce dama Huda ce ta dawo gida da kuɗi ta ce shine ya bata, so ta kira to confirm ko haka ne, ya bata amsa da eh shi ya bata, godiya sosai ta yi masa kafin suka yi sallama, Maleek ya ajiye wayan, nan take ya ji wani irin tausayin iyayen da ke tsaye akan tarbiyar yaransu ya kama shi, rayuwa ta lalace, kana jajircewa akan bawa yaron ka tarbiya amman hakan bai hana tarbiyan lalacewa, al'amarin tarbiya yanzu sai dai mutum ya yi iya bakin ƙoƙarinsa sannan kuma ya dage da roƙon shiriya daga wurin ubangiji. Gaba ɗaya Maleek ji ya yi bai son komawa gida, a bakin hanya ya parker motan ya fito, wani street bench irin kujeran zama na bakin hanya dake gefe ya nufa ya zauna, haɗe hannuwansa ya yi tare da ɗaura ha6arsa ya rufe ido, tunaninsa ne ya maida shi can baya, a cikin ransa yake raya miya sa yake fuskantar irin wannan munanan ƙaddaran, tunanin ko dai akwai abun da yake aikatawa da ya sa6a ma shari'a ba tare da sanin sa ba ya zo masa a rai, saidai a iya hangen sa bai iya hango wani abu da yake aikatawa da ya sa6a addini ba, gaba ɗaya Maleek ya ji duniyar bata masa daɗi...lalle A CIKIN RAYUWA da akwai tarin darussa, hamshaƙin mai kuɗi kamar Maleek yau shine ya za6i zaman bakin titi fiye da ya koma cikin daular da yake, wannan na nuna duk irin tarin arziƙin mutum Allah na iya jarabtarsa ta yadda arziƙinsa ba zai iya masa magani ba face shi ubangijin da ya ɗaura masa ƙaddaran, don haka mutum kada ya ga yana cikin ni'ima, a ko yaushe Allah ya so zai iya jarabtarsa ta yadda zai manta duk wani jin daɗi da yake ciki, kada ni'imar da mutum yake a ciki ta saka shi shagala da yin addu'ar neman kariya daga mummunan ƙaddara. Maleek ya ɗauki lokaci a wurin cikin tsananin damuwa, har sai da Sapna ta kira shi tana tambayar ina ya tafi tun da ba ranar aiki bane, sannan ya miƙe ya koma mota ya tafi. Haka kwanakin suka kasance ma iyalin ba daɗi, kana ganin su gaba ɗaya suna a cikin matsananciyar damuwa, ita Sapna ma ko aiki ta kasa zuwa tana gida duk don saboda saka ma Basma ido, gashi tun bugun da Maleek ya yi mata har lokacin bata da isassar lafiya, a yadda Sapna take ji har aikinta zata iya ajiyewa saboda Basma. Ba irin ƙoƙarin da Sapna bata yi ba wurin ganin ta shawo kan Maleek ya amince da auren su biyun amman ya kafe akan bakansa, ƙarshe ma da kansa ya je har ɗakin Basma wanda tun da abun ya faru bai sake zuwa ɗakin ba, ko haɗuwa a cikin gidan ma basu yi don yanzu har abinci kowa a 6angarensa yake ci, sun daina zama tare a falo ko wurin shan coffee, duk wasu abubuwa da suke yi a tare musamman na nishaɗi duk sun daina yi, a kausashe ya ce mata ta fidda rai da auren Deen, idan ma har zai amince ta aure shi to sai ya tabbatar ta shiryu ta daina aikata abun da take yi don ba zai cuci Deen ya aura masa ita ba bayan ta lalata rayuwarta, kuka wiwi Basma ta saka masa tana masa rantsuwar ta daina don Allah tana son Deen kada ya ƙi amince ma auren su, ya ce mata a baya ma ai haka ta yi masa rantsuwa da alƙawarin ta daina, don haka yanzu sai idan shi da kansa ya tabbatar da ta daina ta shiryu sannan ko zan amince. Ba ƙaramin tashin hankali Basma ta shiga ba da hukuncin da dad ɗinta ya yanke, haka ta kasance cikin matsananciyar damuwa kullum bata da aiki sai na kuka, a gefe guda kuma Sapna na matuƙar ƙoƙari wurin jan ta a jiki tana kwantar mata da hankali tare da ɗaura ta kan hanyar daidai, musamman saboda hakan Sapna ta ɗauki hutun aiki.

Tuni Nijeriya ta samu tikitin zuwa gasar world cup bayan ta yi nasara a wasan neman cancanta wato qualifiers, wanda nasarar samun tikitin ya fito daga hannun Deen da ya buga mata wasannin biyun ƙarshe da ya kai su ga samun nasara. Gaba ɗaya idanun duniya sun koma kan ƙasa mai masaukin baƙi wato Saudiyya, wadda tuni an yi babban shiri don wannan gagarumin taro, shirye shiryen sun haɗa da ƙara samar da wadatattun kayan more rayuwa, sufuri, da sauran abubuwan da ake buƙata don shirya irin wannan taro, an kuma sabunta da kuma gina manyan stadiums a birane guda biyar da aka za6a don gudanar da gasar. Yadda aka tsara yin gasar, a Riyadh, Dammam, Alkhobar anan ne za a fara gudanar da matakin farko na gasar wato group stage, sai Jedda da Riyadh a nan za a gudanar da Quater and Semi final, sai Final za a yi ta a NEOM wanda yake sabon birni da aka tsara da fasaha, gine-ginen zamani, da tsari mai ban mamaki. Tuni al'umma masoya ƙwallon ƙafa daga yankuna daban-daban na faɗin duniya suka fara hallara a ƙasar Saudiyya don kallon gasar, Riyadh da a nan za a fara gudanar da gasar ko ina ka hanga haske zaka gani, an ƙara ƙawata birnin da abubuwa masu jan hankali da burgewa da suka haɗa da abubuwa da ke jaddada ƙasar addinin musulunci ce, wasu cikin baƙi musulmai sun yi amfani da damar don su jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, wato su kalli gasar kuma su yi umra, hakan ya sa ko ta ina mutane ne sun cika tituna da hotel hotel, tawagogin ƙwallon ƙafa da za su fafata a gasar suma duk sun hallara a masaukai daban daban. Tuni tawagar Nijeriya ma ta iso, in da Deen ya kasance shine wanda aka za6a matsayin captain wato jagoran tawagar Nigeria a ciki da wajen fili, shi ke da alhakin ƙarfafa gwiwar ƴan uwansa, yin magana da alƙali (referee), da tsara ƙwarin gwiwa lokacin da lamari ya yi zafi. An fara gudanar da gasar kamar yadda aka tsara, cikin sa'a Nigeria ta tsallake group stage ta samu zuwa Quater final, gaba ɗaya a cikin gasar Deen yana ɗaya daga cikin taurarin da suke haskawa, wanda mutane har so suke a zo kan wasan shi, mutane a duk faɗin duniya sai yabon ƙwazon da yake nunawa suke, sai dai a wannan matakin da Nijeriya ta kawo a gasar, mutane musamman ƴan Nijeriya sun shiga ɗar ɗar sanin ba lalle su iya tsallakewa ba don nan ne ƙarshen matakin da Nigeria ɗin ta ta6a tsayawa, duk da ganin irin ƙwazon da Deen yake nunawa ya saka ma mutane hope ɗin za su iya tsallakewa. Cikin sa'a ta ubangiji Nigeria ta tsallake ta kawo matakin semi-final wato mataki na biyun ƙarshe, wanda mataki ne da Nijeriya bata ta6a kawo wa ba a tarihin gasar cin kofin duniya, ita da ƙasar Morocco sune ƙasashen Africa biyu da suka samu nasarar kaiwa wannan matakin, saidai ita Morocco ta ta6a kaiwa matakin semi final a gasar.....Abun na Allah ne! Africa ta bada mamaki, irin mamakin da mutane basu ta6a yi ba a gasar cin kofin duniya bayan da ƙasar Nigeria ta kai final, wani abu da bai ta6a faruwa ba a tarihin world cup wato ƙasar Africa ta kai matakin final, tabbas duniya ta shaida cewa africa ba wai ta gaza bane a baya don rashin ƙwarewa, kawai lokacin samun nasararta ne bai yi ba, a wannan mataki ƙasashe biyu ne za su taka rawar gani, ban da Nigeria sai ƙasar Netherlands wadda ita a tarihin world cup ta kakkai matakin final ba sau ɗaya ba amma bata ta6a lashe kofin ba. Gaba ɗaya nahiyar Africa ta cika da farin ciki da alfaharin wannan mataki da ta kai, mutane na ganin ko a haka aka tsaya Africa ta yi nasara...kamar yadda Nijeriya ke kallon Deen a matsayin jaruminta da ya kai ta ga wannan matakin nasara, haka itama ƙasar Netherlands tana da nata jarumin da ƙasar ke alfahari da shi kuma ya kaita ga nasarar kai wa final, sannan suna da ƴan wasa masu ƙwazo da salon wasa mai kyau, yanzu kuma sai zaman jiran ganin yadda zata kaya a final, in da gaba ɗaya hankalin duniya na akan wasan da waɗannan
ƙasashen biyu za su buga, ana son ganin ko wacce zata yi nasarar cin kofin duniya...a wannan lokacin ƙasar Saudiyya ta ƙara cika da mutane da suka zo domin ganin yadda za a fafata a gaban idanunsu, gaba ɗaya ƴan gidansu Deen sun zo, haka Maleek da iyalansa, a 6angaren gidan su mom, Nailah ma alhaji Mahmud ya kawo ta sun zo tare, sai Bash da shima ya zo, daga Funtua ma daddy Sa'ad da mommy sai Sadeeya da Khaleel duk sun zo, sai Fahad shi daga ƙasar India in da a yanzu yake cikin yin course a can ya zo, saboda course din da ya tafi ne India ya sa har yanzu bai kai maganar auren shi da Leemarh ba wurin iyayensa ya bari sai ya gama.

A gida Nigeria, al'umma ta cika da fata da sa ran ita zata yi nasarar lashe kofin, duk da wasu suna ganin abu ne mai wuya, yayin da manyan masu muƙamai da manyan ƴan kasuwa. har da manyan celebrities ke ta yi ma ƴan wasan alƙawarurruka idan har Nigeria ta ɗauki kofin. Ana gobe za a yi final, ƙasar Morocco ta yi nasarar zuwa ta ukku a wasan 3rd place da suka buga, wannan ya ƙara saka ma mutane fatan Nigeria ma ta yi nasara.....

Ranar ta zo.....
Chapter 161 · 0% Book details