← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 197

Sashe 178

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana da turanci, shortly after wani mutumi ya fito, kana ganinsa ka san farar fata ne tare da wasu mata yare guda biyu jikin su sanye da uniform na masu aikin wurin, a gaban motan suka tsaya bodyguards din suka fito, buɗe ma Deen da Salma kofan suka yi suma suka fito, cikin girmamawa mutumin ya gaishe da Deen da turanci ya bashi hannu, suma matan suka ɗan sunkuyar da kai suka gaishe da Deen, daga baya har da mutumin suka gaishe da Salma, mutumin ya yi masu alamar su shiga ciki da hannu, mutanen ne a gaba Deen da Salma a tsakiya sai bodyguards suka rufa masu baya, ashe Salma bata ga komai ba a tsaruwa sai da suka shigo ciki, a kaikaice ta ke kallon wurin ba tare da ta bari ta nuna ƙauyanci ba, bene suka nufa suka haye upstairs, nan ma wata duniyar tsaruwa ce, ƴar tafiya suka yi suka iso bakin wata ƙofa ta glass baturen mutumin ya buɗe masu tare da yi masu alamar su shigo, Salma ta ɗan bi cikin wurin da kallo wanda madaidaicin private dining room ne, wurin sam bai da hayaniya, tsarin da aka yi mai aji tun daga kan ginin, an saka labulaye masu kyau da aji a windows ɗin cikin ɗakin, haka a jikin bango an liƙa framed paintings in wooden frames da suka ƙawata ɗakin sosai suna kama hasken wurin, ga wani irin sanyin Ac da ƙamshi masu saka natsuwa a zuciya da saka masoya shauƙi, ɗan babban table ne a tsakiyar ɗakin da kujeru guda huɗu a zagaye da shi, cikin ma'aikatan mata da ke biye da su ɗaya ta ja ma Deen kujera tana kallon shi da murmushi, ɗayar matar ta ja ma Salma kujerar da ke kallon Deen amman sai ya yi mata alama da kujerar gefen shi wato a nan yake son ta zauna, kallon gulma suka yi da ido ita da ɗayar kafin ta zo ta ja ma Salma kujerar kusa da shi ta zauna tare da yi mata godiya, matar ta jinjina mata kai tana murmushi, gaba ɗaya ma'aikatan mamaki ne fal a ransu kan Salma, tunanin su wacece ita da kuma alaƙar ta da Deen, saboda suma sun ga ba ita ce aka bayyana ba matsayin fiancee ɗin shi, kuma daga alamun da suka bayyana soyayya ce a tsakanin su, sai dai suma duk sun ga kyawun Salma, kuma duk da basu san ita ɗin wacece ba suna ganin ta dace da take yin soyayya da Deen, bayan sun zauna cikin fara'a baturen mutumin ya ce ma Deen ga dukkan abunda aka buƙata nan an tanada sai ya duba ko akwai abun da bai yi ba ko za a ƙara, Deen ya jinjina masa kai, kiran ma'aikatan ya yi gefe ya gargaɗe su kan su kula da su sosai kada a samu wani matsala cikin girmamawa suka amsa masa, bayan ya yi ma Deen sallama ya fita, dama su bodyguards ɗin nasa suna a wajen wurin, Salma ta bi tarin uwayen abubuwan ci da sha da ke shake saman teburin da kallo, yayin da ma'aikatan suka shiga bubbuɗe abubuwan ƙawa da ke ɗauke da kalolin abinciccika na gida dana waje suna nuna masu tare da faɗin sunayen su, bayan sun gama nuna ma Deen cikin girmamawa suka tambayi abun da za su fara serving nasu, kallon Salma ya yi ya sakar mata lallausan murmushi, murya can ƙasa ya ce mi take son su fara ci, ma'aikatan suka wani kalli juna tare da ɗan buɗa ido, tun ɗazun da suke ta karakaina a gaban su ko kallon fuskar wata a cikin su Deen bai yi ba, fuskarsa ma basu wani ganinta sosai saboda face cap ɗin da ke a kansa, Salma sai da ta ɗan so ruɗewa wurin za6ar masu abincin ta rasa wanne zata ce, tana ganin kamar zata kwafsa idan ta faɗi kalan abincinmu da aka saba da shi, ƙarshe ta faɗi wani da ta riƙe sunan shi da suna gabatar masu, bata ma san kalan abincin ba haka nan ta zabe shi, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da aroma daban daban, bayan sun gama serving nasu suka yi masu a ci lafiya tare da ɗan ja gefe alamar a nan za su tsaya suna serving nasu har su gama, a nutse Deen ya fara cin abincin, ita kuwa Salma ta ji duk ta takura da tsayuwar da ma'aikatan suka yi, har sai da Deen ya fahimci ta kasa sakin jiki, bayan ɗan lokaci da fara cin abincin Deen ya ɗaga kai a karon farko ya kalli ma'aikatan ya ce masu za su iya tafiya, da sauri ɗaya ta ce an saka su aikin yin serving nasu har su gama ne, ya ce mata ba komai za su yi serving kan su, daga haka suka yi masu sallama tare da fatan gama cin abinci lafiya, tun a bakin ƙofar fita suka buɗe baki za su fara gulma, suna yin arba da bodyguards ɗin da ke wajen suka yi gum suka wuce...duk da sun tafi Salma ta kasa sakin jiki sosai ta ci abinci, shi kuwa Deen cin abincinsa yake hankali kwance, can ya ɗago kai ya kalle ta suka haɗa ido, ya ce mata zai fi ta saki jiki don komai za su cinye, Salma ta ɗan wara ido sai kuma ta yi ɗan murmushi a sanyaye ta ce, "Ta ya zamu iya cinye wannan abubuwan duka." Deen da ya kai abinci baki bayan ya cinye ba tare da ya kalle ta ba ya ce mata ai tana tare da acici lafiya lau zai koya mata yadda za su cinye, ta yi ɗan faffaɗan murmushi kafin ta langabe kai ta ce, "Ai ko rabin su ba zamu iya ci ba." Bai ce mata komai ba, ta ga ya kawo abincin da ya ɗebo bakinta, slowly ta buɗe baki ya bata, wai sai da ta amsa kuma sannan ta sunne kai alamar kunya, shi dai ɗan murmushi kawai ya yi, daga baya ta saki jikinta ganin yadda yake ta cin abincin sa...da kanshi ya riƙa serving nasu, duk abun da zai zuba mata sai ya tambayi idan zata ci...duk idan ta nuna masa ta ƙoshi sai ya ce ai bata wani ci sosai ba ta ƙara, daga baya ta marairaice masa ta ce ta ƙoshi da gaske, cikin wasa ya ce mata so yake itama ta rinƙa cin abinci sosai kamar shi, Salma ta yi yar dariya ta ce, "To ni da ba yar ƙwallo ba." Yana cin abu ya ce, "Ai kin kusa zama." Ta ɗan yi shiru sai kuma ta tambaye shi mata ma na yin ƙwallon, ya bata amsa da eh ko club ɗin su akwai team na mata, "To da gaske nima ƴar ƙwallon zaka sa in zama?" Ɗan murmushi ya yi da alama bata fahimci nufinsa da maganar da ya yi ba ta ta kusa zama ƴar ƙwallo, "Idan kin zama yar ƙwallo, who will take care of our children?" Salma ta yi shiru tana kallon shi, ya ɗago ido ya kalle ta ta yi saurin sauke idonta, ta ji ya ce ta ci gaba da cin abinci, sai da ta marairaice masa sosai kan ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta, ta maida idonta kan tv dake jikin bango shi kuma ya ci gaba da cin abincin shi, after a short while ta ga ya ɗauki waya yana latsawa ya kai kunne, ƴar magana kaɗan ya yi da ita bata ma ji mi ya ce ba ya cire wayan, bayan ɗan lokaci ba sai ga bodyguards ɗinsa sun shigo, Salma ta juya tana kallon na farkon da ya nufo su hannunsa riƙe da bouquet of flowers masu matuƙar kyau da tsari da kuma wata yar ƙaramar jaka, ɗayan kuma na biye da shi da wani ɗan faffaɗan kwali, Deen ya nuna masu gefe saman teburin suka ajiye kafin suka juya, Salma dai tai ta kallon abubuwa can kuma ta ɗauke kai tunowa da huɗubar aunty, idonta na kan tv ta ji ya yi mata magana ta juya, ƙwalin ya ɗauka ya miƙa mata ta amsa tana bin sa da kallon rashin fahimta ta ajiye a gabanta, yana kallonta ya ɗan lumshe ido slowly ya ce, "Open it..." Hannu ta kai zata buɗe a ranta tana tunanin miye a ciki, ƙamewa Salma ta yi tana ta kallon abun da ta yi arba da shi ƙirjinta yana ɗan bugawa da sauri, lokaci guda kuma ƙayataccen murmushi ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta tana ci gaba da kallon cikin kwalin with astonishment, faffaɗan cake ne mai kyaun gaske daga saman shi an yi adon rubutu, abun da aka rubuta shine, "_Will you marry me?_" A hankali Salma ta juya ta kalli Deen da ya jingina da kujera yana bin ta da kallo da ɗan murmushi, ɗage mata gira ya yi alamar ta bashi amsa, slowly Salma ta hau jinjina masa kai kafin cikin ƴar rawar murya ta furta, "Yes I will..." Kawai sai ga ƙwalla sun zubo mata sharr, bayan hannunta ta saka tana goge ƙwallan tana kuma yin murmushi at the same time, ɗagowa Deen ya yi daga jinginar da ya yi ya kai hannu cikin ƙaramar jakan, wani ɗan ƙaramin jan akwati ya ɗauko tare da buɗe shi, tun Salma bata ga mi ke ciki ba ta ga ƙyallin abun, hannu ya sa ya ciro abun da ke ciki ya riƙe da dogayen yatsun shi ya ɗago yana kallon ta, Salma ta bi haɗaɗɗan zoben da kallo wanda kana gani na diamond ne, ɗago ido ta yi ta kalli Deen suka bi juna da wani kallo, alamar zai saka mata ya yi, hannunta har ɗan rawa yake ta miƙa masa yatsanta, Salma ta bi zoben da ya zauna a yatsanta ya yi mata daidai kamar an gwada da kallo, sosai ya yi ma hannunta kyau sai sheƙi yake yana ɗaukar hasken wurin, ɗago fuskarta ta yi tana kallon Deen da murmushi lokaci guda kuma ƙwalla suka ƙara zubo mata, kawai sai gani ya yi ta duƙe kanta alamar kuka ta ke, shi dai still yay yana ta kallonta da ɗan murmushi, ko bata faɗa masa ba alamu sun nuna tana son shi sosai shima kuma hakan yake ji game da ita, kusan ko wane lokaci son ta
Chapter 178 · 0% Book details